Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mayar Da Kai ‘Dada’:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ko ya halatta mayar da kan ta irin na ‘dada’?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Kodayake asali a musulunci, babin kwalliya da ado yana sashen halacci ne, wanda mutum yana iya yin duk abin da ya so har sai an samu wani dalilin da ya hana aikata hakan a shari’a. To sai dai kuma malamai sun tattauna a kan mas’aloli guda biyu

1. Zaƙewa da zuce iyaka ko ƙaida a wurin kwalliya, mai kai wa ga sauya halittar Allaah.

2. 4886, Sahih Sai kuma koyi da wanda ba musulmi ba a cikin kaya da nau’ukan kwalliyarsu.

Duk waɗannan kuwa abubuwan hanawa ne a shari’a. Abdullaah Bn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) ya samo hadisi daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

لَعَنَ اللَّهُ الْوَاشِمَاتِ وَالْمُسْتَوْشِمَاتِ وَالنَّامِصَاتِ وَالْمُتَنَمِّصَاتِ وَالْمُتَفَلِّجَاتِ لِلْحُسْنِ الْمُغَيِّرَاتِ خَلْقَ اللَّهِ

Allaah ya la’anci mata masu yin zane a fatar jiki da masu neman a yi musu zanen, da mata masu aske gashin gira da masu neman a aske musu gashin, da mata masu yin feƙe haƙora don yin wushirya, masu sauya halittar Allaah. (Sahih Al-Bukhaariy: 4886, Sahih Muslim: 5695).

Don haka duk kwalliyar da ta kai ga sauya halittar Allaah an haramta ta, kuma tana da la’anar Allaah a kan ta. A fili yake kuwa cewa mayar da gashin kai irin wannan sauya halittar Allaah ne.

Allaah ya shiryar da mu.

A kan mas’ala ta-biyu kuwa, watau: koyi da waɗanda ba musulmi ba, akwai hadisi sahihi daga Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya riwaito daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

وَمَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ

Kuma duk wanda ya kamantu da waɗansu mutane, to shi yana tare da su. (Sahih At-Targheeb: 2089).

Waɗanda ake koyi da su a kan wannan abin a yau kuwa, idan ma ba kafirai ne tantagarya ba, to kuwa fasiƙai ne masu ficewa daga ɗa’ar Allaah Ta’aala, waɗanda kuma sam! addini bai yarda a yi koyi da su ba.

Sannan kuma ana koyi da irin waɗannan mutanen ne kawai saboda dalilin ƙauna da soyayyar da ake yi ga ɗabi’unsu da hanyarsu. Wannan kuwa mummunan abu ne mai hatsari a rayuwar musulmi. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« الْمَرْءُ مَعَ مَنْ أَحَبَّ »

Mutum yana tare da wanda yake so. (Sahih Al-Bukhaariy: 6168, Sahih Muslim: 6888).

Ban kuwa san wani musulmin gaskiya da yake sha’awar a tashe shi a ranar Al-Ƙiyamah tare da wani daga cikin Kafirai ko fasiƙai ko munafukai ba!

Allaah ya shiryar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat. whatsapp. com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments