Ticker

6/recent/ticker-posts

Banbancin Kyauta Da Sadaqa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu'alaikum mlm mene ne babancin kyauta da sadaka?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa,alaikumus-salam-warahamatullahi-wabarkatuhu.

Kyauta da Sadaka suna da kusanci da juna matuƙa don sun yi kama, sau da yawa abinda yake bambanta su ita ce niyya.

KYAUTA: Anayintane ga wanda yafi qarfin abu, misali kasamu me kuɗi kabashi turare, wannan shi ake kira kyauta, wato kabashi, batare da ya roqa ba, kamar ne dan ka girmama shi.

SADAQA: Ana bawa mabuqacine, wato wanda yake talaka ko marar abu, seya roqa acemar sadaka, shiyasa Annabi sallallahu alaihi wa sallam baya ci, hakama iyalansa, haramun ne suci sadaqa !

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya tabbatar cewa kar a bai wa iyalan gidan Muhammad sadaka. Muslim ya riwaito.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana karɓar kyauta, amma ba ya karɓar sadaka. Bukhari 3.751.

Sannan baya halatta abawa me qarfi sadaka, haka me kuɗi ko wadata.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya bayar da wata sadaka (ko kyauta) daidai da dabino ɗaya na halal – domin Allah ba Ya karɓar komai, sai mai tsarki (halal) – Allah Zai karɓa da hannunSa na dama, kuma Ya kiwata (Ya tattale) shi, kamar yadda dayanku yake kiwon maraki har ya zama bajimi – to Allah zai tattale shi har ya zama kamar girman tsauni a Ranar Lahira.”  Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.

Lallai sadaka da kyauta basa kawowa mai dukiya komi cikin dukiyarsa sai karin albarka, da yawaita...!

Hadisai da dama ana kwadaitar da mara shi ya bayar da komai kankantar abin da ya samu don Allah, gwargwadon karfi da iyawarsa. Shi bayar da ɗan kaɗan saboda Allah, idan mutum ya gan shi a Ranar Lahira zai yi ta mamakin yadda ya kai haka don girma, saboda Allah Yana kiwata masa shi ne a wajenSa, matukar dai abin da ya bayar ɗin ya same shi ne ta hanyar halal.

Allah Ya bamu ikon bayar da kyauta da sadaka.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments