Ticker

6/recent/ticker-posts

Tagwayen Bakaken Turanci (Tasirin Rubutun Turanci da Larabci da Karin Harshe)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

690. Sai a yi hattara rubutun Turawa,

 Ba a biye shi bai kama da na Hausawa,

 Kwai harufan da an ka ɗauki na Turawa,

Sannan kuma kwai waɗanda an ka yi watsarwa,

  Tasirinsa namu ne zai cutarwa.

 

691. Wasu harufa da an ka sa a rubutunmu,

 Kuri ne kawai na su ‘yanbokonmu,

Ya yi ale-ale cikin ‘yan bokonmu,

Sai yawo da hankali da basirarmu,

  Sun ɗauke shi Hausa don dabircewa.

 

692. Sun ƙago tagwan baƙaƙe sababbi,

 Ba mu da su cikin rubutu kai dubi,

 Sun ƙago shi kuma gurin su a bi,

 Sun masa tanadi ga kalma fa a dubi,

  Sun ka saka su Hausa don lalacewa.

 

693. Ba mu da Ch a Hausa domin a kiyaye,

 In ko ka gan ta, kar ka sa sai ka kuranye,

 Ba a saka ta ka ji malam kai waye,

 In ko ka sa ta kai rubutun wawaye,

Don haka babu Chindo sunan Hausawa.

 

694. Amma “Cindo” ba mu yin jayayya nan,

 Don haka “C” kaɗai a bar saka “h” ɗin nan,

 Kar a game su Hausa ba ta da tsarin nan,

 Sai ka rubuta “C” kaɗai nan bagiren nan,

  Shi ne ƙa’idar rubutun Hausawa.

 

695. Ba mu da Ph a ƙara lura a kiyaye,

 Kar ka sake ka bi ma tsarin wawaye,

 Doka ta kwatanta komai kai waye,

 Ba a rubuta “Ph” a Hausa, kauce tawaye,

  Wannan sai cikin rubutun Turawa.

 

696. Cewa Mustapha kure ne tsabar sa,

 Haka ma can cikin rubutu in an sa,

 Ya zama kuskure cikin rubutun Hausa,

Ba shi zama kansan da an sato an sa,

  Sai dai Mustafa Imamin shiryarwa.

Post a Comment

0 Comments