Dawowar Maniyyi Bayan Saduwa

    TAMBAYA (98)

    Assalamu’alaikum warahmatullah

    Malam idan na sadu da mijina muna gamawa maniyyin se ya dawo Sannan kuma bayan nayi wanka daga baya se inji yana gangaromin har cinya na ko in ganshi a wando na

    Ya wanka ze kasancemin Nagode Allah ya kara haske

    AMSA

    Waalaikumussalam, warahmatullahi, Wabarakatuh

    Kalmar "gangarowa" da kikai amfani da ita hakan yasa bazaki sake wankan janaba ba, da dai ace sabo ne ya sake fitowa ta gabanki

    Abinda zakiyi shine; ki wanke shi daga cinyar taki sannan ki wanke na wandon da ruwa mai tsarki ki ci gaba da ibadarki

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.