Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Ta Haihu Bata Cika Arba'in Ba Jini Ya Ɗauke, Mijinta Ya Sadu Da Ita

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Allah ya ninka suttura malam Tambayata anan shi ne: Ya matsayi matar da ta haihu batai arba'in ba mijin ta ya sadu da ita Amma jini ya ɗauke shin hakan kuskure ne , Sai dole tayi arba'in zai kusanceta ? Allah ya saka da alkairi ameen wassalam

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, malamai sun bayyana cewa; shi jinin haihuwa ba shi da qarancin kwanaki, matuqar ya ɗauke wa mai haihuwa ko da kafin ya cika kwana 40 ne, to za ta yi wankan tsarki ta ci gaba da yin ibada, sannan kuma mijinta zai iya saduwa da ita. In ma ya qara dawo mata ne, to sai ta dakata da ibada, da zarar ya cika kwana arba'in (40) ko da bai dakata da zuwa ba, to shi kenan sai ta yi wankan tsarki ta ci gaba da yin ibada, kuma mijinta zai iya saduwa da ita. Kwana arba'in shi ne iya tsawon kwanakin jinin haihuwa (nifasi), da zarar ya cika kwana 40 bai ɗauke ba, to shi kenan ya zama gurɓataccen jini, babu laifi idan mijinta ya zo mata tana wannan jini, tun da ta cika kwanaki arba'in. Wato dai cikin kwanaki arba'in ɗin nan ne ba a yarda miji ya zo wa matarsa ba.

Al-Imaam Abu-Daawud da Al-Imaam At-Tirmiziy da Al-Imaam Ibn Maajah duk sun riwaito hadisin da Al-Imaam Al-Muhaddith Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Al-Irwaa’u (lamba: 201), daga Sahabiya Ummul-Mu’mineen Ummu-Salamah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa

A zamanin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ita mai jinin haihuwa tana zama a cikin jininta har zuwa kwanaki arba’in ne. Kuma ba ya umurtan ta da rama sallolin da ba ta yi su a halin tana jinin haihuwar ba.

Al-Imaam Abu-Isaa At-Tirmiziy a ƙarshen riwayarsa ga wannan hadisin ya ce

Malamai ma’abuta ilimi daga cikin Sahabban Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu duk sun haɗu a kan cewa: Ita mai jinin haihuwa tana barin yin sallah na tsawon kwanaki arba’in ne, sai dai ko in ta ga tsarki kafin hakan. Daga nan sai ta yi wanka ta cigaba da sallah. Idan kuma ta ga jinin a bayan kwanaki arba’in ɗin ne, to mafi-yawan malamai masana ilimi sun ce, ba za ta bar yin sallah a bayan kwana arba’in ba. Wannan kuma shi ne maganar mafi-yawa daga cikin malaman Fiqhu, shi ne maganar Sufyaan At-Thawriy, da Ibn Al-Mubaarak, da As-Shaafi’iy, da Ahmad, da Is’haaq.’

Shaikhul Islaam Ibn Taimiyah (Rahimahul Laah) ya ce

Jinin haihuwa ba shi da iyaka ta fuskar ƙaranci ko ta fuskar yawa. Don haka, idan aka ƙaddara cewa wata mace ta ga zuban jinin fiye da kawanaki arbain ko sittin ko sabain kuma a yanyanke, to dai jinin haihuwa ne. Amma idan a haɗe da juna ne, to shi jinin istihaalah ne, kuma a lokacin sai a ce: Bakin iyakan kwanakinsa arba’in ne, domin shi ne iyakan kwanakin yawancin mata, kamar yadda hadisi ya nuna.’ (Tamaamul Minnah: 1/144).

Ibn Qudaamah Al-Maqdisiy a cikin littafinsa Al-Mughnee: 1/392 ya ce

Idan jinin haihuwa ya zarce kwanaki arba’in sai kuma ya dace da lokacin al’ada, to shi haila ne. Idan kuwa bai dace ba, to shi Istihaalah ne.’

Game da matar da ta tsarkaka daga jinin haihuwa kafin kwana arba’in, daga baya kuma sai jinin ya dawo mata kafin cikan kwanaki arba’in ɗin, shi ne Al-Allaamah Ibn Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah) a cikin As-Sharh Al-Mumti’: 1/450 ya ce: ‘Sai ta lura da alamomin jinin: Idan ta ga siffofin jinin haihuwa a tare da shi, to jinin haihuwa ne. Idan kuwa alamun ba su nuna shi jinin haihuwa ba ne, to ita mai tsarki ce.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments