Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Mai Yawan Bukata Ne, Ina Neman Shawara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam da fatan kana lfy tambaya ta ita ce mace ce da mijinta kullum sai ya nemeta wani lokacin ma har sau biyu da rana da daddare in ba da azumi bane inda azumi kuma kullum da daddare ita kuma hakan Yana damunta kasancewar kowane lokaci in dai yazo kusa da ita sai ya bukaci saduwa, in ta nuna Tana San hutawa kuma sai ya bata rai har ta kai ga magana ma ba sosai yake mata, shin in taki akwai laifi sabida yanayin gajiya da aikin gida dana gurin aikinta ita ma'aikaciyace ko tsallaken kwana ɗaya tace suyi sai ya damu mallam menene shawara tunda ita ma tana da hakki a kansa. Sannan yanzu haka Tana da karamin cikin da bai wuce yan satika ba shin ba matsala game da cikin nata.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wajibi ne idan har ya Nemeki ki bashi Kanki. Sabida Hadisi Sahihi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace IDAN MACE TA KAURACEWA SHIMFIDAR MIJINTA ALLAH YANA FUSHI DA ITA, HAR SAI IDAN MIJINTA NE YA YAFE MATA. KO HAR SAI GARI YA WAYE.

Ki ƙara haƙuri, ki tuna cewa aikin ibada ko bautar Allaah na samun lada kike yi. Galibi aikin ibada yana wahalarwa ga rai, ana buƙatar juriya kafin a kai ga biyan buƙata, in shà Allâh.

Idan kuma ya kai gaɓar da ba zaki iya ɗauka ba, Ki zauna da mijinki ki nuna masa halin da kike ciki a sakamakon hakan ko zai iya ragewa daga buƙatar tasa, Idan ba zai iya ragewa ba, ki bashi Shawara akan ya kara Aure. Domin kina Samun hutun da kike Bukata. Tinda ke kaɗai ba zaki Iya gamsar da shi ba.

Da Alama kuma ya Aureki ne a Bazawara. Sabida Akasarin bazawara kana iya samunta ne a yadda Mijinta na baya ya Sabar Mata. Idan bai Sabar mata da yawan Bukata ta da Namiji ba. Haka zaka same ta. A Matsayin Mace Wadda Ba ta son Takurawa. Haka zalika idan ka same Macen da Mijinta Na Baya ya Sabar mata akan yawan Bukata, to fa haka zaka sameta. Wanda idan har kai ba haka kake ba. Zata Iya Fitinarka ko kuma ta Nemi sai ta Koma inda ta fito. Sabida Samun Biyan Bukatarta ta da Namiji.

Wannan ne ma yasa Wasu suke Tsoron Auren Bazawara kai tsaye. Sabida zaka ga Mutum ya haɗu da wadda ta fi karfinsa. Sakamakon sabon da Mijinta na baya yayi Mata ya zarta irin Naka. Kamar Yadda haka yake Faruwa wani Lokacin ita matar ce take hawa Zarra. Sakamakon Mijin ta na baya bashi da yawan Bukata Alhalin ya sabar Mata akan Hakan. Gashi a yanzu Kuma Ta Auri wanda yake da yawan Bukata.

Wannan ne ma yasa Ni Nake ganin, Yana da kyau indai har Namiji da mace sun san Aure za su yi Tsakanin su da Allah. Su fito su Gayawa Junansu gaskiya. Yadda Karfin Sha'awarsu yake. Ma'ana ya gaya mata Shi fa yana da yawan Bukata. Idan mace ta ga ba matsala Shikenan. Haka zalika Ita ma ta fito ta gaya masa tana da yawan Bukata. Idan Yaga zai Iya shikenan. Amma Aji Tsoron Allah, kuma hakan ya zama Magana ce ta Sirri a Tsakanin su.

 Kinga kenan idan Abin Nasu zai yiwu Shikenan. Idan kuma ba zai yiwu ba. Sai su Hakura kowa ya Kama Gabansa. Sabida wata matar Irin wannan Matsalar ce ta fito da ita daga gidan Mijinta. Ma'ana Mijin yana da yawan Bukatar da ita ba zata Iya ba. Ko kuma ita tana da yawan Bukata. Shi kuma Mijin ba haka yake ba. Amma idan aka yi magana a Sirri bisa Amana. Hakan inaga babu wata matsala da za'a Fuskanta a nan gaba.  

Duk da cewar Anfi Samun wannan Matsalar ga Maza. Sai ka ga Namiji ya Auri Mace Alhalin ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai iya Gamsar da ita. Nufinsa shi ya auri mace akan ta Zame masa Yar Aikace-aikace. Wanda kuma wannan ba zai yiwu ba. Sai ka samu tana Neman ya saketa. Yace ba zai saketa ba. A haka Zatana bin Maza ko wani Abu na daban.

Idan kuma Budurwa ce Zaka Aura. Wannan ba ka da wata damuwa. Yadda ka Sabar mata. Haka zaka sameta.

Allah Shine Masani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments