Ticker

6/recent/ticker-posts

Cutarwar Mahaifiya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Kasuwanci ya haɗa mahaifiya da ɗanta, kuma sai ta riƙa cutar da shi tana janyo masa asara. Ta hana shi tara komai. Menene hukuncin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A ƙaidar musulunci ba mu san wata doka da ta hana ciniki a tsakanin iyaye da yayansu ba. Don haka mahaifiya tana da daman yin ciniki da ɗanta haka shi ma ɗa yana iya yin ciniki da mahaifiyarsa ko mahaifinsa.

A nan mai tambaya bai bayyana menene mahaifiyar take yi na cutarwa da har yake janyo wa ɗan asara ba, balle har a duba a ga ko da gaske aikinta ɗin shi ya janyo masa asarar har kuma ya kasa tara komai, ko kuwa dai wani ko waɗansu abubuwan ne daban kawai. Wato kar ya zama kamar yadda Hausawa suke cewa, ‘kulɓa ce ke ɓarna amma ana cewa jaɓa ce.’

Amma in dai haka abin ya ke kamar yadda aka faɗa, to bai halatta ba a addinance mahaifi ko mahaifiya su cutar da ɗansu ba, su riƙa zama dalilin janyo masa asara a cikin harkokinsa na tattali, suna hana shi tara komai ba.

Al-Imaam Ibn Maajah ya riwaito sahihin hadisin da Abdullaah Bn Abbaas da Ubaadah Bn As-Saamit (Radiyal Laahu Anhum) suka riwaito daga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« لاَ ضَرَرَ وَلاَ ضِرَارَ »

Ba cuta ba cutarwa. (Sahih Al-Jaami’: 7517).

Sai dai kuma lallai ’ya’ya su san cewa fa, da kai da kaya duk mallakan wuya ne, ma’ana: Su kansu tare da abin da suka mallaka duk na iyayensu ne, kamar yadda Al-Imaam Ibn Maajah (2379) ya riwaito sahihin hadisin da Jaabir Bn Abdillaah (Radiyal Laahu Anhumaa) ya riwaito cewa, wani mutum ya kawo ƙara wurin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa, yana da dukiya da yaya masu yawa, amma kuma mahaifinsa yana son ya lalatar masa da dukiyar! Shi ne Annabin Rahama (Sallal Laahu Alaihi Wa Alaa Alihi Wa Sahbihi Wa Sallam) ya ce

« أَنْتَ وَمَالُكَ لأَبِيكَ »

Kai da dukiyarka duk na mahaifinka ne. (Sahih Al-Jaami’: 1486).

Don haka kar ’ya’ya su ji zafi a kan ɗan abin da iyaye suke tsakura daga cikin abin da Allaah Ta’aala ya mallaka musu na dukiya. Amma a kasa ganin irin wannan damuwa da zafin a lokacin da matan aurensu ko ’ya’yansu ne suke salwantar na abin da ya fi hakan tsada da ƙima a wurinsu!

A taƙaice dai dole duk mu riƙa tuna sahihiyar maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alaa Alihi Wa Sahbihi Wa Sallam) cewa

« كُلُّكُمْ رَاعٍ ، وَكُلُّكُمْ مَسْئُولٌ عَنْ رَعِيَّتِهِ »

Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku za a tambaye shi a kan abin kiwonsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 4828, Sahih Muslim: 8698).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Ga Masu Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments