Ticker

6/recent/ticker-posts

Limancin Ƙaramin Yaro

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Shin ya halatta yaron da bai balaga ba ya yi limancin sallah. Wata ce ɗanta mai shekaru biyar yake jan ta sallah da yar'uwarsa. Ko hakan ya yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Malamai suna  da mabambantan ra’ayoyi a kan wannan mas’alar: A lokacin da wasu ke ganin ba zai yiwu yaron da bai balaga ba ya yi limancin sallah, wasu suna ganin ya halatta ya yi. Matuƙar dai yaron ya waye, kuma ya san abin da ake nufi da sallar, kuma ya iya kawo ta daidai gwargwado, tare da rukunnanta da sharuɗɗanta har zuwa sallama, shikenan.

Dalilinsu kuwa shi ne hadisin da Al-Bukhaariy (4302) ya riwaito cewa Sahabi Amru Bn Salamah (Radiyal Laahu Anhu) ya zama limamin mutanen ƙauyensu saboda shi ne ya fi su karatun Alqurani, a lokacin yana ɗan shekaru shida zuwa bakwai. Kuma ba a ji Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi musun hakan ba.

Faɗin cewa: Ai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai san sun yi hakan ba, don ba a tare da shi su ke ba a lokacin, malaman sun bayar da martani ga hakan da cewa: Ko da a ƙaddara cewa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai san hakan ba, ai kowa ya san Ubangijinsa (Subhaanahu Wa Taaala) ya san da aukuwar hakan. In da kuwa ba daidai suka aikata ba, ai da ya saukar da wahayi domin faɗakar da shi hakan, irin yadda ya faɗakar da shi a lokacin da ya fara yin sallah da takalmin da ke ɗauke da najasa. Kuma da ma Allaah Ta’aala ya ce:

وَإِن تَسۡـَٔلُوا۟ عَنۡهَا حِینَ یُنَزَّلُ ٱلۡقُرۡءَانُ تُبۡدَ لَكُمۡ

Kuma idan kuka yi tambaya a kan al’amari a lokacin da ake saukar da Alqur’ani sai a yi muku bayani. (Surah Al-Maa’idah: 101).

Amma game da wannan mas’alar, me ya sa ita mahaifiyar yaran ba za ta shugabance su ba kawai, a wuce wurin? Ko yaron ya fi ta sanin Alqur’ani ne? Meye laifi idan ita ta yi musu limanci? Ba ga Sahabiya Ummu-Waraqah (Radiyal Laahu Anhaa) ta kasance tana yi wa mutanen gidanta limanci ba?! (Sahih Abi-Daawud: 553).

Daga baya idan yaron ya ƙara girma, kamar idan ya kai shekaru shida zuwa bakwai sai ta fara sakam masa ragamar limancin, kamar yadda hadisin Amr Bn Salamah ya nuna. Tare da cewa, in dai ba da wata larura ba, kamata ya yi a lokacin ya riƙa tafiya masallaci ne tare da mahaifinsa yana yin sallolinsa na farilla a bayan liman.

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments