Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mace Mai Ciki Tana Jinin Al'ada

TAMBAYA (53)

Asalamu alaikum warahamatulahi wabarkatuhu mallam ni dalibinkane inada tambaya allah yakara daukaka allah yabiyaku allah yasa kamuku da gidan aljana mallam tambayata shine idan mace tanada ciki tanayin jinin al ada  sai tambaya nabiyu idan nasadu da matata akwai wani ruwa fari yana fituwa agabanta nagode

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

Alhamdulillah

A al'adance dukkan mace mai ciki ba ta jinin al'ada la'akarida musabbabin zubar jinin al'adar yanada nasaba da rashin haduwar maniyyin namiji (sperm) da kuma qwayayen halittar mace (ovum ko kuma egg cells) wanda idan ba'a samu haduwarsu ba to qyanqyasar mutum (fertilization) cikin ikon Allah bazai auku ba

Idan wadannan halittun qwayayen (egg cells) suka karada mahaifar mace (uterus) basu ga abokan qyanqyasa ba (maniyyi da ake kirada sperm cell) sai kawai su mutu su koma jini (wato hemoglobin mai dauke da sinadarin qwayar iron da kuma protein) wanda a dabi'ance ake kirada jinin al'ada a shari'ance kuma jinin haida (haila) a turance kuma catamenia ko kuma menstruation (monthly period/cycles)

Kenan fitar da jinin al'ada ba karamar lafiya ce ga mace ba domin kuwa ta hakanne mace zata gane cewar budurcinta yana nan bi ma'ana babu wani wanda ya sadu da ita kuma mahaifarta (uterus) bata samu baquwar halitta ba (sperm cells) wanda a kowanne inzali (fitar maniyyi daya tak) da akwai yayan halittu qanana (microscopic) da idanunmu basa iya gani wanda adadinsu yakai ko kuma ya zarce guda 250,000,000 (miliyan 250) wanda a cikinsu da kyar dubunnai suke tsira a cikin dubunnan kuma daruruwa suke galabaita a cikin daruruwan kuma baifi guda ashirin bane suke tsira (a karshe dukkansu mutuwa suke wannan kuma cikin ikon Allah da akwai abinda ake kirada white blood cells sune suke kashe wadancan miliyoyin maniyyin) wanda a karshe dai guda daya ne tak yake iya qetara mahaifar mace (uterus) ya shiga ya hadu da qwan mace (egg cells) wanda suna haduwa zasu zama zygote daganan kuma a samu fertilization sai Allah Azzawajal ya tsara halittar da yaga damar fitarawa mace ko namiji. A haka aka samar da kusan kowa tun daga yayan Annabi Adam AS (Habil da Qabil) har zuwa dan Adam din da za'a haifa na karshe. Allahu Akbar ! (Tsoron Allah Madaukakin Sarki ya zama dole)

Wannan bincike ne da ilimin kimiyya ya tabbatar amman shekaru 1,400 baya tuni Allah Azzawajal ya sanar da Annabi Muhammad SAW;

( ثُمَّ خَلَقْنَا النُّطْفَةَ عَلَقَةً فَخَلَقْنَا الْعَلَقَةَ مُضْغَةً فَخَلَقْنَا الْمُضْغَةَ عِظَامًا فَكَسَوْنَا الْعِظَامَ لَحْمًا ثُمَّ أَنشَأْنَاهُ خَلْقًا آخَرَ ۚ فَتَبَارَكَ اللَّهُ أَحْسَنُ الْخَالِقِينَ )

المؤمنون (14) Al-Muminoon

Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa.

Allah Azzawajal shine wanda ya halicci mutum daga maniyyi kamar yanda ya fada a cikin littafin Qur'ani mai girma;

( خَلَقَ الْإِنسَانَ مِن نُّطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ مُّبِينٌ )

النحل (4) An-Nahl

Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.

( ثُمَّ جَعَلْنَاهُ نُطْفَةً فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ )

المؤمنون (13) Al-Muminoon

Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.

Dangane da batun jinin haila kamar yanda nayi bayani a baya cewar shi wannan cuta ne kamar yanda Allah Azzawajal ya fada a cikin Qur'ani;

( وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى

البقرة (222) Al-Baqara

Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne.

Don haka amsar tambayarka a taqaice shine; a iya dan karamin sani na, mace bata jinin al'ada a lokacin da take dauke da juna biyu kamar yanda dalilai a kimiyyance suka gabata. Duk da cewar abune mai yiwuwa mace ta samu jini alhalin bata dauke da juna biyu. Misali: Mace zata iya ganin digon jini wanda ya damfaru a jikin mahaifa saidai wannan ba jinin al'ada bane, ana kiransa  da suna "Implantation bleeding", haka kuma macen da take jinin al'ada kuma taji kamar alamun tana dauke da ciki to ba juna biyu bane, ana kiran abinda suna "Normal hormonal fluctuations" (Karin bayani kuma sai a tambayi qwararrun likitocin da ake kira da gynecologist)

Sai kuma tambayarka ta biyu wadda kayi akan fitar wani farin ruwa a gabanta

Shi wannan farin ruwan shine masana ilimin jima'i suke kiransa da orgasm, yana fitowa ne sakamakon qololuwar jin dadin sha'awa yayin saduwa. Yana fitowa ne da karfi, yana feshi, sannan kuma masana sunce fitarsa ba matsala bane kawaidai shi din sakamako ne ya bayyana na yanda jin dadin saduwar yakai maqura sannan kuma a cikin mata 100 (alal misali) baifi a samu mace 1 da take fitarda irin wannan ruwan ba

Zan danyi jan hankali anan, a duk lokacin da namiji zai kusanci iyalinsa to ya tabbatar da ya karanta addu'ar da Annabi SAW ya koyar;

Annabi SAW yace; Idan dayanku ya auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, sai ya ce;

اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.

Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.

(Ya Allah ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa.)

(Hisnul Muslim)

Idan kuma zai sadu da iyalinsa sai yace;

بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.

Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.

(Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi.)

(Sahih Al-Bukhari, Fath ul-Bari lamba ta 138 )

Sannan kuma kafin mutum yayi inzali (releasing) sai ya karanta addu'ar da Abdullahi Ibn Mas'ud (RA) yake karantawa; "Allahumma la taj'allish-shaidaani fimaa razaqtanaa nasibaan"

(Ya Allah ! Kada ka bawa shaidan rabo akan abinda za ka azurtamu)

(Imam Ibn Abi - Shayba a cikin Al-Musannaf fil Ahaadith wal - Athaar 3:402)

A cikin littafinsa "Hasken Addu'o'i", Mufti Taqi Uthman (Rahimahullah) yace "Daga cikin fa'idar karanta wadannan addu'o'in guda biyu, shine; a yayinda mutum ya shagala da jin dadin tarawa da iyalinsa duk da cewar firta hakan abin kunya ne amman addini ya koyarda mutum ya shagaltu da ambaton Allah a wannan yanayin ya zamana ambaton Allah Azzawajal shine farko da karshen ibadar ta sa. Abinda yake da alaqa da shauqin fata da fata ya koma ibada"

(Hasken Addu'o'i, P. 65)

Ya Allah muna roqon ka bamu mataye nagari, suma matan ka basu maza nagari. Allah ka tabbatar damu akan daidai ka bamu ikon koyi da sunnar Ma'aiki SAW gwargwadon iyawarmu.

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments