Ticker

6/recent/ticker-posts

Mata Zasu Iya Ziyartar Makabarta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam, ina da tambaya akan ko ya halatta mata su ziyarci makabarta, don suyi addu’a ga magabatansu ??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Ya halatta mata su ziyarci Makabarta, amma kar su yawaita, saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya la’anci mata masu yawan ziyarar Makabarta, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi !!

Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya wuce wata mace tana kuka a jikin Kabari, sai ya ce mata “Ki ji tsoran Allah, ki yi hakuri” kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (1283), a cikin hadisin Manzon Allah bai hana ta ziyarar Kabari ba, kawai ya yi mata WA’AZI ne akan ruri da koke-koken da take yi, sannan Nana A’isha ta tambayi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam game da addu’ar da za ta yi in ta je Makabarta sai ya koya mata, kamar yadda ya zo a Sahihi Muslim a hadisi mai lamba ta (974), hakan sai ya nuna mustahabbancin zuwan mata Makabarta ba tare da yawaitawa ba.

Addu’ar ita ce kamar haka

اَلسَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ المؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنّا إِنْ شَاءَ اللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، وَيَرْحَمُ اللهُ الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنَّا وَالْمُسْتَأْخِرِينَ أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمْ الْعَافِيَةَ.

Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma'abota waɗannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu in Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji kan waɗanda suka gabata daga cikinmu da waɗanda suka yi saura. Ina rokon Allah aminci daga bala'i gare mu da gare ku.

Hadisin da aka rawaito cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya la’anci mata masu ziyartar Makabarta bai inganta ba, saboda a cikin sanadinsa akwai Salih Baazaam, shi kuma yana da rauni a wajan malaman Hadisi, kamar yadda Ibnu Abdulbarr ya ambata a Tamheed 3/234.

Don haka ya halatta mata su ziyarci Makabarta, saidai su kiyayi yawaitawa, saboda hadisin Farko da na ambata, da kuma ruri da koke-koke, saboda hadisin Bukhari da ya gabata

Don neman karin bayani duba: Almuhallaa 3/388 da kuma Almajmu’u 5/310.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments