Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Bukaci Mijinta Ya Sake Ta

TAMBAYA (50)

Meye matsayin sakin aure,  Idan matar ce tace tanason sakin. Rashin lpyr mijin ba wadda ake daukabace amman wadda se anyi wahala da ita

AMSA

Saki halas ne idan ya cike sharuddan da shari'a ta gindaya. Dukda cewar halas ne amman shi ne aikin da Allah yake qyama a cikin halastattun ayyukan mutane. Wannan shi ne dalilin dayasa Shaidan yafison sakin aure fiyeda kowanne irin laifi banda shirka

Kul'i kenan. Sai ya saketa ammanfa da sharadin xata maido masa da sadakin da ya bata saboda ita ce ta buqaci sakin da kanta ba wai mijinba

Kamata yayi ta ci gabada haqurin zama dashi tunda ai Allah bai saukarda cuta ba saida ya saukarda maganinta kamar yanda hadisi sahihi ya tabbata

Ko ana dauka dinma kamar irinsu HIV/AIDS, sickler, ciwon sanyi da sauransu, saikaga silar addu'a Allah ya dauke cutar kamar ba'a taba yi ba

Shawarata guda 2 ce, indai ita ce ta nemi sakin saboda tana takura to ta biyashi sadakin kawai a rabu tunda shari'a ta halasta hakan ko kuma ta ci gabada haquri tunda ai cuta ba mutuwa baceba. Watarana sai labari

Munga misalin hakan ya faru ga Annabi Ayuba AS, wanda saida ya rasa komai, ga rashin lafiya ta ci karfinsa amman da Allah ya qaddara waraka sai gashi ya bashi sauki ya kuma maido masa da duk abubuwan da ya rasa da kuma qari

Malaman tarihi sukace lokacin da Annabi Ayub AS yakai shekaru 70, sai ya rasa lafiyarsa da iyalansa. Ya samu cutar fata (zata iya zama smallpox) yanda gaba daya ilahirin fatarsa ya samu matsala in banda harshensa da kuma zuciyarsa. Bai yi qasa a gwiwa ba, ya koma ga Allah SWT ya amsa roqonsa kamar yanda Allah SWT ya labarta mana a cikin Suratu Anbiya:

( وَأَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الضُّرُّ وَأَنتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ )

الأنبياء (83) Al-Anbiyaa

Kuma da Ayyũba a sa'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shafe ni, alhali kuwa Kai ne Mafi rahamar masu rahama."

( فَاسْتَجَبْنَا لَهُ فَكَشَفْنَا مَا بِهِ مِن ضُرٍّ ۖ وَآتَيْنَاهُ أَهْلَهُ وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِّنْ عِندِنَا وَذِكْرَىٰ لِلْعَابِدِينَ )

الأنبياء (84) Al-Anbiyaa

Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kawo masa mutanesa da kwatank wacinsu tare da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunatarwa ga masu ibada.

Kuma indai har tayi imani da Allah ai dolene ta jira zuwan jarabawa kanar yanda Allah SWT ya fada:

( أَحَسِبَ النَّاسُ أَن يُتْرَكُوا أَن يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ )

العنكبوت (2) Al-Ankaboot

Ashe, mutane sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmani," alhali kuwa ba za a fitine su ba?"

Ayar gaba sai ta tabbatarda cewar ba ita kadai bace aka taba jarabta a rayuwa, an jarabci wadanda suka gabata ma:

( وَلَقَدْ فَتَنَّا الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ فَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ صَدَقُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْكَاذِبِينَ )

العنكبوت (3) Al-Ankaboot

Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabaninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.

An jarabci Annabi Ibrahim AS domin kafirai har wuta suka jefashi, Allah SWT ya kiyayeshi

Hakama Annabi Yunus AS ma'abocin kifi, Allah SWT ya tseratar dashi

Ga Annabi Yaqub AS wanda ya rasa idanuwansa silar bacewar dan sa Annabi Yusuf AS amman a karshe Allah SWT ya warkar dashi

Annabi Ayub AS ma haka Allah SWT ya jarabceshi da rashin lafiya saida yazamana ya rasa komai amman da ya haqura ya koma ga Allah sai ya samu waraka

Sannan shi kansa katimul anbiya, Manzon Allah SAW an jarabceshi da rasa yayansa. Ga kuma maraici tun tasowarsa. Ahakan yayi haquri saboda Allah SWT yana tareda masu haquri:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ )

البقرة (153) Al-Baqara

Ya ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku nmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tare da masu haƙuri.

An karbo daga Mus'ab bin Sa'd RA daga mahaifinsa Sa'd bin Abu Waqqas RA ya ce: Na tambayi ma'aikin Allah SAW, wadanne mutanene akafi jarabta ? Sai Annabi SAW ya ce: "Annabawa, sai mutane nagari sai, sai nagari. Mutum za'a gwadashi gwargwadon riqon addininsa, idan yana da riqon addini sosai to Allah zai jarabceshi dayawa, hakama idan yana sakwa-sakwa da addininsa to za'a jarabceshi gwargwadon hakan. Jarabawar rayuwa (da musibu kala-kala) zasu ci gabada kewayeshi har sai ya koma yana yawo a doron duniya ba tareda zunubi ko daya ba" (Sunan Ibn Majah 4023

Anan ina bata shawara a karo na biyu, ta dage da yawaita addu'a, da fadin Allah SWT:

( الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ )

البقرة (156) Al-Baqara

Waɗanda suke idan wata masĩfa ta same su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmawa."

Ta yawaita haquri domin kuwa kowanne tsananin yana tareda sauqi:

( فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا )

الشرح (5) Ash-Sharh

To, lalle ne tare da tsananin nan akwai wani sauƙi.

( إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا )

الشرح (6) Ash-Sharh

Lalle ne tare da tsananin nan akwai wani sauƙi.

A karshe ta dage da addu'ar Istikhara don miqawa Allah SWT zabin zama dashi ko kuma rabuwa dashi. Allah yasa mudace

Wabi hazal qadri kifaya. Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments