Ticker

6/recent/ticker-posts

Wajibcin Mace Ta Nemi Izinin Mijinta Kafin Ta Fita Daga Gida

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Hadisan da suka nuna wajibcin mace ta nemi izinin mijinta kafin ta fita daga gida sahihai ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Da farko dai: Abu ne sananne cewa a duk inda mutane suka haɗu dole ne a samu shugabanci da adalci da ɗa’a da biyayya domin kyautata zamantakewa. Kuma babu wanda Allaah ya zaɓa ya mayar da shi shugaba a cikin gida domin a yi masa biyayya, sai miji (maigida). Allaah ya ce

ٱلرِّجَالُ قَوَّ ٰ⁠مُونَ عَلَى ٱلنِّسَاۤءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضࣲ وَبِمَاۤ أَنفَقُوا۟ مِنۡ أَمۡوَ ٰ⁠لِهِمۡۚ

Maza masu tsayuwa ne a kan mata saboda fifitawan da Allaah ya yi wa sashensu a kan sashe, kuma saboda abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu. (Surah An-Nisaa’: 34).

Ma’ana: Namiji shi ne Allaah ya ba aikin tsayuwa da yin gyara ko saitin matar aurensa.

A wani wurin kuma Allaah ya kira miji cewa shi ne shugaba a kan matarsa a cikin ƙissar Annabi Yuusuf (Alaihis Salaam), inda ya ce

وَأَلۡفَیَا سَیِّدَهَا لَدَا ٱلۡبَابِۚ

Kuma sai suka yi kiciɓis da shugabanta a dokin ƙofa. (Surah Yusuf: 25)

Tun da miji shi ne shugaba to lallai dole a yi masa ɗa’a da biyayya domin samun ɗorewar zamantakewa.

Daga cikin abin da ke nuna wannan matsayin na shugabancin miji akwai neman izininsa kafin mace ta zartar da komai da ke a ƙarƙashin ikonsa.

Kuma Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce

 وَقَرۡنَ فِی بُیُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجۡنَ تَبَرُّجَ ٱلۡجَـٰهِلِیَّةِ ٱلۡأُولَىٰۖ

Ku tabbata a cikin gidajenku, kuma kar ku fita da kwalliya irin fitar jahiliyyar farko. (Surah Al-Ahzaab: 33).

Kodayake wannan ayar a kan matan auren Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) uwayen muminai (Radiyal Laahu Anhunna) ne ta sauka, amma malamai sun yarda cewa, sauran mata muminai ma sun shiga cikin maganar. Haka Ibn Katheer da Al-Qurtubiy da sauran malaman Tafseer suka ambata a ƙarƙashin ayar.

Matan aure na kirki suna fita daga gidajensu ne kaɗai idan sun buƙatu ga hakan ko idan wata larura ta kama su. Daga cikin irin waɗannan buƙatun da suke fitar da ita akwai zuwa masallaci. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« إِذَا اسْتَأْذَنَتِ امْرَأَةُ أَحَدِكُمْ إِلَى الْمَسْجِدِ فَلاَ يَمْنَعْهَا »

Idan matar ɗayanku ta nemi izininsa domin ta je masallaci, to kar ya hana ta. (Sahih Al-Bukhaariy: 5238, Sahih Muslim: 1016, Al-Musnad: 4617).

Wannan hadisin sahihi ne, in ji malaman Hadisi irin su Al-Imaamul Albaaniy (Rahimahul Laah) a cikin Sahih Al-Jaami’: 319).

Daga nan muna fahimtar cewa: Idan dai har zuwa masallatai - wuraren da ya fi soyuwa a wurin Allaah Ubangijin Halittu a duniya domin yin ibadar da Allaah Ubangiji ya halicce mu dominta - sai mace ta nemi izinin mijin aurenta, to ina kuma ga zuwa wurin da ba wannan ba kamar zuwa wuraren bukukuwa ko taruka ko ma’aikatu ko makarantu ko kasuwanni - waɗanda su ne wuraren da Allaah ya fi ƙyamarsu a duniya?!

A taƙaice dai mace ta nemi izinin mijinta kafin ta fita daga gida abu ne sananne a cikin addini. Shiyasa tun tuni malaman fiqhu suka lissafa shi a cikin haƙƙoƙin miji da su ke a kan matar aure. (Sahih Fiqhis Sunnah: 3/174, Tamaamul Minnah: 3/116).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments