Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Zai Kara Aure, Shin Ya Halatta Inyi Addu'a Allah Ya Dakatar Da Auren?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum, mlm ya aiki, Allah ya qara basira, malam dan Allah mijina ne zai qara aure kuma wlh malam bawai dan muna cikin walwala ba, gidan haya ma muke, ga lalurar gida kuma yanzu ma wata hayar ce zai kama, ga ni da yara biyu na iskoshi da yara uku ya rabu da mamamnsu, shin malam ya halatta inyi addu'a Allah ya dakatar da auren nan har zuwa wani lokaci kuma dan Allah wace addu'a zanyi Allah ya kawomin dangana ga rayuwa. nagode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullah Wabarkatuhu

Toh irin wannan yana daga cikin matsalarda take damun wasu daga cikin mazaje, sekaga mutum befi karfin matsalar gidanshi ba shida 'Yar matarshi guda ɗaya amma kuma sekaji yace ze kara aure, kuma dayawa inka bincikama zaka samu bashi sukeci suna kara auren. Dayawan mutane kara aure a haqqinsu haramunne amma saboda jahilci da karancin tunani sekuma kaga sunkara dan kawai sunaso su tonama kansu asiri.

shawarar da zan baki anan ita ce kiyi hakuri kada ki tada hankalinki ko hankalin mijinki akan haka. Kowanne abu da kika gani yana da dalili kuma ba'a rasa wata hikima da Ubangiji ya ajiye aciki. To haka shima wannan abin da mijinki yake niyyar yi, watakila ta dalilin wacce za'a auro ɗin kema ki samu chanjin al'amari a yanayin zaman gidan.

Amatsayinki na Musulma, yana daga cikin ginshikan imani cewa ki rika yarda da duk Qaddarar da Allah ya nufa gareki. Kada ki rika neman mafita ta hanyar zuwa wajen 'yan duba da bokaye. Domin Annabinmu (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "DUK WANDA YAJE WAJEN BOKA KO ƊAN DUBA KUMA YA GASKATASHI CIKIN ABIN DA YAKE FAƊA, TO HAKIKA YA KAFIRCE WA ABIN DA ANNABI MUHAMMADU YAZO DASHI" (Sallallahu Alaihi Wasallam)

kiyi hakuri, kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah". Kiyi yawaita Addu'a Allah Ya sa idan ta zo ku Zauna Lafiya Kuma Ku Haɗe kanku.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments