1.
Na gode Sarki Allah
Mai Arziki da Jalala
Shi ɗai ya ke da Kamala
2.
Na gai da Manzon nasa
Mahmudu baƙon Aƙsa
Angon Khadija da Hafsa
Baban su Fatima Binta.
3.
Ga 'yar ƙasida na yi
Manya da su nai koyi
Domin nishaɗi nai yi
Dangi ku zo ku karanta.
4.
Na jera baiti-baiti
Tamkar gini da siminti
Kuma na aje su a saiti
Su goma 'yan matsakaita.
5.
Hammadu yaron Umma
Gaishe ka sannu da himma
Ga ɗan da ya wuce goma
Gun hankali da nagarta.
6.
Hammadu yaron Abba
Wai kai da shi kas saba
Muddin idan ka duba
Ka gan shi, rai ya faranta.
7.
Kai duniya mai sauri
Jiya nan ka ke jariri
Amma kamar ɗan shuri
Ka girma sai makaranta.
8.
Hammadu na gaisheka
Na tabbatar ba shakka
In dai ka jure shuka
Girbinka za ya yawaita.
9.
Gaishe ka yaron kirki
Na san fa ba ka raki
Sannunka sannu da aiki
Hammadu ɗan makaranta.
10.
Roƙo ga Al-Mannanu
Allahu Ar-Rahmanu
Ya sa ma ɗan nan hannu
Don rayuwa ta rabauta.
Mustafa Adamu
18.11.2023
0 Comments
Post your comment or ask a question.