Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Amfani Da Maganin Bindiga Ko Ƙarfe

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Ina daga cikin jami’an tsaro da ake turawa su kamo ’yan ta’adda, shi ne nike tambaya: Ko ya halatta in nemi maganin bindiga da maganin ƙarfe saboda kariya daga farmakin yan taadda?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Idan abin nufi da maganin bindiga da ƙarfe shi ne: Abin da ake amfani da shi na waɗansu rataye-ratayen layu ko guraye, ko yin wanka ko shafawa ko kuma shan waɗansu magungunan da ake samowa daga wurin matsafa da bokaye da malaman tsibbu, wannan kam haram ne, bai halatta ba. Saboda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

مَنْ أَتَى عَرَّافًا أَوْ كَاهِنًا ، فَصَدَّقَهُ بِمَا يَقُولُ ، فَقَدْ كَفَرَ بِمَا أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ

Duk wanda ya tafi wurin mai duba ko boka kuma ya gaskata shi a kan abin da yake faɗi, to haƙiƙa! Ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). (Ahmad da Al-Haakim ya riwaito shi, kuma As-Shaikh Albaaniy ya inganta shi a cikin Sahih Al-Jaami: 5939).

Sannan kuma tun da dai tarihi ya nuna cewa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da Sahabbansa masu daraja (Radiyal Laahu Anhum) sun kutsa a cikin surƙuƙin jihadi da arna da sauran kafirai a wurare kuma a cikin yanayi masu tsananin wahala kuma har da yawansu suka yi shahada, amma kuma ba a taɓa jin ko ɗaya daga cikinsu da ya yi amfani da irin waɗannan magungunan na ƙarfe, irin yadda waɗansu suke da’awar amfani da su a yau ba, wannan dalili ne a kan cewa amfani da irin waɗannan ɗin a yau ba koyarwar musulunci ba ne. Domin in da wani abin alkhairi ne to da kuwa waɗancan zamunnan na-farko waɗanda suka fi na-baya alkhairi sun riga yin amfani da shi.

Amma idan maganin ƙarfen wani abu ne da aka san amfaninsa a fili, kuma wanda kuma ba ta hanyoyin matsafa ko yan duba ko bokaye aka samo shi ba, kamar ta amfani da hular kwano ko sulke ko garkuwa da makamantan hakan, wannan kam halal ne ba laifi ba ne. Kuma wannan bai kore tawakkali ko dogaro ga Allaah Taaala ba. Musamman dayake magabatan wannan alummar tun daga kan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) shi kansa da Sahabbansa (Radiyal Laahu Anhum) duk sun yi amfani da su.

Wata hanyar da take da matuƙar muhimmanci a nan ita ce: Jamian Tsaro su yawaita yin adduoin neman Allaah Taaala ya tsare su, ya ba su kariya daga sharrin maƙiyansu. Kuma su yawaita adduar neman taimakon Allaah Mabuwayi Mai Girma a kan samun cin nasara a kan maƙiya. Haka kuma da yawaita ayyukan biyayya da ɗa’a ga Allaah Ta’aala da nisantan dukkan ayyukan saɓo da zunubi. Waɗannan ma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da magabatan wannan al’ummar duk sun yi amfani da ita a lokutan yaƙe-yaƙensu da kafirai da yan fashi da yan tawaye da sauransu.

Don haka, ya zama wajibi ga dukkan musulmin da yake neman tsira a cikin addininsa - musamman waɗanda suke aiki a fagen fama, waɗanda kuma aka fi tsammanin aukuwar mutuwa gare su a kowane lokaci - ya zama dole su yi nesa da duk wani abin da zai iya rusa musu addininsu, tun daga ƙanana har zuwa ga manyan zunubai da saɓon Allaah, da gwargwadon iko da ƙarfin iyawarsu.

Muna roƙon Allaah Mai Girma Ɗaukaka ya ba jamian tsaronmu nasara a kan aikin da suke yi na ƙoƙarin kawar da taaddanci a yankunanmu da ƙasarmu da sauran ƙasashen musulmi gaba-ɗaya. Allaah ya ba mu zaman lafiyar da za mu iya cigaba da yi masa bauta a cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Allaah ya taimake mu gaba-ɗaya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Tambayad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments