Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Yi Addu'ar Bude Sallah Idan Limam Yayi Ruku'u

TAMBAYA (88)

Assalama alaikum. Mln tambayace dani. Idan kazo kaga liman yatayar da sallah har yayi ruku u idan nima nayi kabbara nayi ruku un zan yi addu ar bude sallah neh kokuma kawai zan cigaba da sallah ne

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu

Alhamdulillah

Yin addu'ar sunnah ne, ba farillah bane ba kamar yanda Shaikh Nasiriddin al-Albany yayi bayani a cikin littafin Sifatus Salatin Naby minal takbiri ilat taslim ka'annaka taraha

Ga daya daga cikin addu'o'in bude salla

Kafin kayi kabbarar harama zaka ce: "Allahu Akbar kabira, walhamdulillahi katheera, wa subhanallahi bukratan wa asila", sai kuma kayi kabbara, sannan za ka fara bude karatun Fatiha da "Audhu billahi minash shaidanir rajim, min hamzihi wa nafkihi wa nafsih". Duk a sirrance ake addu'o'in

Idan kace zakayi addu'ar zaka iya rasa wannan raka'ar akan jam'i, duk da cewar ko da Tahiyya ka samu to ka samu ladan jam'in wannan sallar kamar yanda hadisi ya tabbata

Don haka a takaice zaka yi Takbiratul ihram ne ka bi Limamin

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments