Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Ya Ba Ku, Mata Sun Karbe - Hausa Haiku 21

1.
Zamani ne ya
zo da sauyin yanayi
uwa ta zam y'a.

2.
Iyaye ne sun
gajiya sun kasa a
fagen tarbiya. 

3.
IImi maimakon 
wayarwa yasa wasu 
bayi girman kai. 

4.
Wayewa kuwa
ta yiwa al'ada da 
gargajiya war!

5.
Makahon so ya 
hana a shuka k'auna
Kan ka ce kwabo!

6.
Jahilci ya sa
daraja da k'imarmu
duk a warwatse.

7.
Kwaikwayo ya sa 
tari shiga k'unci da
halin ni y'asu. 

8.
Hak'uri kuwa 
d'oki da azar6a6i 
sun masa shan kai.

9.
Mutane ba mai 
gaskiya kowa cuta
ana ta kuka.

10
Aure ake yi
akan tubalin toka
kullum a rushe.

11.
Kowa ka ta6a
kuwwa yake ba kanta 
tsadar rayuwa.

12.
Mazan sun saki
hidimar gidajensu
a hannun mata.

13.
Su ci da kansu 
mazansu da yara. Tir 
da tozarta kai.

14.
Ya matan ke yi
ko oho! Mai sana'a
na yi, maras shi...?

15.
Yara a sake
suna bilinbituwa
ba sa karatu.

16.
Illa k'alilan
ke Arabi da boko
aike da aiki.

17.
Arewa an yi
sake tun da fari da
alk'iblar yara.

18.
Amma k'orafin
ya isa haka ku zo
mu sake lale.

19.
Manya da yara
kowa ya zage dantse
mu sa hannunmu.

20.
Mu cicci6a mu 
dage mu bar lalaci
lokacin ya yi.

21.
Duk nisan gari
da tattaki sahunmu
zai cim masa.

Kwalliya

From the Archive of:

Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +2348067062960

©2023 Tijjani M. M.

Post a Comment

0 Comments