Taruwa Don Addu’ar Mamaci

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, ko ya halatta dangin mamaci su taru mutane domin yi masa addu’a a ranar uku (3) ko bakwai (7) ko arba’in (40) da rasuwarsa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Da farko, ya kamata mu san cewa al’amarin janaza yana sashe ne na ibada a cikin Fiqhun Musulunci, wanda kuma ya wajaba a cikinsa a tsaya kyam a kan abin da shari’a ta tsayar ne kawai, ba tare da ƙari ko ragi ba. Saɓanin sashen al'amuran rayuwa a addini, wanda aka ba da dama mutum ya yi duk abin da yake so, har sai lokacin da Shari'a ta kafa masa doka, ta dakatar da shi.

    Don haka, daga cikin abin da Shari’a ta tanada na haƙƙoƙin mamaci a bayan rasuwarsa shi ne a yawaita yi masa addua kawai, kamar a lokacin da ya cika, da lokacin da aka bai wa mutum labarin rasuwarsa, da lokacin yi masa sallah, da bayan an gama rufe shi, da duk lokacin da aka tuna da shi. Ubangijinmu Subhaanahu Wa Ta'aala ya ce

    وَالَّذِيْنَ جَاۤءُوْ مِنْۢ بَعْدِهِمْ يَقُوْلُوْنَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَـنَا وَلِاِخْوَانِنَا الَّذِيْنَ سَبَقُوْنَا بِالْاِيْمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِىْ قُلُوْبِنَا غِلًّا لِّلَّذِيْنَ اٰمَنُوْا رَبَّنَاۤ اِنَّكَ رَءُوْفٌ رَّحِيْمٌ

    Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cwa, "Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai. (Surah Al-Hashr: 10)

    A duk waɗannan wuraren da Sunnah ya yi umurni da yi wa mamaci addu'a, ba ta keɓance yin addu’o’in da ƙarin bayanin cewa a tara jamaa ba a lokacin yin su, ko kuma a waɗansu ranaku na musamman, kamar uku ko bakwai ko arba'in ko shekara da makamantan hakan. Kamar yadda kuma ba ta nuna siffar addu’ar ba, kamar cewa wani ya riƙa yin addu'ar sauran jama'a kuma suna amsawa da cewa: Amin! Amin ba!

    Domin ko a maƙabarta bayan gama rufe shi, umurnin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya bayar shi ne

    « اسْتَغْفِرُوا لأَخِيكُمْ وَسَلُوا لَهُ التَّثْبِيتَ فَإِنَّهُ الآنَ يُسْأَلُ »

    Ku roƙa wa ɗan uwanku gafara, kuma ku roƙa masa samun tabbata, domin kuwa shi yanzun nan ana yi masa tambayoyi. (Abu-Daawud: 3223)

    Don haka, abinda ya ke wajibi a kan duk mai imani, a cikin wannan babin da sauran babukan addini makamantansa shi ne ya tsaya a inda Allaah ya tsayar da shi kawai, kamar dai yadda As-Shaikh Abdurrahmaan Al-Akhdariy ya faɗa

    وَيَقِفَ عِنْدَ أَمْرِهِ وَنَهْيِهِ

    Kuma ya tsaya a kan umurninsa (Shi Allaah) da haninsa.

    Amma abin da wani ya ce: Tun da dai shari’a ta yarda a yi addu’ar kuma ba ta keɓance masa rana ko wuri ba, to wanene ya hana yin addu’ar a rana ta uku ko ta bakwai ko ta arba’in?!!

    Faɗin wannan ya nuna rashin fahimta ko ƙwarewa ne a cikin ilimin Usuul ne, in ma ba a kira shi ha'inci ko ƙoƙarin rufe gaskiya ba. Domin abu ne sanannen a wurin malaman Usuul cewa: Asali a cikin Al-Ibaadaat haramci ne, watau ba a yin komai sai da umurni. Kuma asali a cikin Al-Muaamalaat halacci ne, watau ba a hana komai sai da dalili. Kuma mun riga mun ambaci cewa, ayyukan janaza, tun daga lokacin da aka zare ran mamaci har zuwa rufe shi, har kuma zuwa ga abubuwan da suka biyo bayansa ayyuka ne na ibada, ba al’ada ba ne. Don haka dole a bi koyarwar Sunnah Sahihiya a nan in ana son dacewa.

    Amma maganarsa cewa: Waye ya hana?! Shi ne wani malami ya amsa da cewa: Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ne suka hana

    يٰۤاَيُّهَا الَّذِيْنَ اٰمَنُوْا لَا تُقَدِّمُوْا بَيْنَ يَدَىِ اللّٰهِ وَرَسُوْلِهٖ وَ اتَّقُوا اللّٰهَۗاِنَّ اللّٰهَ سَمِيْعٌ عَلِيْمٌ

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da ManzonSa. Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani. (Surah Al-Hujuraat: 1)

    Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

    « مَنْ عَمِلَ عَمَلاً لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ »

    Duk wanda ya aikata wani aikin da babu umurninmu a kansa, to shi abin mayarwa ne. (Sahih Muslim: 4592).

    Allaah ya shiryar da mu.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.