Ticker

6/recent/ticker-posts

In Ki Samu Miji Ki Yi Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya ce wa matarsa: ‘In kin samu miji ki yi aure!’ ta saku? Kuma sun yi wata shida yanzu ba su a tare da juna, ko za ta iya yin auren?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Malamai sun kasa Lafazin Saki gida biyu ne: Akwai Saki Sarihi wanda ba a iya fahimtar komai daga cikinsa sai dai sakin kawai, kamar idan mijin ya ce wa matarsa: Na sake ki!

Akwai kuma Saki na Kinaya, wanda ke iya ɗaukar ma’anar saki, kuma a lokaci guda ya ɗauki wata ma’anar da ba sakin ba. Kamar miji ya ce wa matarsa: Tafi gidanku!

Ma’anarsa za ta iya zama saki ne yake nufi, ko kuma ya zama manufarsa: Tafi gidanku sai al’amura sun gyaru. Ko: Tafi gidanku kafin in dawo daga tafiya. Ko kuma: Tafi gidanku a koya miki abinci ko ladabi da biyayya. Da sauransu.

Kamar haka, wannan kalmar: In kin samu miji ki yi aure, a fahimtata ta fi kama da nau’in saki na kinaya. Domin ma’anarta kan iya kasancewa: ‘In kin samu miji ki yi aure, in gani!’ Domin ƙarancin maza masu son yin auren da ake da su! Ko kuma: In kin samu miji ki yi aure, in kin isa! Watau saboda tsananin soyayyar da ya san tana yi masa!

Don haka, kafin a yanke hukunci a kan irin wannan sakin na kinaya sai dole an ji daga bakin mijin: Shin sakin yake nufi, ko kuwa wani abin daban yake nufi?!

Matar da aka ɗaura mata sahihin aure ba za ta sake yin aure da wani mijin ba sai a bayan aurenta na farko ya mutu: Ko dai ta hanyar mutuwan mijin ko mutuwar auren. Kuma ko a bayan mutuwar auren ba za ta iya sake yin wani auren ba, sai a bayan ta gama idda. Ita kuma Idda tana bambanta da gwargwadon  matsayin macen da aurenta ya mutu

1. Idan ya kasance saboda mutuwar mijinta ne, to iddarta watanni huɗu ne da kwanaki goma.

2. Idan kuma saboda saki ne, to iddarta tsawon haila uku ne, idan matar tana daga cikin waɗanda suke cikin shekarun yin hailar ce.

3. Idan kuwa ba ta daga cikin masu yin hailar saboda tsufa ko yaranta, to tsawon iddarta watanni uku ne.

4. Idan kuwa matar mai ciki ce a lokacin da aka sake ta, to iddarta shi ne ta haife cikinta.

Don haka, waɗannan matar ba za ta iya yin aure ba, har sai an tabbatar da cewa mijin sakinta ya yi. Sannan kuma ko a bayan hakan sai kuma bayan ta gama yin idda.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments