Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Auren Ɗandaudu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaamu Alaikum, Ni ne iyayen wata yarinyar da wani yaro ke neman ta da aure suka tambaya game da halayensa. Ni kuma sai na gaya musu iya abin da na sani cewa, shi yaron kirki ne. Bayan an yi auren ne kuma munanan halayensa suka bayyana cewa, shi ɗandaudu ne! Kwanan baya ya matsa wa matar wai sai ta bi shi tafiya zuwa garin da yake zuwa yin sana’arsa ta daudancin. Da ta ƙi sai ya ce: In ba ta yarda ta bi shi ba, to a bakin aurenta! Ba ta dai yarda ta bi shin ba. Daga baya shi kaɗai ya tafi, kuma bayan ya dawo da kwanaki huɗu sai matar ta haihu.

Tambayoyina a nan su ne

1. Menene hukuncin aurensu a matsayinsa na ɗandaudu?

2. Menene hukuncin aurensu bayan ya ce: A bakin Aurenta, tun da kuma ba ta bi shi ba?!

3. Idan ta saku daga waccan maganar, to saki nawa ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh

1. BINCIKE KAFIN AURE:

Kafin a ƙulla aure a musulunci daidai ne a tsananta bincike har a gano ko maaurata suna da siffofin da ake buƙata a cikin masu son auren juna a musulunci, kamar siffofin addini da kyawawan ɗabi’u a cikin namiji, ko kuwa a’a.

Annabi (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce

إِذَا أَتَاكُمْ مَنْ تَرْضَوْنَ دِينَهُ وَخُلُقَهُ فَزَوِّجُوهُ

Idan wanda kuka yarda da addininsa da ɗabi’unsa ya zo muku, to ku aurar masa.

 (Sahih At-Tirmiziy: 886).

Don haka, duk wanda ya rasa kyawawan ɗabi’u da halaye na-gari bai dace a ba shi aure ba, ko da kuwa yana da addini. Kamar yadda ba za a ba mai ɗabi’u kawai aure ba, har sai ya haɗa kyawawan ɗabi’un da samun nagartaccen addini.

Sannan duk wanda aka tambaya, kuma ya san haka ko kishiyar hakan game da wani manemin aure, to haƙƙi ne na wajibi a kansa ya faɗi gaskiya, kar ya yi ƙumbuya-ƙumbuya. Don kar a je a ɗaura auren da bai kamata ba, daga baya kuma a zo ana da-na-sani.

Ban ga kuwa yadda ɗandaudu zai zama mai ɗabi’u kyawawa, abin yabo ba a cikin kowace al’umma ma, ba wai mafificiyar al’ummar musulunci ba, balle kuma uwa-uba addini! Domin dai sakin fuska ko kyautan dukiya ko kusanci da manya ba su ne abubuwan dubawa ba a nan.

2. RASHIN SANI

Dayake tun da farko ba ka san cewa wannan saurayin ɗandaudu ne ba sai daga bayan aurensa, to dole ne ka yi gaggawan sanar da iyayen yarinyar wannan abin da zaran ka gano hakan, saboda dalilai guda biyu

(i) Kar ya zama ka bar su a cikin duhu, har kuma ya zama kamar ka yaudare su ko ka cuce su, ta nuna musu wanda bai dace ya zama surukinsu ba. Sai fa ko in kana ganin bayyana musu hakan a lokacin, zai haifar da wata mummunar matsalar da ta fi barin gaya musu!

(ii) Kare mutunci, saboda gaba. Domin kar ya zama sun ɗauke ka a matsayin mayaudari, har kuma su nisanci yin mu’amala da kai nan gaba saboda haka, alhali kuwa ba haka ka ke ba.

3. HUKUNCIN DAUDANCI

Daudanci, wanda ke da ma’anar: Namiji ya yi ƙoƙarin siffatuwa da siffofin mata, kamar ta karairaya murya a wurin magana, da lanlanƙwasa jiki wuri tafiya da sauran harkokinsa, da sanya tufafin mata, da yin kwalliya irin nasu, da sauran makamantan haka, duk waɗannan munanan ayyukan haram ne a musulunci, saboda dalilai masu yawa kamar haka

Sahabi Abdullaah Bn Amr (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce: Ya ji Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cewa:

 لَيْسَ مِنَّا مَنْ تَشَبَّهَ بِالرِّجَالِ مِنَ النِّسَاءِ ، وَلَا مَنْ تَشَبَّهَ بِالنِّسَاءِ مِنَ الرِّجَالِ

Duk wadda ta yi kama da maza daga cikin mata ba ta tare da mu, haka ma duk wanda ya yi kama da mata daga cikin maza.

Kuma Sahabi Abdullaah Bn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce

لَعَنَ النَّبِيُّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - الْمُخَنَّثِينَ مِنَ الرِّجَالِ ، وَالْمُتَرَجِّلَاتِ مِنَ النِّسَاءِ ، وَقاَلَ : أَخْرِجُوهُمْ مِنْ بُيُوتِكُمْ

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya la’anci masu kamantuwa da mata daga cikin maza, da kuma masu kamantuwa da maza daga cikin mata. Kuma ya ce: Ku fitar da su daga cikin gidajenku.

Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce:

فَأَخْرَجَ النَّبِيُّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - فُلَانَا ، وَأَخْرَجَ عُمَرُ فُلَانَا

Don haka, sai shi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fitar da wane; Umar kuma ya fitar da wane!

 

A wani lafazin kuma ya ce

لَعَنَ رَسُولُ اللهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - الْمُتَشَبِّهِينَ مِنَ الرِّجَالِ بِالنِّسَاءِ ، وَالْمُتَشَبِّهَاتِ مِنَ النِّسَاءِ بِالرِّجَالِ

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya la’anci masu kamantuwa da mata daga cikin maza, da masu kamantuwa da maza daga cikin mata.

Duk waɗannan hadisai ne sahihai ingantattu, waɗanda As-Shaikh Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) ya yi bayanin sahihancinsu a cikin littafinsa: Jilbaabul Mar’atil Muslimah a inda yake bayanin sharuɗɗan Hijabin Mace Musulma, sannan a ƙarshe ya ce:

Daga cikin waɗannan hadisan akwai hujja a fili ƙarara a kan haramcin kamantuwar mata da maza, haka ma akasinsa. Kuma gamammen hukunci ne: Ya haɗa tufafi da abin da ba tufafi ba.

Daga nan kuma sai ya cigaba da janyo maganganun malamai wurin sharhin hadisan, har zuwa inda ya kawo maganar da Al-Imaam At-Tabariy a kan riwaya ta biyu na hadisin Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa), kamar yadda Al-Haafiz Ibn Hajr ya takaito a cikin Fat-hul Baariy: (10/273-4):

 

Bai halatta ga maza su kamantu da mata ba a cikin tufafi ko kwalliyar da ta keɓanci matan, haka ma akasinsa.

Daga nan sai shi kuma shi At-Tabariy (Rahimahul Laahu) ya kawo maganar Ibn Abi-Jamrah inda ya ce

Zahirin wannan lafazin tsawatarwa ne daga kamantuwarta a cikin komai, amma kuma an gano daga waɗansu dalilan cewa abin nufi shi ne: Kamantuwa a cikin tufafi da kwalliya da wasu siffofi da harkoki da makamantansu kawai.

Sannan kuma ya ce

وَالْحِكْمَةُ فِي لَعْنِ مَنْ تَشَبَّهَ ، إِخْرَاجُهُ الشَّيْءَ عِنِ الصِّفَةِ الَّتِي وَضَعَهَا عَلَيْهِ أَحْكَمُ الْحُكَمَاءِ ، وَقَدْ أَشَارَ إِلَى ذَلِكَ فِي لَعْنِ الْوَاصِلَاتِ بقَوْلِهِ : (الْمُغَيِّرَاتِ خَلْقَ اللهِ)

Kuma hikimar da ta sa aka la’anci wanda ya yi kamantuwar ita ce

Domin ya fitar da siffar abu ne daga yadda Allaah Mafi-Hikimar Masu Hikima ya ajiye ta a kansa. Shiyasa ya yi nuni ga hakan a cikin la’antar mata masu sadar da gashin-kai, inda ya ce: Masu sauya halittar Allaah.  

Shi kuwa ɗandaudu a cikin ɗabi’unsa da harkokinsa duk ya karya waɗannan maganganun da suka zo a cikin hadisan nan.

Ban da kuma sauran ayyukan haram da yake yi, na yin hulɗa da matan da ba muharramansa ba: Ya shiga cikinsu, ya keɓance da su, ya kalli tsiraicinsu da siffofinsu, ya isar da bayanan haka ga masoyansu, ya haɗa su, ko ya nuna musu, ko kuma ma ya kai su wurin waɗanda za su yi zina da su, shi kuma a biya shi!!

4. AUREN ƊANDAUDU

Dayake ta hanyar aure ne ake samun fa’idoji masu yawa a rayuwar duniya da lahira, kamar haka

Hanyar aure ita ce hanya guda ɗaya tilo domin samu da yawaita zuri’a mai tsarki mai albarka, kuma mai kai wa ga yaɗuwar al’ummar da Annabi (Sallal Laahu ’Alaihi wa Alihi wa Sallam) zai yi alfahari da ita a ranar Lahira.

Hanyar aure hanya ce ta samun ’ya’yan kirki waɗanda za su amfanar da iyaye tun daga wannan duniyar har zuwa lahira.

Ta hanyar aure ake samun ƙananan yaya masu iya ceton iyayensu a wurin shiga gidan Aljannah a Lahira.

Aure hanya ce ta samun ’ya’yan kirki masu imani waɗanda ake fatar su bai wa musulmi da garuruwan musulmin kariya, kuma masu nema wa jama’ar musulmi gafara.

Aure hanya ce ta samun natsuwar rai da kwanciyar hankali da kuma samun ƙarin ƙauna da tausayi waɗanda Allaah Maɗaukakin Sarki yake samarwa a tsakanin ma’aurata.

Zai yiwu a samu irin waɗannan fa’idojin da makamantansu masu yawa a cikin auren ɗandaudu?

Don haka, babu yadda wasu iyaye masu mutunci za su yarda su aurar da ’yarsu ga irin wannan mutumin, kuma babu wata mace mai mutunci da za ta yarda ta zauna da namijin da ke da irin wannan ɗabi’ar ta daudanci. Haka kuma babu ɗa na-gari da zai yi alfahari ko murna da farin-ciki da mahaifin da yake da irin wannan halin na daudanci.

Amma tun da an riga an ɗaura musu aure har ma sun fara haihuwa, ya rage a wurin ita yarinyar da iyayenta da kuma sauran ’yan’uwa da abokan arziki su yi shawara a kan wannan al’amarin, su kalli fa’ida da rashin fa’idar cigaba da wannan auren. Musamman ma ta fuskar halaccin irin abin da zai cigaba da ciyar da ita da ’ya’yanta da shi, da kuma yadda tarbiyyar ’ya’yan za ta kasance a cikin jama’a. Sannan sai su ɗauki matakan da suka dace, yadda suka dace, kuma a daidai lokacin da ya dace. Kamar na kai maganar gaban adalin alƙalin musulunci, don ya taimaka wurin yin maganin irin wannan matsalar a cikin alumma.

5. NAU’UKAN SAKI

Furuci da saki nau’i biyu ne: Sarihi da Kinaya . Saki sarihi shi ne wanda ake fahimtar ma’anar sakin a cikinsa, wanda kuma ba ya ɗaukar wata ma’ana ko fassara in ba sakin ba. Kamar mutum ya ce wa matarsa: Na sake ki! Ko: Ke sakakkiya ce!

Da wannan irin furucin matar ta saku. Kuma ko da ya yi da’awar cewa ba sakin yake nufi ba, ba za a yarda da shi ba.

Don haka, kalmar: ‘A bakin Aurenki’ ya shiga cikin nau’in saki na kinaya ne ba na sarihi ba, in ji wasu malamai. Watau wanda mijin ya yi amfani da waɗansu kalmomin da ana iya fahimtar ma’anar saki a cikinsu, a lokaci guda kuma suna ɗaukar wata ma’anar da ba sakin ba, kamar ya ce: Tafi gidanku! Irin wannan ba ya zama saki sai a lokacin da mai faɗin maganar ya yi nufin sakin, watau ya niyyace shi.

Saboda abin da A’ishah ta faɗi cewa: Lokacin da aka kawo Ibnatul-Jawni ga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) kuma ya kusance ta, sai ta ce

 A’uzu Bil Laahi Minka!

Allaah ya tsare ni daga gare ka!

Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

عُذْتِ بِعَظِيمٍ ، الْحَقِي بِأَهْلِكِ

Tabbas! Kin nemi tsari da Mai Girma, tafi gidanku…!

 (Sahih Al-Bukhaariy: 5254).

A nan saki ne yake nufi.

Amma a cikin ƙissar su Kaab Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) lokacin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya sa aka yanke hulɗa da su saboda laifin da suka yi, har ya hana su kusantar matansu, sai Ka’ab ya ce wa matarsa

الْحَقِي بِأَهْلِكِ

Tafi gidanku…!

 (Sahih Al-Bukhaariy: 4418).

A nan kuma ba saki yake nufi ba.

Don haka, malamai suka ce: Duk sakin auren da ya zama na-kinaya ba na-sarihi a fili ƙarara wanda aka yi amfani da Kalmar Saki ba, ana buƙatar wanda ya yi shi ya ƙara bayanin manufarsa a kansa. Idan saki yake nufi sai a tabbatar masa da manufarsa.

Amma dai furta saki fiye da guda ɗaya a kalma guda ko a mazauni guda bidi’a ne, kuma ana ɗaukar sa a matsayin saki ɗaya ne, wanda kuma akwai kome a cikinsa, a magana mafi-ƙarfi a wurin malamai.

Idan kuma ba saki yake nufi ba, illa dai kawai yana nufin razanarwa ne ga matar, don ya hana ta aikata wani abu, ko ya ɗora ta a kan aikata wani abu, a nan ba a cewa matarsa ta saku.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇��𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments