Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Uba Yana da Haqqin Tilastawa Ɗansa Yasaki Matarsa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam uba ne yasa ɗansa ya Saki matarsa asakamakon rashin zaman lafiya da basuyi sam zaman yaki daɗi kuma ita uwargidan ita ta kirkiri rashin zaman lafiya kuma shi mijin yayi attempting raba masu gida se shi mahaifinsa ya hana so daga qarshe se ya ce masa tunda bashi quality na zama da mace 2 se ya saki amarya. ita kuma amarya bayan an saketa Se tace Insha Allah kamar yadda yasa ɗansa ya saketa bada haqqi ba shima insha Allah se ansa an saki yarsa watarana. To shi ne wasu suka ce sam bata kyauta ba. to don Allah malam yaya hukunci hakan shin daidai ne ita ta faɗi hakan haka zalika hukunci da mahaifin ya zartar shima daidai ne. Nagode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam.

Hakkin iyaye na ɗaya daga cikin manyan hakkoki da Allah Ya yi magana, haka aure na daga cikin sunnar kowane Annabi da Allah Ya aiko bisa doron kasa, har Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yake cewa “ Aure sunnah ta ne kuma duk wanda ya kyamace ta ba ya tare da ni”.

Amma duk da girman wannan hakki na iyaye Allah Bai rataya saki a hannun su ba. Gaskiya abinda uban yayi bai halattaba, alkaline kawai yake da wannan damar amma uba bashida wannan hurumin.

Zaman lafiya wannan ai wata jarabawace watarana saikaga ansamu zaman lafiyar.

Na biyu kuma shi ne abinda wannan matar tafada kuskure ne amma kuskuren bashida yawa wata fuskarma bata da laifi.

Abinda yasa nace tanada laifi tayi kuskure saboda lallai nasan anzalinceta to yakamata tayi Allah ya isa kawai tajira taga irin hukuncin da Allah yazama dakanshi yaga dama yayi mata amma ba ita ce yakamata tazaɓi irin sakamakon da za'ayi mataba.

Abinda yasa nace kuma batai kuskureba saboda babu laifi amuslunci azalinci mutum shima yanemi Allah yasakamar amma gaskiyar magana dai baikamata tace hakaba domin ita yar wannan mutumin bata dalaifi kuma kinzo kina rokon Allah yasa asaketa.

Sakin mutumin da aka tilasta; Dole ne miji ya kasance mai ra’ayin kansa, idan kuma har wasu za su yi amfani da matsayi na jini ko kusanci ko kuma karfi na mulki a bisa tilasci a sakar wa mutum mace to ba ta saku ba, ciki har da iyaye.

Sai dai mafi kyawu a duk lokacin da mahaifan mutum suka nuna masa ba su son wani abu, sai ya bi hanyar da ta dace don fahimtar da su ta yadda za su amince da abin, in kuma har suka cije a kan sai ya yi abin sai ya dubi girman darajar su da suka yi silar samar da shi a bisa doron kasa ya yi masu biyayya don neman yardar Allah.

Don haka ina kira ga iyayen da suka aukar da irin wannan saki da mazajen da aka sakar wa matan da ma waɗanda suka aura da dukkanin al’ummar musulmi da mu ji tsoron Allah sannan mu tuntubi malamai, don gaskiya akwai ganganci kuma za a rika afkawa cikin zina da gangan.

Da fatan Allah Ya shiryar da mu bisa tafarki na kwarai.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments