Ticker

6/recent/ticker-posts

Yin Wankan Haila Da Janaba Da Niyya Daya

TAMBAYA (93)

Aslm malam ina wuni ubangiji Allah ya taimaka

Malam don Allah a amsa mun tambaya ta idan ina jinin al'ada bbu ynda zanyi muyi having intercourse da mijina to muda dan yin oral sex ba tare da ya wuce ka'idar musulunci ba amma wani bin ina releasing to malam idan na tashi yin wankan tsarki guda 2 zanyi ko na haila kawae zanyi a amsa mun don Allah

AMSA

Waalaikumussalam, warahmatullahi, Wabarakatuh

Alhamdulillah

To yar uwa, na fahimci cewar kina halin waswasi akan shin ya halatta kiyi wanka daya da niyya biyu

Ibn Qudamah yace: "Idan har akwai abubuwa guda biyu da suke wajabta wanka kamar fitar jinin haila da kuma janabah ko kuma haduwar namiji da mace (da releasing) sannan kuma sai mutum yayi niyyar tsarki daya da niyya biyu, wannan ya halatta. Wannan shine fahimtar magabata irinsu; Ataa’ Ibn Rabah, Abu Az-Zinaad, Rabee’ah, Maalik, Ash-Shaafi'i, Is-haaq, da kuma malaman mazhabin hanbaliyya"

(Al-Mughni)

Kenan kamar yanda mutum zai wanke jikinsa don kawar da dauda to hakanan mutum zai iya yin wanka da niyyar ibadah, anan kinga kayi niyya biyu kenan, na farko kawar da dattin jiki (kamar shi jinin haila din) na biyu kuma don yin ibadah ma'ana kayi wannan wankan ne saboda Allah Azzawajallah yana son masu tsarkakewa kamar yanda ya fada a cikin Suratul Baqara ayata 222

( وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ ۖ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ ۖ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ )

البقرة (222) Al-Baqara

Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakwa.

To saidai kuma jamhurin malamai sun ce bai halatta mutum yayi wanka daya da niyya biyu ba saboda hadisin "Innamal a'amali binniyyati" wanda Bukhari ya rawaito cewar kowanne aiki yana tare da niyya ne

Kamar yanda a bangaren azumi kowanne niyyar sa daban take, bai halatta ace mutum ya fake da azumin da ake binsa bashi ba kuma yayi niyya biyu don ganin yayi kamar irinsu Sitta Shawwal (guda shida) don neman lada biyu ba

Haka kuma an yiwa Shaikh Saleh al-Fawzaan tambaya game da hukuncin hade niyyar alwala a cikin wankan Janabah yace: "Idan mutum yayi wankan da niyyar alwala ya halatta. Idan kuma bai yi niyyar ba to zai yi alwala bayan ya kammala wankan"

(Al-Ijabat Al-Mukhtasarah)

Don gudun fadawa sabanin malamai abinda yafi dacewa shine kiyi amfani da sahihin hadisin nan da Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "Kowanne aiki yana tare da niyya ne" la'akari da shi wankan janaba din da zakiyi aiki ne mai zaman kansa shi ma kuma wankan haila din aiki ne mai zaman kansa

Ki fara gabatar da wankan haila din tunda jinin ne ya fara zuwan miki kafin saduwar wadda ta zama musabbabin da za'ayi wankan janabar

Kowannensu zaki yi niyyar ne a zuciya sabanin wasu da suke firtawa a fili

Allah ya sa mu dace. Ya tabbatar damu akan daidai

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments