Ticker

6/recent/ticker-posts

Neman Saki Don Miji Ba Ya Adalci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Shin ko laifi ne idan na nemi saki daga mijina sakamakon ba ya min adalci, don ba ya so na?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Asali dai ya halatta mace ta nemi mijinta ya sake ta, idan ba ta son shi, saboda hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy (5273) ya riwaito daga Sahabi Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa: Matar auren Thaabit Bn Qaisin (Radiyal Laahu Anhumaa) ta zo wurin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ta ce: Ni dai ba na zargin Thaabit Bn Qaisin da wani mummunan abu a cikin ɗabi’a ko addini, sai dai kaɗai ina ƙyamar kafirci ne a cikin musulunci! Sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« أَتَرُدِّينَ عَلَيْهِ حَدِيقَتَهُ » .

Za ki mayar masa da lambunsa kenan?

Ta ce: E. Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce masa

« اقْبَلِ الْحَدِيقَةَ وَطَلِّقْهَا تَطْلِيقَةً »

Karɓi lambunka, kuma ka sake ta saki guda.

Amma kuma in ba da dalili ƙwaƙƙwara ba haram ne mace ta nemi mijinta ya sake ta, saboda hadisin da Al-Imaam Abu-Daawud (2226) da At-Tirmiziy (1187) suka riwaito daga Thaubaan (Radiyal Laahu Anhu) daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« أَيُّمَا امْرَأَةٍ سَأَلَتْ زَوْجَهَا طَلاَقًا فِى غَيْرِ مَا بَأْسٍ فَحَرَامٌ عَلَيْهَا رَائِحَةُ الْجَنَّةِ »

Duk wata matar da ta nemi saki daga wurin mijinta ba da wani dalili muhimmi ba, to kuwa ƙamshin Aljannah haram ne a gare ta.

Sannan kuma ba ki yi bayanin me kike nufi da cewa: ‘ba ya miki adalci’ ba. Idan kina nufin adalci a wurin soyayyar zuci da sha’awar saduwa da sauran makamantan haka, to wannan ba abu ne mai yiwuwa ba tun daga nassin Alqur’ani

وَلَنْ تَسْتَطِيْعُوْۤا اَنْ تَعْدِلُوْا بَيْنَ النِّسَاۤءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ فَلَا تَمِيْلُوْا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوْهَا كَالْمُعَلَّقَةِۗوَاِنْ تُصْلِحُوْا وَتَتَّقُوْا فَاِنَّ اللّٰهَ كَانَ غَفُوْرًا رَّحِيْمً

Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. (Surah: An-Nisaa, Ayat: 129)

Idan kuwa kina nufin ba ya yin adalci a cikin abubuwan da su ke a fili ne a bayyane, kamar a wurin rabon kwana da abinci da tufafi da makamantan haka, to a nan ya janyo wa kansa wani babban zunubi ne. Kuma neman ya sake ki ba ita ce hanyar warware matsalar ba. Kamata ya yi ki tsaya ki cigaba da janyo hankalinsa, ko ki sanar da wanda zai iya janyo hankalinsa cikin hikima da kyakkyawan wa’azi. Me yiwuwa Allaah ya sa ya gane ya dawo kan hanya, ke kuma ki samu ladan da ya fi jajayen raƙumma, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa game da wanda Allaah ya shiryar da wani mutum ta hanyarsa.

Idan kuma, kamar yadda kika ce, ba ya son ki ne, to ai shi ya kamata ya ɗauki duk matakin da ya dace kamar ya sake ki, ba wai ke ki nemi sakin ba. Tun tuni dai Allaah Ta’aala ya ja kunnen mazaje

وَاِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاۤءَ فَبَلَغْنَ اَجَلَهُنَّ فَاَمْسِكُوْهُنَّ بِمَعْرُوْفٍ اَوْ سَرِّحُوْهُنَّ بِمَعْرُوْفٍۗ وَلَا تُمْسِكُوْهُنَّ ضِرَارًا لِّتَعْتَدُوْاۚوَمَنْ يَّفْعَلْ ذٰلِكَ فَقَدْ ظَلَمَ نَفْسَهٗۗ وَلَا تَتَّخِذُوْۤا اٰيٰتِ اللّٰهِ هُزُوًا وَّاذْكُرُوْا نِعْمَتَ اللّٰهِ عَلَيْكُمْ وَمَاۤ اَنْزَلَ عَلَيْكُمْ مِّنَ الْكِتٰبِ وَالْحِكْمَةِ يَعِظُكُمْ بِهٖۗ وَاتَّقُوا اللّٰهَ وَاعْلَمُوْۤا اَنَّ اللّٰهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيْمٌ

Kuma idan kun saki mãta, sa'annan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhri ko ku sallame su da alhri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne. (Surah: Al-Baqara, Ayat: 231)

Amma idan a bayan duk waɗannan bayanan kin ga ba za ki iya yin haƙurin jurewa ba, to kamata ya yi ki fara sanar da manyansa, kafin manyanki waɗanda suka ɗaura muku auren, domin su zauna su binciki al’amarin, kuma su samar da mafita. Allaah Ta’aala dai cewa ya yi

Surah: An-Nisaa, Ayat: 35

وَاِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوْا حَكَمًا مِّنْ اَهْلِهٖ وَحَكَمًا مِّنْ اَهْلِهَاۚاِنْ يُّرِيْدَاۤ اِصْلَاحًا يُّوَفِّـقِ اللّٰهُ بَيْنَهُمَاۗاِنَّ اللّٰهَ كَانَ عَلِيْمًا خَبِيْرًا

Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Turo tambayar ka ta WhatsApp number, banda kira: 08164363661

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments