Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsayin Auren Matar Da Ta Kwashe Kayanta Ta Bar Gidan Mijinta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Malam mace ce da mijinta bayan aukuwar wata matsala a tsakaninsu sai matar ta kwashe kayanta ta bar gidan mijin, sai bayan watanni tara take son ta dawo. To wai akwai auren, ko sai an sake ɗaura Sabon Aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Da zaran an ɗaura aure da ƙaidojinsa da sharuɗɗansa to yana nan a ƙulle, babu abin da yake warware shi sai in mijin da zaɓin ransa ya warware shi ta hanyar aukar da saki. Ko kuma da umurnin alƙali kamar idan ya gano cewa mijin yana cutar da ita, ba ya sauke haƙƙoƙinta da suke a kansa.

Kuma a bayan ɗaura aure ba ya halatta mace ta kwashe kayanta haka nan kawai ta bar gidan mijin domin ɓacin rai. Sannan bai kamata su kansu iyayenta ko waliyyanta su bar ta a gabansu na tsawon lokaci haka nan ba tare da binciken mijin ba. Allaah Ta’aala ya ce

وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوا حَكَمًا مِنْ أَهْلِهِ وَحَكَمًا مِنْ أَهْلِهَا، إِنْ يُرِيدَا إِصْلَاحًا يُوَفِّقِ اللَّهُ بَيْنَهُمَا، إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا

Idan kuma kuka ji tsoron aukuwar saɓani a tsakaninsu to sai ku aika da mai hukunci a cikin danginsa da mai hukunci a cikin danginta. Idan dai suna nufin gyara ne to Allaah zai datar a tsakaninsu. Haƙiƙa Allaah ya kasance masani ne mai ba da labari. (Surah An-Nisaa: 35).

A ƙarƙashin wannan matar da ta dawo bayan watanni tara ko fiye ko ƙasa da haka tana nan a matsayin matarsa, tun da dai bai sake ta ba, kuma ba ta kai ƙara kotu don neman rabuwa da shi, kamar ta hanyar khuli ko makamantan hakan ba.

Amma a wannan zamanin da gaskiya da riƙon amana da tsoron Allaah suka yi ƙaranci a cikin mutane bai kamata su amince kawai ta shiga ta zauna haka nan ba tare da sake binciken lafiyarsu ba. Haka kuma lallai kafin ya kusance ta ya tabbatar babu komai a cikin mahaifarta, don kar a ɗauko zuriyar wani gida a haɗa da na gidan wannan mijin.

Allaah ya ƙara mana shiriya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat. whatsapp. com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments