Ticker

6/recent/ticker-posts

Zubar Hawaye

1. Zuciya in har akwai ta,,

Za a ƙyamaci ai mugunta.


2. Za kai suka ga cuta,

A gidanka da ma maƙota.

3. Kullum za kai hawaye,

Mutuƙar an zo da cuta.


4. Duk halitta in mutum ce,

             Zuciya kuma in akwai ta.


5. Ba ta cewa ya wuce ni,

Jifan da ya tsallake ta.


6. Ba ‘yar son kai ba ce ba,

Mara kishin ‘yan uwanta.


7. Zuciyar in mumina ce,

Tausayi shi ne adonta.


8. A gabas ne ko a yamma,

Ba ta ƙaunar masu ƙeta.


9. Ko masu kisa da roka,

Yan share wuri macuta.


10. Mai cin haƙin waninsa,

Ba na kwaɗayin ya huta.


11. Mai kisan yara ƙanana,

Abadan shi zan li’anta.


12. Mai kisan mata a Gaza,

Ban mas fatan rabauta.


13. Fatana na ji yai asara,

Кarshe rami ya rufta.


14. Sabaran ya Ahla Gaza,

Da akwai ranar wadata. 


15. Bashhiru jama’a Ramallah,

Duk usur yusrun gabanta.


16. Duk fa cuta za ta ƙare,

Bishiyar ƙarya gare ta. 

Na:

Murtala Uba Mohammed
15/10/2023
7:26 n.s.

Post a Comment

0 Comments