Ticker

6/recent/ticker-posts

Zargin Musulunci Da Ta’addanci: Shin Musulmai ‘Yan Ta’adda Ne?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Malam, wace amsa za ka bayar ga kafiran da suke zargin Musulunci da ta’addanci, suna kafa hujja da hadisin da ya ce: ‘An umurce ni da in yaƙi mutane?!’

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

[1] Mutane a ƙasar nan iri biyu ne: Musulmi da waɗanda ba musulmi ba. Kowannensu kuma nau’uka biyu ne: Masana da marasa sani. Galibi marasa sani sun fi yawaita surutu da hayaniya, a daidai lokacin da su kuma masanan suka fi ƙoƙarin koyar da mabiya sahihin addininsu.

[2] Dukkan musulmi da ya tashi har ya girma a cikin gidan mutunci na musulunci kuma ya samu sahihiyar tarbiyya ya san cewa, Addinin Musulunci shi ne kaɗai addinin gaskiya, wanda Allaah ya yarda ya zaɓe shi domin al’ummar duniya, ba tare da bambancin harshe ko jinsi ko yankin ƙasa ko wuri ba. (Surah Al-Imraan: 19, 38).

[3] Waɗanda ba musulmi ba a ƙasar nan nau’i biyu ne: Kafirai mabiya addinin gargajiya daga cikin matsafa da maguzawa da makamantansu, waɗanda ba su cika magana ko tallata aƙidarsu da addininsu ba. Sai kuma kiristoci masu jingina kansu ga addinin da Annabi Isaa Al-Maseeh (Alaihis Salaam) ya kawo. A cikinsu ne aka fi samun masu yawaita surutu da hayaniya da tsokana ko takalar musulmi a duk lokacin da suka samu dama da iko.

[4] Bayar da martani ko amsa a kan irin waɗannan mas’alolin bai cika burge ni ba, domin abu ne sananne cewa, duk yadda aka yi ƙoƙarin gamsar da su da hujjoji da kyar ake samun amincewa ko yarda daga wurinsu. Shiyasa ba na ganin wata fa’ida ga shigar da kaina a cikin irin waɗannan matsalolin, saboda a fahimtata ɓata lokaci ne kawai.

[5] Amma dayake wannan tambayar wani ƙaramin ɗalibin makarantar boko ne ya zo da ita a cikin guntuwar takarda, wanda kuma daga makarantarsu ne aka aiko shi da ita, sai na ji tsoron kar yin shiru a kan mas’alar ya zama taimakawa wurin cigaba da saka matasa da ƙananan yaranmu cikin rikici, ko a sa musu shakku a cikin sahihin addininsu. Daga nan kuma a samu daman shigar da su wani addinin da ba shi ba. Wannan ya sa dole in kalli matsalar, in bayar da ɗan abin da na sani na ilimi a kanta.

Allaah ya ƙara mana taimako da ilimi mai amfani.

[6] Da farko dai dole kowa ya san cewa, ba a samun kyakkyawar fahimta a kan al’amari a cikin musulunci ta kallon wani nassi ƙwara ɗaya ko biyu su kaɗai kawai a fanɗare. Dole sai an tattaro kan dukkan nassoshi a kan al’amarin daga cikin Alqur’ani da Sunnah Sahihiya kafin a samu cikakken bayani gamsasshe. Wannan ne matafiyar malamai.

[7] A gaskiya wannan hadisin ba shi ne kaɗai abin da suka gutsuro daga cikin nassoshin Alqur’ani da Sunnah domin irin wannan manufar ba. Na taɓa ganin inda suka ciro sassan ayoyi har goma sha-biyu domin suka da zargin addinin musulunci cewa yana goya wa ’yan ta’adda da ta’addanci baya! Amma idan mai bincike ya koma ga inda ayoyin su ke a cikin Alqur’ani, kuma ya karanci yadda suka zo a cikin tsarin magana, sai ya tarar ba irin abin da mai ciro su yake son nunawa suke nunawa ba.

[8] Har wannan hadisin ma idan aka koma asalinsa za a ga shi ma ba abin da ake son nunawa ne yake nunawa ba. Domin an fara kafa hujja da shi tun a zamanin manyan halifofin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), wato Abubakar da Umar (Radiyal Laahu Anhumaa). Sun nuna kafiran da suka yi ridda daga musulunci a bayan wucewar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) waɗanda kuma har suka ƙi tsayar da dokokin shari’ar musulunci, su ne aka kafa hujja da hadisin domin yaƙarsu, da komo da su cikin musulunci. (Sahih Abi-Daawud: 1558).

[9] Shiyasa waɗansu malamai suke ganin kalmar ‘mutanen’ da aka umurce shi da ya yaƙe su a cikin hadisin Larabawa ne kaɗai yake nufi, amma ba dukkan mutanen duniya ba. Ko da ma an ɗauki fassarar da ta fi na cewa dukkan kafirai ake nufi, yana da kyau a san cewa yaƙi a musulunci iri biyu ne:

(i) Akwai yaƙin kare kai da kore farmaki da ta’addancin kafirai da maƙiya daga garuruwa da ƙasashen musulmi. Wannan shi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fara yi a lokacin da mushirikai da Yahudawa suka haɗa kai domin gallaza masa shi da mabiyansa.

(ii) Sai kuma yaƙin cin ƙasashe da faɗaɗa daular musulunci a lokacin da ya samu ƙarfi da iko, kamar dai yadda kowaɗanne dauloli masu ƙarfi suke yi a kowane zamani. Yadda dai muke ganin manyan ƙasashen duniya a yau suna ta yi wa ƙasashen da suka fi su ƙarfi, musamman na yammacin Afirka.

[10] Amma kuma dole a nan a tuna cewa: Akwai dokoki da ƙa’idoji da addinin musulunci ya shimfiɗa a wurin kowane yaƙi, waɗanda suka fi na kowane addini da kowaɗanne mutane kyawun tsari. Daga cikin dokokin da ake koyar da sojojin musulunci akwai cewa:

(i) Kar su kashe waɗanda ba mayaƙa ba daga cikin maƙiyansu, kamar mata da yara da tsofaffi da mahaukata da malaman addini a wuraren bautarsu. Kar su daddatsa matacce ko su ƙona shi da wuta. Kar kuma su karkashe dabbobi ko su lalata ruwan sha da abinci! (Tamaamul Minnah: 4/402).

(ii) Kuma duk lokacin da maƙiya suka nemi a tsagaita wuta a yi sulhu, musulunci ya umurci shugabannin musulmi da su amince da yin sulhun. Domin zaman lafiya ya fi alkhairi fiye da tashin hankali da yaƙi. (Surah Al-Anfaal: 61).

(iii) Haka duk lokacin da wani daga cikin sojojin abokan gaba ya furta Kalmar Shahada mai nuna ya musulunta, ko da kuwa a halin takura da tsoron mutuwa ne, ba a yarda musulmi ya kashe shi ba. (Sahih Al-Bukhaariy: 4019, sahih Muslim: 95).

[11] Yanzu za a haɗa waɗannan dokokin da irin abin da muka ga ya faru a lokacin da sojojin taron dangi a ƙarƙashin jagorancin kafirai suka shiga ƙasashen musulmi da yaƙi, kamar a Andalus a shekarun baya, ko kuma a Iraq da Afghanistan a ’yan shekarun nan? Mata da yara da tsofaffi nawa ne suka karkashe su haka siddan? Kuma matan aure da ’yan mata nawa ne suka yi wa fyaɗe?!

[12] Irin wannan fa shi ke rubuce a cikin littafan addininsu, kamar a cikin Littafin Lissafi na cikin Tsohon Alƙawari na Littafin Baibul:

(i) A nan ne aka nuna yadda sojojin Isra’ila suka karkashe dukkan mazajen Madayanawa da suka kai wa hari, wato suka kashe dukkan samari da dattijai da tsofaffi maza na garin, kuma suka ƙona dukkan birane da sansanoninsu da wuta ƙurmus! (Lissafi, 31: 7-10).

(ii) Kuma bayan sun koma da kamammun yaƙi daga cikin mata da yara da dabbobi da sauran kayayyakin ganima, wai sai Annabinsu a lokacin ya yi fushi da kwamandojin yaƙin, domin sun bar matan a raye ba su karkashe su ba! (Lissafi, 31: 14-15).

(iii) Don haka, nan take ya bayar da odar cewa a karkashe dukkan ƙananan yaran maza. Haka ma dukkan macen da ta taɓa kwanciya da namiji. Amma ƙananan ’yan matan da ba su kai girman sanin namiji ba a bar su a raye domin amfanin sojojin! (Lissafi, 31: 17-18).

[13] Wannan shiyasa malamai a yau suke kukan cewa, waɗannan ayyukan ta’addanci da suke aukuwa a yankin Arewa da sauran sassan ƙasar nan, kodayake ana ta ƙoƙarin jingina su ga musulunci, amma ba su yi kama da ayyukan musulmi ba. Sun fi kama da irin waɗancan ayyukan na sojojin Isra’ila a cikin baibul.

[14] Masu aikata su a cikinmu suna ne kaɗai suke da shi na musulunci, amma ayyukan ba su nuna ɗabi’u da halayen musulmi da musulunci ba ko kaɗan. Idan ba haka ba, meyasa duk kashe-kashen da sauran ayyukan ta’addancin yake ta cin yankuna da garuruwan musulmi ne, amma yana barin kafirai da yankunansu da garuruwansu?!

[15] Masu bincike sun tabbatar da cewa, makirci kawai ake shirya wa musulunci domin duniya ta zarge shi da abin da ba shi yake aikatawa ba. An ce baƙaƙen arna maɓarnata kuma mahandama ’yan jari-hujja daga ƙasashen ƙetare ne suke ɗaukar nauyin koyar da waɗannan matasan dabarun yaƙin ta’addanci a cikin dazuzzuka, kuma su ke ba su muggan makamai domin su yi musu waɗannan ayyukan, su kuma su cigaba da sace ma’adinai da sauran kayan arzikin da Allaah ya huwace mana!

Allaah ya kare mu gaba-ɗaya daga makircin makirai.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi


Post a Comment

0 Comments