Ticker

6/recent/ticker-posts

Haƙƙin Ciyar Da Bazawara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salamu Alaikum. Malam, matar da mijinta ya sake ta kuma ta dawo gidan iyayenta, wai haƙƙin ciyar da ita a kan wanene ya ke? Domin wasu iyaye sai ka ji suna cewa, yanzu ciyar da ita ba shi ne a gabansu ba! Suna ganin ƙannenta sun fi ta daraja a wurinsu. Wai ita bazawara ba ta da daraja ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

To, da farko dai ma’anar ciyarwa shi ne abin da malaman Fiqhu suke kira: An-Nafaqah , watau abin da mutum yake bayarwa domin amfanin kansa ko waninsa, na abinci ko abin sha ko tufafi ko sauran abubuwan buƙata, kamar wurin zama da magunguna a lokacin rashin lafiya.

Ciyarwa wajibin abu ne da Allaah ya ɗora ta a kan muminai a cikin ayoyi da hadisai ingantattu.

يٰۤـاَيُّهَا الَّذِيْنَ اٰمَنُوْۤا اَنْفِقُوْا مِمَّا رَزَقْنٰكُمْ مِّنْ قَبْلِ اَنْ يَّأْتِىَ يَوْمٌ لَّا بَيْعٌ فِيْهِ وَلَا خُلَّةٌ وَّلَا شَفَاعَةٌۗوَالْكٰفِرُوْنَ هُمُ الظّٰلِمُوْنَ

Ya ku waɗanda suka yi Imani! Ku ciyar daga abin da Allaah ya azurta ku da shi, tun kafin wani yini ya zo muku, wanda babu ciniki a cikinsa, babu abota kuma babu ceto. Kuma kafirai sune azzalumai. (Surah Al-Baqarah: 254)

Shari’ar musulunci ta ɗora wa musulmi nauyin ciyar da matan aurensu da ’ya’yansu da iyayensu da danginsu mabuƙata da barorinsu masu yi musu hidima, da kuma dabbobin da suke ƙarƙashin ikonsu da kulawarsu. (Al-Wajeez, shafi: 394-400)

Haƙƙin ciyar da mace a bayan aure yana kan mijinta ne. Allaah Taaala ya ce

لِيُنْفِقْ ذُوْ سَعَةٍ مِّنْ سَعَتِهٖۗ وَمَنْ قُدِرَ عَلَيْهِ رِزْقُهٗ فَلْيُنْفِقْ مِمَّاۤ اٰتٰٮهُ اللّٰهُۗ لَا يُكَلِّفُ اللّٰهُ نَفْسًا اِلَّا مَاۤ اٰتٰٮهَاۗسَيَجْعَلُ اللّٰهُ بَعْدَ عُسْرٍ يُّسْرًا

Sai mawadãci ya ciyar daga wadãtarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bã shi. Allah bã Ya kallafa wa wani rai fãce abin da Ya bã shi. Allah zai sanya sauƙi a bãyan tsanani. (Surah At-Talaaq: 7)

Kuma da aka tambayi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a kan haƙƙin matar ɗayanmu a kansa, sai ya ce: ‘Shi ne ka ci da ita idan ka ci, kuma tufatas da ita idan ka tufatu, kuma kar ka bugi fuska, kuma kar ka munana, kuma kar ka ƙaurace sai dai a cikin ɗaki.’ (Abu-Daawud; Ibn Maajah)

Wannan haƙƙin yana nan a kan mijin har a bayan ya saki matar har zuwa lokacin gama iddarta, matuƙar dai sakin rajai ne wanda akwai kome a cikinsa. Allaah Taaala ya ce

وَالْوَالِدٰتُ يُرْضِعْنَ اَوْلَادَهُنَّ حَوْلَيْنِ كَامِلَيْنِ لِمَنْ اَرَادَ اَنْ يُّتِمَّ الرَّضَاعَةَۗوَعَلَى الْمَوْلُوْدِ لَهٗ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوْفِۗ لَا تُكَلَّفُ نَفْسٌ اِلَّا وُسْعَهَاۚلَا تُضَاۤرَّ وَالِدَةٌ بِۢوَلَدِهَا وَلَا مَوْلُوْدٌ لَّهٗ بِوَلَدِهٖ وَعَلَى الْوَارِثِ مِثْلُ ذٰلِكَۚ فَاِنْ اَرَادَا فِصَالًا عَنْ تَرَاضٍ مِّنْهُمَا وَتَشَاوُرٍ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَاۗوَاِنْ اَرَدْتُّمْ اَنْ تَسْتَرْضِعُوْۤا اَوْلَادَكُمْ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ اِذَا سَلَّمْتُمْ مَّاۤ اٰتَيْتُمْ بِالْمَعْرُوْفِۗ وَاتَّقُوا اللّٰهَ وَاعْلَمُوْۤا اَنَّ اللّٰهَ بِمَا تَعْمَلُوْنَ بَصِيْرٌ

Kuma mãsu haifuwa (sakakku) suna shãyar da abin haifuwarsu shkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne. (Surah: Al-Baqara, Ayat: 233)

Amma idan sakin baa’in ne wanda babu kome a cikinsa, kamar wanda ya auku a matsayin na cikon uku ko ta hanyar khul’i ko Li’aani , to a nan babu sauran ciyarwa a kan mijin. Haka Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa wa Faatimah Bint Qais (Radiyal Laahu Anhaa) a lokacin da mijinta ya sake ta na ƙarshen uku: Ba ki da wani abu na ciyarwa ko mazauni a kansa. (Muslim)

Sai dai ko in ya sake ta alhali tana da ciki ne. A nan wajibi ne ya cigaba da ciyar da ita har sai ta haihu. Allaah Ta’aala ya ce:

اَسْكِنُوْهُنَّ مِنْ حَيْثُ سَكَنْـتُمْ مِّنْ وُّجْدِكُمْ وَلَا تُضَاۤرُّوْهُنَّ لِتُضَيِّقُوْا عَلَيْهِنَّۗ وَاِنْ كُنَّ اُولَاتِ حَمْلٍ فَاَنْفِقُوا عَلَيْهِنَّ حَتّٰى يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّۚ فَاِنْ اَرْضَعْنَ لَـكُمْ فَاٰ تُوْهُنَّ اُجُوْرَهُنَّۚ وَأْتَمِرُوْا بَيْنَكُمْ بِمَعْرُوْفٍۚ وَاِنْ تَعَاسَرْتُمْ فَسَتُرْضِعُ لَهٗۤ اُخْرٰىۗ

Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar daga gwargwadon sãmunku. Kuma kada ku cũce su dõmin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abũta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shãyar da mãma sabõda ku, sai ku bã su tsãdõdinsu. Kuma ku yi shãwara a tsakãninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nũna talauci to wata mace zã ta shãyar da mãma sabõda shi (mijin). (Surah: At-Talaaq, Ayat: 6)

Idan kuma ba ta yarda ba shikenan, sai ya nemi wata ta shayar masa.

Matar da aka ce babu haƙƙin ciyarwa ko mazauni a kan mijinta a bayan saki, ko wacce ta gama idda, ko ta haife cikinta, ya zama dole ta rabu da gidan mijin domin babu wata alaƙa da ta rage a tsakaninsu. Sai ta koma gidan iyayenta ko danginta.

Daga wannan lokacin, haƙƙin ciyarwa, tufataswa da mazauni ya tashi daga kan mijinta ya dawo kan iyayenta ko danginta. Nassoshi da yawa sun kwaɗaitar da iyaye ga ciyarwa a kan ’ya’yansu, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: ‘Mafificin dinaren da mutum ya kashe shi ne dinaren da ya kashe shi a kan iyalinsa.’ (Muslim).

Haka kuma ya tsawatar a kan yin rowa da ƙin ɗaukar nauyin iyali: ‘Ya ishi zunubi ga mutum ya tozarta wanda yake ciyarwa.’ (Abu-Daawud)

A kan haka ne ma wasu nassoshin suka halatta wa mace ta ɗebi daidai gwargwadon abin da ya ke haƙƙinta da yayanta daga cikin dukiyar mijinta da ya zama ƙanƙamo, ko da kuwa ba da saninsa ba ne. (Al-Bukhaariy da Muslim)

Sai dai kar a manta fa: Duk maganar da ake yi a kan ciyar da ’ya’ya maza da mata da sauran dangi, yana zama wajibi ne kawai a lokacin da ’ya’yan suka zama talakawa kuma marasa ƙarfi, waɗanda ba za su iya nema da kansu ba. Amma shari’a ba ta ɗora wa wani mutum ciyar da ’ya’ya ko danginsa ƙarfafa da suka ƙi neman na-kansu, suka shantake suka zama cima-zaune ba! Musamman a lokacin da ake cikin halin ƙaƙa-ni-ka-ki irin wannan. (Tamaam Minnah)

Don haka, shawarar da ya dace a bai wa irin waɗannan zawarawan a nan ita ce:

1. Ku yi haƙurin zama a cikin gidajen mazajen aurenku, irin yadda uwayenku suka yi kuma suke yi a gidajen mazajensu, watau ubanninku da suka haife ku.

2. Kar ku riƙa neman fita ko rabuwa da su. Domin mijin aure da gidan aure daraja ce, kuma rufin asiri ne ga mace.

3. Tun kafin aure da bayan aure ku yi ƙoƙarin samun sanaa ta halal da za ku dogara da ita a cikin rayuwa. Kar ku dogara ga abin hannun wani: Iyaye ko miji ko ɗan’uwa ko dangi.

4. Ku yi amfani da sadakin aurenku wurin ƙara jali a cikin sanaoinku, kar ku yi gaggawan cinye shi a kayan tanɗe-tanɗe da lashe-lashe ko maƙulashe!

5. Kar ku sake harkokin sana’o’in su shagaltar da ku daga kula da ayyukanku na asali a cikin gida, kamar haƙƙokin miji da tarbiyyar yayanku.

Ina kyautata zaton cewa rashin hali da ƙuncin rayuwar da iyaye suke ciki ne ke sanyawa ake gaya muku irin waɗannan maganganun da ba ku jin daɗin su. Don haka, ku yi haƙuri kuma ku yi ƙoƙarin neman na-halal ɗin ku, kuma ku taimaka musu. Da haka, sai ku ga komai ya wuce, in shà Allâh.

Amma kuma su ma iyaye dole su san cewa: Takurawa ’ya’ya zawarawa da sauran ’ya’ya maza da mata, da gaya musu baƙaƙen maganganu irin wannan kan iya kangarar da su. Wani lokaci kuma ya sanya su kauce hanya, su fice daga gida da himmar neman nasu na-kansu ta mummunar hanyar da ba ta dace ba!! Sai kuma a zo ana tafa hannu, ana sallallami!

Sai mu kiyaye.

Allaah Ta’aala ya shirye mu gaba-ɗaya.

 WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments