Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Kanin Kaka

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. 'Yan uwa biyu ne maza kuma ’yan-uba, sai ’yar da babbansu ya haifa tayi aure kuma ta haifi yarinya, shi ne wai wannan yarinyar take son auren kanin kakanta. Tambaya a nan ita ce: Wai auren ya halatta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah

A kan bayanin matan da suka haramta ta hanyar dangantaka ga abin da Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala ya ce

{ حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ }

An haramta muku auren uwayenku, da ’ya’yanku mata, da ’yan uwanku mata, da goggoninku, da innoninku da ’ya’ya mata na ’yan uwanku maza, da ’ya’ya mata na ’yan uwanku mata. (Surah An-Nisaa’: 23).

Abin nufi da ’ya’yanku mata, in ji malamai: Duk macen da namiji yake matsayin mahaifi gare ta, kamar ’ya ko ’yar ’ya, ko ’yarta duk kuwa yadda suka yi ƙasa. Kuma wannan yar ko ta aure ne aka same ta, ko ba ta aure ba ne.

Ƙanin kakanta shi ne ƙanin mahaifin mahaifiyarta. Wannan bai halatta ba lura da wannan ayar.

Sannan kuma ƙaidar da malaman Fiqhu suka shimfiɗa ma a nan ita ce

Haram ne namiji ya auri duk wata macen da yake da dangantaka na jini da ita, sai dai guda huɗu kawai

1. ’Yar baffansa.

2. ’Yar kawunsa.

3. ’Yar goggonsa.

4. ’Yar innarsa.

(Sahih Fiqhis Sunnah: 3/72).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments