Ticker

6/recent/ticker-posts

Palestine: Halin Da ‘Yan Uwanmu Musulmai Suka Tsinci Kansu

Tambaya (51)

Shin abin da ke faruwa a Palestine yana da alaƙa da alamomin tashin alqiyama ?

AMSA

Tabbas ta'addanci da zaluncin da yahudawa suke ga yan uwanmu musulmai mazauna Zirin Gaza dake kasar Palestine yana da alaƙa da alamomin tashin alqiyama

Kafin hujjoji su biyo bayan bayanina yakamata mu san tarihin Isra'ela

Kisan gillar da sukewa yan uwanmu Musulmai abin dubawa ne wanda a satin da ya wuce sun kashe majinyata da likitoci da injiniyoyi dake aiki a asibitin "al-Ahli Baptist Hospital" harin da suka kai yayi sanadin salwantar rayukan musulmai sama da 500, to ammanfa dukda haka wannan zaluncin da suke a wannan zamanin bai kai kaso 1% cikin 100% na abin da sukayi a zamanin baya ba

Ko ka san cewar Yahudawa

Sun taba kashe Annabawa 43 a rana daya, da yammacin ranar kuma suka kashe musulmai masu wa'azi 170

Haka kuma Abdullahi Ibn Mas'ud (RA) ya ce: Banu Isra'ela sun taba kashe Annabawa guda 300 da hantsi suka koma suka bude shagunansu suka ci gaba da sabgar kasuwancinsu kamar ma ba'ayi komai ba

Hujjar wannan hadisi na cikin Athari na al-Imamu Ibn Abi Hatim wanda ya rawaito a cikin Tafisirinsa

Kasar Palestine ita ce kasar da akai tafiyar Isra'i daga Makka sannan kuma aka yi Mi'iraji a daidai masallachin al-Aqsa, waje ne mai albarka kamar yanda Allah SWT ya fada;

( سُبْحَانَ الَّذِي أَسْرَىٰ بِعَبْدِهِ لَيْلًا مِّنَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ إِلَى الْمَسْجِدِ الْأَقْصَى الَّذِي بَارَكْنَا حَوْلَهُ لِنُرِيَهُ مِنْ آيَاتِنَا ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ )

الإسراء (1) Al-Israa

Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da bawanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ayõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.

Nan ne garin da Annabi Musa AS yasha gwagwarmaya da Banu Isra'ila

( وَآتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ وَجَعَلْنَاهُ هُدًى لِّبَنِي إِسْرَائِيلَ أَلَّا تَتَّخِذُوا مِن دُونِي وَكِيلًا )

الإسراء (2) Al-Israa

Kuma Mun bai wa Mũsa littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isra'ila, cwa kada ku riƙi wani wakĩli baiciNa.

Duk da gatan da aka yi musu amman sun kasance azzalumai

( وَقَضَيْنَا إِلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ فِي الْكِتَابِ لَتُفْسِدُنَّ فِي الْأَرْضِ مَرَّتَيْنِ وَلَتَعْلُنَّ عُلُوًّا كَبِيرًا )

الإسراء (4) Al-Israa

Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isra'ĩla a cikin Littafi, cewa lalle ne, kuna yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kuna zalunci, zalunci mai girma.

Silar haka Allah SWT ya jarabcesu da sharrin Bukhtanasar ya kashesu, da kuma Adolf Hitler wanda yayi ta babbakasu da wuta a raye kamar a gidan biredi, silar gudun tsirar rai da sukai ne aka basu matsuguni a Palestine amman wai yanzu sune suke kashe musulman yankin alhalin an haramta musu wajen zama a duniyarnan

( فَإِذَا جَاءَ وَعْدُ أُولَاهُمَا بَعَثْنَا عَلَيْكُمْ عِبَادًا لَّنَا أُولِي بَأْسٍ شَدِيدٍ فَجَاسُوا خِلَالَ الدِّيَارِ ۚ وَكَانَ وَعْدًا مَّفْعُولًا )

الإسراء (5) Al-Israa

To idan wa'adin na farkonsu yaj, za Mu aika, a kanku waɗansu bayi Namu, ma'abũta yaƙi mafĩ tsanani, har su yi yawo a tsakanin gidajenku, kuma ya zama wa'adi abin aikatawa.

Allah ya basu ni'mah dayawa daya daga ciki shi ne ya tseratar dasu daga fitinar fir'auna (Ramses II) da suka ga mutuwarsa da al'ummarsa akan idanunsu;

( يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اذْكُرُوا نِعْمَتِيَ الَّتِي أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَنِّي فَضَّلْتُكُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ )

البقرة (47) Al-Baqara

Ya banĩ Isra'ĩla! Ku tuna ni'imaTa, wadda Na ni'imta a kanku, kuma lalle ne Ni, na fĩfĩta ku a kan talikai.

( وَإِذْ نَجَّيْنَاكُم مِّنْ آلِ فِرْعَوْنَ يَسُومُونَكُمْ سُوءَ الْعَذَابِ يُذَبِّحُونَ أَبْنَاءَكُمْ وَيَسْتَحْيُونَ نِسَاءَكُمْ ۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَاءٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَظِيمٌ )

البقرة (49) Al-Baqara

Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutanen Fir'auna, su na taya muku muguntar azaba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rayar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku.

( وَإِذْ فَرَقْنَا بِكُمُ الْبَحْرَ فَأَنجَيْنَاكُمْ وَأَغْرَقْنَا آلَ فِرْعَوْنَ وَأَنتُمْ تَنظُرُونَ )

البقرة (50) Al-Baqara

Kuma a lõkacin da Muka raba tku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutanen Fir'auna, alhali kuwa kũ kuna kallo.

To amman dukda wannan sai suka koma bautawa dan maraqi;

( وَإِذْ وَاعَدْنَا مُوسَىٰ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً ثُمَّ اتَّخَذْتُمُ الْعِجْلَ مِن بَعْدِهِ وَأَنتُمْ ظَالِمُونَ )

البقرة (51) Al-Baqara

Kuma a lõkacin da muka yi wa'adi ga Mũsa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bayansa, alhali kũ, kuna masu zalunci (da bauta masa).

( وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ يَا قَوْمِ إِنَّكُمْ ظَلَمْتُمْ أَنفُسَكُم بِاتِّخَاذِكُمُ الْعِجْلَ فَتُوبُوا إِلَىٰ بَارِئِكُمْ فَاقْتُلُوا أَنفُسَكُمْ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ عِندَ بَارِئِكُمْ فَتَابَ عَلَيْكُمْ ۚ إِنَّهُ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ )

البقرة (54) Al-Baqara

Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutanensa: "Ya mutanena! Lalle ne ku, kun zalunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kawunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.

A karshe suka ce sai sun ji maganar Allah SWT sannan zasuyi imani kamar  dai yanda Annabi Musa AS (Kalamullah) yake jin maganarSa ba tareda hijabi, bayan ya zabi mutane 70 a cikinsu sunje dutsen Dur Sina, sunji maganar Allah SWT amman sai sukace sai mun ga Allah tukunna, sai aka saukarda tsawa ta kashesu nan take;

( وَإِذْ قُلْتُمْ يَا مُوسَىٰ لَن نُّؤْمِنَ لَكَ حَتَّىٰ نَرَى اللَّهَ جَهْرَةً فَأَخَذَتْكُمُ الصَّاعِقَةُ وَأَنتُمْ تَنظُرُونَ )

البقرة (55) Al-Baqara

Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Musa! Ba za mu yi ĩmani ba dõminka, sai munga Allah bayyane," sabada haka tsawar nan ta kamaku, alhali kuwa kuna kallo.

( ثُمَّ بَعَثْنَاكُم مِّن بَعْدِ مَوْتِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ )

البقرة (56) Al-Baqara

Sa'an nan kuma Muka tayar da ku daga bayan mutuwarku, tsammaninku, kuna gõdwa.

Duk da an maido musu da rayukannasu sai suka ce yanzu kuma suna son a saukar musu da girgije saboda hasken rana yana takura musu kuma sukace su abinci daya ya ginshesu saidai a saukar musu da naman salwa da darba (zuma) daga Aljannah;

( وَظَلَّلْنَا عَلَيْكُمُ الْغَمَامَ وَأَنزَلْنَا عَلَيْكُمُ الْمَنَّ وَالسَّلْوَىٰ ۖ كُلُوا مِن طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ ۖ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ )

البقرة (57) Al-Baqara

Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga masu daɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zalunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zalunta.

Duk wannan falalar amman a karshe sukace mun gaji da abinci kala daya, ka roka mana Ubangijinka ya bamu alkama, albasa da sauransu;

( وَإِذْ قُلْتُمْ يَا مُوسَىٰ لَن نَّصْبِرَ عَلَىٰ طَعَامٍ وَاحِدٍ فَادْعُ لَنَا رَبَّكَ يُخْرِجْ لَنَا مِمَّا تُنبِتُ الْأَرْضُ مِن بَقْلِهَا وَقِثَّائِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَا ۖ قَالَ أَتَسْتَبْدِلُونَ الَّذِي هُوَ أَدْنَىٰ بِالَّذِي هُوَ خَيْرٌ ۚ اهْبِطُوا مِصْرًا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلْتُمْ ۗ وَضُرِبَتْ عَلَيْهِمُ الذِّلَّةُ وَالْمَسْكَنَةُ وَبَاءُوا بِغَضَبٍ مِّنَ اللَّهِ ۗ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَانُوا يَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَيَقْتُلُونَ النَّبِيِّينَ بِغَيْرِ الْحَقِّ ۗ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَوا وَّكَانُوا يَعْتَدُونَ )

البقرة (61) Al-Baqara

Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Mũsa! Ba za mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna nman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musu walaƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna kafirta da ayõyin Allah, kuma suna kashe Aannabawa, bada hakki ba. Wancan, sabõda saɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi.

Kuma a cikin wadannan Yahudawanne dai aka maida wasunsu birrai;

( وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ الَّذِينَ اعْتَدَوْا مِنكُمْ فِي السَّبْتِ فَقُلْنَا لَهُمْ كُونُوا قِرَدَةً خَاسِئِينَ )

البقرة (65) Al-Baqara

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu."

Kai akwai watarana da suka cewa Annabi Musa AS shi jahili ne;

( وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَن تَذْبَحُوا بَقَرَةً ۖ قَالُوا أَتَتَّخِذُنَا هُزُوًا ۖ قَالَ أَعُوذُ بِاللَّهِ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْجَاهِلِينَ )

البقرة (67) Al-Baqara

Kuma a lõkacin da Musa ya ce ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata saniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina nman tsari daga Allah da in kasance daga jahilai."

( قَالُوا ادْعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِيَ ۚ قَالَ إِنَّهُ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٌ لَّا فَارِضٌ وَلَا بِكْرٌ عَوَانٌ بَيْنَ ذَٰلِكَ ۖ فَافْعَلُوا مَا تُؤْمَرُونَ )

البقرة (68) Al-Baqara

Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mec ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita saniya ce; ba tsõfuwa ba, ba kuma budurwa ba, tsakatsaki ce a tsakanin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku."

( أَفَتَطْمَعُونَ أَن يُؤْمِنُوا لَكُمْ وَقَدْ كَانَ فَرِيقٌ مِّنْهُمْ يَسْمَعُونَ كَلَامَ اللَّهِ ثُمَّ يُحَرِّفُونَهُ مِن بَعْدِ مَا عَقَلُوهُ وَهُمْ يَعْلَمُونَ )

البقرة (75) Al-Baqara

Shin fa kuna tsammanin za su yi imani sabõda ku, alhali kuwa, haƙĩƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar da ita daga bayan sun gane ta, alhali sũ, suna sane?

Su ne kuma sukace wutar Jahannama basa ta qona su ba face na wasu kwanaki qididdigaggu;

( وَقَالُوا لَن تَمَسَّنَا النَّارُ إِلَّا أَيَّامًا مَّعْدُودَةً ۚ قُلْ أَتَّخَذْتُمْ عِندَ اللَّهِ عَهْدًا فَلَن يُخْلِفَ اللَّهُ عَهْدَهُ ۖ أَمْ تَقُولُونَ عَلَى اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ )

البقرة (80) Al-Baqara

Kuma suka ce: "Wuta ba za ta shafe mu ba, face, 'yan kwanuka ƙidayayyu."Ka ce: "Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai saɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?"

Sune masu kashe Annabawa ba adadi kuma sun tsani Mala'ika Jibrilu;

( وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ آمِنُوا بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ قَالُوا نُؤْمِنُ بِمَا أُنزِلَ عَلَيْنَا وَيَكْفُرُونَ بِمَا وَرَاءَهُ وَهُوَ الْحَقُّ مُصَدِّقًا لِّمَا مَعَهُمْ ۗ قُلْ فَلِمَ تَقْتُلُونَ أَنبِيَاءَ اللَّهِ مِن قَبْلُ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ )

البقرة (91) Al-Baqara

Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmani da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna ĩmani da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kafircwa da abin da ke bayansa, alhali kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tare da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabawan Allah gabanin wannan, idan kun kasance masu bayar da gaskiya?"

( قُلْ مَن كَانَ عَدُوًّا لِّجِبْرِيلَ فَإِنَّهُ نَزَّلَهُ عَلَىٰ قَلْبِكَ بِإِذْنِ اللَّهِ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ وَهُدًى وَبُشْرَىٰ لِلْمُؤْمِنِينَ )

البقرة (97) Al-Baqara

Ka ce: Wanda ya kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatawa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishara ga mũminai.

Kuma sune wadanda suke bautar gunkin Ba'al a zamanin Annabi Ilyas wanda a yanzu haka (a wani bincike da nayi) sun dawo da wannan bautar tunaninsu ta hakanne zasuyi nasara akan musulman Palestine;

( وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ )

الصافات (123) As-Saaffaat

Kuma lalle Ilyas, haƙĩƙa, yana daga Manzanni.

( إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَلَا تَتَّقُونَ )

الصافات (124) As-Saaffaat

A lõkacin da yake ce wa mutanensa, "Ashe, ba za ku yi taƙawa ba?"

( أَتَدْعُونَ بَعْلًا وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ الْخَالِقِينَ )

الصافات (125) As-Saaffaat

"Shin, kuna bauta wa Ba'al ne, kuma kuna barin Mafi kyautatawar masu halitta?"

( اللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ )

الصافات (126) As-Saaffaat

"Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"

Yakai mai karatu to Wannan fa shi ne kadan daga cikin sharrin banu Isra'ela (wanda a kalla sun kashe musulmai yan uwanmu  kusan 3,000 ko sama da hakan a cikin musulmai 2,300,000, mazauna Zirin Gaza). Saidai Alhamdulillah domin kuwa suma an kashe musu sama da Yahudawa 5,000. Har yanzu sun rasa gano wai ya akai sojojin Hamas suka samu manyan rokokin da sukai musu wannan babbar illa haka

Idan kuma muka koma tarihi, zamu ga cewar shekaru 2,000 kafin zuwan Annabi Isah AS, akwai Kan'anawa da suka zauna a wajen, suna jin yare 3, kananiyya (Can'an), araniyya (Aramaic), da arabiyya (Arabic)

Hijirar Annabi Ibrahim AS daga Oud ta kasar Iraqi zuwa Palestine, ya haifi Annabi Ismael da Ishaq AS, shekaru 3,000 kafin zuwan Annabi Isah AS, a zamanin Annabi Musa AS kuma Sarki Ramses II (Firauna) ya kori Banu Israela su bar Misra zuwa Palestine, wanda  hakan ya zama musabbanin halakarsa a cikin kogin Nile (Ruwan maliya) lokacin da yabi biyansu

Kun tonu tarihin Jaluta da Daluta ?, harma Annabi Dawuda AS ya kashe Jaluta, silar hakan Sarki Daluta ya bashi babban muqami, a karshe Allah SWT ya bashi sarauta da Annabta, ya haifi  Annabi Sulaiman AS, shi ma ya gajeshi harma ya mulki duniya, har suka hadu da Bilqisu ta musulunta

Sulaiman ya kafa daula 2, Yahuza da Israela, Buktanasar ya yaqi Palestine, shekaru 600 kafin zuwan Annabi Isah AS, yahudu suka riqe mulkin shekaru 400 kafin Annabi Isah AS. Kasar Japan, da Rumawa sukai zamani da Annabi Isah  AS, da'awarsa ta tsone musu ido silar hakan suka kashe Annabi Yahya AS (A garin Damascus) sunso kashe Annabi Isah AS amman sai akai sama dashi  sai suka gicciye mai kama dashi, kuma tabbas a karshen duniya zai dawo a matsayin Musulmi mai bin tafarkin Ahlus Sunnah

A shekarar 1917, General Alinbai, baturen England yaci Palestine da yaqi, ta sake fadawa karkashin mulkin mallakan turawan England kamar yanda Nigeria ta fada, har zuwa 1948, lokacin da suka dauki matsalar suka kaita majalissar dinkin duniya, akaita munafurci a karshe suka janye suka sa sharadin lallai sai an kafawa yahudawa daula a wajen saboda yabudawa sun warwatse kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin Suratul Isra

Su kansu turawa so suke su rabu da sharrinsu shiyasa suka dauki tsarin maida angulu gidanta na tsamiya, aka kafa musu daula aka bawa Palestine rabi wanda bai kai na yahudawa ba domin kuwa yahudawan anbasu waje mai kyau

Aka kwacewa musulmai wajen da suka mallaka wanda yakai eka miliyan 4, aka yiwa matansu fyade, aka fitardasu daga garuruwansu sama da guda 400, inda aka basu shima aka kara rabashi gida 2 (West Bank da Gaza), a karkashin ikon Israela, komai idan zai shiga ya fita saida izinin Israela

An dauke musu ruwa, wuta da sauransu. Yankin West bank, Fatah suke mulki, Gaza kuma yan Hamas suke mulki dukkansu Ahlus Sunnah na, amurka ke shawartar Israela su karya kowacce doka UN ta saka, an basu manyan makamai wadanda suka ninninka na jaziratul arab

Kwanannan aka yi hira da wani sojan Israela wanda ya ce yana shaawar yaga yaro dan Palestine yazo wucewa makaranta ya samu bindiga ya kasheshi, akace mutane nawa ka harbe ya ce baisan adadi ba amman kullum sai ya durawa bindigarsa harsashai 250 kuma baya dawowa da ko guda 1, su HAMAS abbreviation ne na Harafatul Maqawana Islamiyya

Dan gwagwarmayar ba amurken nan mai fashin baqi, Jackson Hinkle a yayinda yake dauko rahotannin musayar fursunonin Israela (Nurit Cooper da Yochaved Lifshitz) ya ce: kafafan yada labarai karya suke wa mutane la'akarida yanda ya ga Yahudawa suke shan shayi (tea & cookies) tareda yin musabaha da sojojin Hamas cikin fara'a da kuma kewar rabuwa

Sannan kuma a shafinsa na Twitter, ranar 23 ga watan October, 2023 da misalin karfe 9:29pm, ya dora hoton bomb (qirar amurka) wanda ya nuna cewar amurka ce take bawa Israela gudunmawa wajen kashe musulman Gaza

Sahabban da suka rayu a Palestine sun hada da; Ubadat bin Salih, Shaddad bin Aus, Usama bin Zayd, Wasilat bin Asqa, Da'iya alkalby (wanda Jibril AS yake bayyana da siga irin tasa), Aus bin Samit, Masud bin Aus, manyan malamai da suka bar tarihi Malik bin Dinar, Imam ash-Shafi'i, Sufyan at-thauri, Muhammad bin Muslim bin Shabiz zuhri

Haka kuma Sayyadina Umar RA tareda Abu Ubaidah RA sunje Palestine sun kwato Masjid al-Aqsa daga hannun Yahudawa. Tarihi ya tabbatar da cewar Abdulaziz Bin Marwan shi ne ya gina Qubbatus saqra (masallachin nan wanda ake saka hotonsa a jikin calendar, mai kallon masjid al-Aqsa shekara ta 72 bayan hijira)

Nuruddan Zanki baturkennan, shima ya bada gudunmawa a masallachin a zamanin Salahudden Ayyubi

A zamanin Annabi SAW saida aka kwashe wata 17 ana kallon Palestine (al-Aqsa) kafin a dawo da alqibla zuwa ga Ka'aba. Masjid al-Aqsa shi ne masallachi mafi daraja idan ka dauke Masallachin Harami (Ka'aba) da kuma Masjid an-Nabwy

A yanzu haka mayaqan Hamas sun kwacewa Banu Israela taswirarsu (Map) wanda yake a cikin wani Hard Disk mai dauke da planning din mallake duk inda suke so a duniya, wanda suke kiran taswirar da suna "Great Israel" wato Babbar Isar'ela wanda sunce har Saudi Arabia sai ta dawo karkashinsu saboda idan bamu mantaba ai suna da tarihi acan Madinar tun zamanin Annabi SAW, sunada alqaryu guda 3; Banu Nadir, Banu Quraiza da Banu Qainuqa. Kwanannan sukayiwa kasar Misra magana akan idan zata yarda ta karbi musulman Palestine ta basu wajen zama ita kuma zata yafe mata duk wani bashi da take bin Misra din amman Egypt bata amshi tayin ba

Amurka (USA) sun kawo jiragen ruwa manya guda 2 kowannensu a kalla akwai jiragen yaqi guda 70, kudin kowanne jirgin ruwan yakai 12bn dollars (wato dollars biliyon 2). Prime minister England yazo Israela ya ce muna taredaku shima Joe Biden ya ce yana goyon bayan kisan da akewa musulmai. Hakama akwai masu jahilan Christians yan Nigeria da suke jin dadi sabod ana kashe musulmai alhalin sun manta da cewar a satin da ya wuce Israela ta wullo makami mai linzami cikin asibitin Al-ahli Baptist Hospital wanda mallakin Christians ne, to anan yakamata kagane cewar su fa yahudawa kamar yanda suka tsani musulmai to haka suka tsani Nasara (Christians) indai kai ba nasu bane to karensu ma yafika a wajensu. Kuma baka isa ka shiga addininsu ba, su kansu kadai suka sani, shiyasa zakaji bahaushe na cewa "Yahudu tuba babu"

To ammanfa wai a haka zakaga mutanenmu musulmai sunata kwaikwayonsu ta hanyar bata lokaci wajen kallace-kallacen ball, wrestlings, fina-finansu na Hollywood da koyi da al'adunsu irinsu gayyato masu kida yayin gudanarda bukukuwa (Dj) kuma wai ahaka muke son Allah ya sa albarka a rayuwar zaman auren, ga kuma yin kwalliya (make up) da mata suke wanda yake canza yanayin halittunsu (kuma nunsan dai haramunne mutum ya canza halittar da Allah yayi masa) da kuma sauran abubuwa da yahudawa suka tunkudo mana kuma muka riqesu hannu bibbiyu muna dabbaqawa, wanda daman tuni Allah SWT ya gargademu da kada mu daukesu a matsayin majibinta;

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَىٰ أَوْلِيَاءَ ۘ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ )

المائدة (51) Al-Maaida

Ya ku waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi Yahudu da Nasara majiɓinta. Sashensu majiɓinci ne ga sashe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yana daga gare su. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.

( وَلَن تَرْضَىٰ عَنكَ الْيَهُودُ وَلَا النَّصَارَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ ۗ قُلْ إِنَّ هُدَى اللَّهِ هُوَ الْهُدَىٰ ۗ وَلَئِنِ اتَّبَعْتَ أَهْوَاءَهُم بَعْدَ الَّذِي جَاءَكَ مِنَ الْعِلْمِ ۙ مَا لَكَ مِنَ اللَّهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ )

البقرة (120) Al-Baqara

Kuma Yahũdu ba za su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasara ba za su yarda ba, sai ka bi irin aƙidarsu. Ka ce: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya." Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bayan abin da ya zo maka na ilmi, ba ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma babu wani mataimaki.

Kuma Annabi SAW ya ce zamu bisu sauda kafa gashi kuma din muna binsu wanda iya wannan kadai ya isa ya tabbatar mana da cewar alqiyama ta kusa, me ya rage: bayyanar Muhammad Bin Abdullahi (Imam Mahdi), bayyanar Dajjal sai kuma dawowar Annabi Isah AS wanda zai hallakashi a daidai kofarnan mai suna Bab al-Lud daje Palestine, sai kuma bayyanar Ya'juj da Ma'juj sai bayyanar Zi as-Suwaiqatan al-Afhaj wanda shi ne zai zo daga kasar Yemen ya rusa Ka'aba, sai mutuwar salihan bayi masu imani sai kuma aikata alfasha a bayyane (Wanda a yanzu haka 2023 dinnan, gwamnatin kasar Mexico tace kowa ya aikata abin da yake so na alfasha a bayyane) sai a rasa masu iya firta kalmar shahada, to akan wadannan fasiqanne Allah SWT zai tashi alqiyama, za'a ji sautin busar kahon Mala'ika Israfil a yankin kasar Palestine kuma anan dai Masjid al-Aqsa dinnan ne za'a tattara bayi ayi hisabi a wata ranar Juma'a wadda Allah SWT ne ya barwa kansa sanin wacce ce

Don haka a karshe ina son nayi amfani da wannan damar don janyo hankalin musulmai  da mu koma ga Allah mu yawaita Istighafari, domin kuwa naji yawancin malamai sunata cewa anya kuwa ba a kanmu za'ayi tashin alqiyama ba ?, wallahu a'alamu, don haka mu taya yan uwanmu na Gaza addu'ar Allah ya basu nasar akan wadannan azzaluman yahudawan. Allah ka karbi shahadarsu. Allah ka yafe mana ka yafe musu sannan ka sakamu tare dasu baki daya a Aljannatil Firdous

Ku turawa yan uwa da abokan arziqi domin mu amfana da saqon baki daya

A DUBA: Littafin Albidaya wan Nihaya wallafar Abubakar Alhafiz Ibn Khathir,  Hudubar Shaikh Professor Mansur Sokoto, Karatun Marigayi Shaikh Muhammad Auwal Albany, Karatun Shaikh Professor Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, Karatun Shaikh Dr. Abdallah Gadon Kaya, Karatun Shaikh Sulaiman Mahmud, Karatun Shaikh Musa Yusuf Asadussunnah, Karatun Shaikh Hamza Yusuf Hanson (President Zaytuna College, California, USA), Karatun Shaikh Bilal Asad, Karatun Shaikh Sulaiman Omar (Founder Yaqeen Institute, USA), mu daina kallon videos da BBC suke yadawa domin kuwa duk mallakin Yahudawane saidai a shawarce mu dinga bibiyar shafin Instagram na Motaz Azaiza (jajirtaccen musulmin dan jarida daga Palestine), ko Plestia Alaƙad, Ahmed Hijazi, Afaf Ahmed, Sara alsaqqa, Meera Adnan, da kuma YouTube channels irinsu; Sense Islam, Quran and Islam, One Path Network, Rational Believer. Sannan nayi amfani da Qur'ani tarjamar Hausa na marigayi Shaikh Abubakar Gumi (Rahimahullah)

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy

Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu anla ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments