✍️✍️✍️ Imrana Hamza Tsugugi
A kwanan baya na yi wani posting
mai kama da wannan, amma mutane da dama sun nemi ƙarin haske a kan shi. Wannan
dalilin ne ya sa zan yi sharhi a kan wannan batu.
Ga bayani kamar haka:
AURE KIKE SO KA KARATU ZA KI YI???
1. SHIMFIƊA
Wannan ita ce tambaya da wasu
iyaye sukan yi wa 'ya'yansu mata, musamman waɗanda suka kammala karatun
sakandare. Sukan yi Wannan tambayar ne domin su riƙa kafawa yaran hujja a duk
lokacin da suka kawo musu maganar aure. Ni dai ban san hikimar wannan tambayar
ba, kuma ban san dalilin ta ba. Haka kuma wannan tambaya ce mai matuƙar wahalar
amsawa. Ba kowace 'ya mace ce za ta iya kallon ubanta ta ce masa aure take so,
ko da kuwa tana da wanda ya shirya ya aure ta. Idan ta ce tana son aure, sai a
ce mata ba ta da kunya. Idan kuma ta kasa bayyana ra'ayinta, za ta ci gaba da
cutuwa. Amma dai bayanan da za su biyo baya za su ƙara mana haske.
2. MACE BALAGAGGIYA
Duk wata 'ya mace da siffofin
matantaka suka bayyana a jikinta, babu yadda za a yi a ce ba ta jin sha'awa ta
ɗa namiji, domin wannan shi ne tsarin Allah. Sai dai wata tana da ƙarancin
sha'awar, yayin da wata kuma tana da sha'awa mai yawa, ta yadda ba ta iya
ɓoyuwa. Irin wannan rukunin na biyu akan same su da yawan son magana da namiji
ko zama da shi ko ma ƙoƙarin kusantar shi. Domin haka, irin wannan rukunin suna
buƙatar kulawa ta musamman daga wurin iyaye. A taƙaice dai, duk wata mace
balagaggiya tana da sha'awa.
3. ME YA SA IYAYE SUKE YI WA 'YA'YANSU WANNAN TAMBAYAR?
Iyayen da suke yi wa 'ya'yansu
mata wannan tambayar suna yi ne saboda manufar da suke da ita na son 'ya'yan
nasu su yi karatun BOKO mai zurfi, su kammala, su sami aiki, su riƙa ɗaukar
albashi domin su taimaki kansu da 'ya'yansu da kuma iyayensu. Har wasu ma sukan
ce wa yaran "kar ki dogara da miji, zai iya sakin ki, ko ya yi miki
wulaƙanci, idan ba ki da aiki, sai ki tagayyara".
Wasu iyayen kuwa, suna so ne
'yaran su yi wani karatu da al'umma take da buƙatar shi kamar Likitanci ko
Jinya da makamantansu, saboda 'yaran su sami damar taimakawa al'umma.
Tabbas waɗannan manufofi me
masu kyau, kuma abin a kwaɗaitar da 'ya'ya mata da su tashi su yi.
Amma abin tambaya a nan shi ne,
MACE BA ZA TA IYA YIN KARATUN A GIDAN MIJINTA BA?
Sanin kowa ne cewa, akwai mazan
da sukan nemi auren mace, su ƙulla yarjejeniya da ita da iyayenta a kan cewa
zai bar ta ta yi karatu ko aiki, amma idan ya samu ta shigo gidansa sai ya yi
biris da wannan yarjejeniya. Wasu suna da dalilai karɓaɓɓu da sukan sa su saɓa
alƙawarin, wasu kuma tsabar rashin cika alƙawari ne. Irin waɗannan abin da ya
kamata shi ne a ɗauki matakin doka a kan su.
4. SHIN AURE YANA HANA KARATU
Maganar gaskiya wannan tambaya
ce da amsar ta tana da alaƙa ne da halin da ma'aurata suka tsinci kan su. Akwai
waɗanda aure yake hana su karatu, akwai kuma waɗanda auren ne yake sa su yi
karatu. Aure yana haifar da cikakkiyar natsuwa wajen karatu, yana samar da
kariya ga mutunci musamman na 'ya mace, yana kawar da hange-hange da
tunane-tunane na sha'awa.
Akwai malamai da dama na addini
da na boko da suka sami damar zurfafa karatunsu bayan sun yi aure. Na san wata
mace Farfesa wadda takan bayar da labarin cewa an yi mata aure ne lokacin da ta
kammala karatun Firamare. Amma a haka ta ci gaba da karatu har ta kai matsayin
Farfesa. Abin nufi dai a nan shi ne, aure ba ya hana karatu, kamar yadda karatu
ba ya hana aure. Akwai misalai marasa adadi a kan wannan.
5. SHIN DOLE NE KOWACE MACE SAI TA YI KARATUN BOKO
Ya kamata iyaye su sani cewa, ba
lallai ba ne kowace 'ya mace sai ta yi karatun BOKO mai zurfi. Asali Allah ya
halicci mace ne domin ta zama mai bayar da tarbiyya, wadda za ta haifi waɗanda
za su yi aiki, ba wai ita ya fita ta yi aiki ba. Mace ce za ta haifi shugaban
ƙasa da Gwamna da sauran Ma'aikata, ba wai ita ta fito ta yi wannan gwagwarmaya
ba. Don haka, abin da ya kamata shi ne, iyaye su lura da yanayin 'ya'yansu ta
fuskar sha'awa ko son karatu. Wadda aka lura ta fi son karatu a ƙarfafe ta da
haka, wadda kuma ta nuna aure take so, a ji tsoron Allah a yi mata auren ta.
Maganar karatu kuma su ƙarata da mijinta.
6. WACE IRIN ILLA KARATUN BOKO YAKE YI WA MATA MARASA AURE?
Haƙiƙa 'yan mata suna tsintar kan
su a cikin mawuyacin yanayi na sha'awa a tsawon lokacin da suke ɗauka na yin
karatu ba tare da aure ba. Wasu sukan sami zamiya su faɗa tarkon sheɗan
sakamakon tilasta musu da iyaye suke yi na cewa sai sun yi karatun BOKO kafin a
yi musu aure. Wasu 'ya'yan ana kai su karatu nesa da iyayensu, ta yadda sukan
sami damar sheƙe ayar su yadda suke so. Wasu kuma sukan rage wa kan su
sha'awar ne ta wasu hanyoyi na daban. Allah ya kyauta!
7. ME YA KAMATA IYAYE SU YI
Ya kamata iyaye su sani cewa,
Allah ya ba su amanar 'ya'yansu ne, kuma ya umarce su da su kare su daga shiga
wuta. Haka kuma, iyaye su sani cewa, Allah ya halicce mu ne domin mu bauta
masa, ba wai domin mu zo mu nemi kuɗi a duniya ba. Aure yana daga cikin manyan
ayyukan bautar Allah. Ashe kenan bai kamata mu fifita son duniya a kan neman
lahira ba. Don haka, ya kamata iyaye su ji tsoron Allah su sauke haƙƙin
da Allah ya ɗora musu. Idan Allah ya kawo wa 'yarka miji nagari, kada ka bari
ya kuɓuce, a lallaɓa a yi musu aure, idan kana da hali ka ɗauki nauyin karatun
ta, shi kuma mijin ya ji tsoron Allah ya bar ta ta yi karatu matukar za ta kame
kanta. Iyaye da dama suna cutar da 'ya'yansu ta hanyar hana su yin aure ko da
kuwa sun sami mai neman su da gaske, da hujjar wai sai ta kammala karatu. Kuma
wani abin haushi, duk wadda aka ce sai ta yi karatu, to karatun BOKO fa ake
nufi ba wai haddar Alkur'ani ake so ta kammala ba. Wasu daga cikin yaran sukan
tsinci kan su a halin takaici bayan kammala karatun, domin duk manemanta sun
gaji da jira sun gudu. Yanzu kuma ta kammala karatun, ta zama abar tsoro ga
maza, saboda tana da digiri, wanda yake sama da ita kuma ba zai neme ta ba
saboda gudun kada ya kasa samun iko a kan ta. Daga karshe sai ta tsofe a gida,
ta zama abar kwatance, ga digiri ga aiki amma ba mijin aure. Don haka a ji
tsoron Allah.
8. WA KE AMFANA DA KARATUN MACE
Idan mace ta kammala karatun
BOKO, sanin kowa ne, mijinta da 'ya'yanta su ne suke amfana da sakamakon
karatun kafin iyayenta ko sauran al'umma. Idan haka ne kuwa, ashe bai kamata
iyaye su tauyewa 'yarsu haƙƙinta ba a kan abin da ba lallai ba ne su amfana da
shi.
9. DAGA ƘARSHE
Wannan rubutun ba da kowa ake ba.
Nuni ne kawai nake yi wa al'umma.
KUKAN KURCIYA JAWABI NE....
Ina roƙon Allah ya yi mana
jagoranci, ya kuɓutar da mu daga dukkan sharri. Ameen.
Wassalamu alaikum
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.