Wadda za ta buge ta danne,
Wadda za ta rufe ta binne,
Wadda ba ta ido da kunne,
Ba ta tausai in ka gan ta,
Babu sauyi in ka ji ta,
Babu alƙawari gidanta,
Ba aminci sam gurinta.
Ba ni son na ji ambatonta,
Tunda kuka ke biyo ta,
Lahaula ake gabanta,
Ba’a murna ran kiran ta.
Tunda ta ɗauke na Allah,
Ta kaɗe mai ta da Sallah,
Ba ta ƙyalewa jumulla,
Babu ɗangata gareta.
Tunda ta ɗau ɗan Amina,
Ba ta ƙyale guda sanina,
Ko saraki da malumana,
Ba guda ɗaya mai guje ta.
Ga shi ta karyan lagona,
Ta yi wuf ta ɗau gwanina,
Mai halin a yaba da ƙauna,
Abadan na bar musun ta.
Baba Yakubu yau ta amsa,
Mun sani shi bai da wasa,
Mai halin kirki adonsa,
Mai yawan fara’a zumunta.
Mun yi kuka kan rashi nai,
Har Prof. Adnan da kai nai,
Duk aminai sun hawai nai,
Sun yi rauni yau zukata.
Rabbi kai jinƙai sifarka,
Rabbi kai masa gafararka,
Don biyarsa ga annabinka,
Sa a can su zamo maƙota.
Rabbi sa shi cikin na gaske,
Rabbi sa a gidansa haske,
Rabbi duk zunubinsa wanke,
Rabbi sa shi ya zam rabauta.
Tunda ya so mai Madina,
Rabbi Sarki sa shi Janna,
Rabbi Sarki ba shi manna,
Ba shi don kai ke da kyauta.
Rabbi mai baiwa da karɓa,
Kai ka bayar, kai ka karɓa,
Ka yi mun yi biya da karɓa,
Ba mu yin furuci na wauta.
©
Murtala Uba Mohammed
13/11/2023
6:58nd
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.