Ticker

6/recent/ticker-posts

Ci Gaban Harshen Hausa a Yau

 

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

674. Yau harshenmu ya zamo gagara badau,

 Ya gagara ya wuce su shi gagara badau,

 Bai da sa’a duk ga harsuna malam dau-

 Re kai nazari ka san da ta yo fintinkau,

  Furce Afirka har ƙasashen Turawa.

 

675. Bi-bi-si, Amerika ta kama su,

 Hausa ake ta yi matsa kama tasharsu,

 Safe da rana har maraice a tasharsu,

 Hausa shirinta ko da yaushe burinsu,

  Jamus sun daɗe da harshen Hausawa.

 

676. Misra da Makka, har ƙasar Sin sun yarda,

 Ta mamayi harsunan batun har ga jarida,

 Kuma ga shi a zahiri, abin ya kore sheda,

Ba tamka gare ta harsuna  tun-tun can da,

  Farisa sui riƙo ga harshen Hausawa.

 

677. Libya tuni Gaddafi ya ce ya yarda,

 Al’ummar ya sani kuma ya shaida,

 Sun bunƙasa ga yawa ba su saranda,

 Sun riƙi gaskiya akwai su da al’ada,

  Bai jayayya ya aminta da Hausawa.

 

678. Ba harshe guda a Afirka da yak kutsu,

 Yas shiga yankunan ƙasashe yar ratsu,

 Al’ummarsa duniya sun warwatsu,

 Harshen Hausa ko’ina ya warwatsu,

  A gidan rediyon gabas da na Turawa.

 

679. Rediyo Ghana ba Asante suka yi ba,

 Ba wani yare da ya fi Hausa ake yi ba,

 Bayan Ingilishi ba harshe babba,

 Tamkar Hausa ko ba ka gane ba?

  Nijar ba a Zarma sai dai Hausawa.

 

680. Senegal Gambiyanmu Mali duka sa su,

 Sun yarda da Hausa ta ci yaƙi na dukansu,

 Ta mamayi harsunansu duk ta kama su,

 Sun yi mubayi’a  gareta sun yarda da kansu,

  Hausa a Cana ga Wolof bai motsawa.

 

681. Birnin Makka can wurin jifan shaiɗan,

 An yi muhalli a keɓe don jifar shaiɗan,

 Al’ummar duniya ka taruwa sai ka ga ɗan,

 Mutum bisa ɗan mutum suna jifar shaiɗan,

  Ga shi ɓato-ɓato rubutun Hausawa.

 

682. Rasha harsunansu wane a ƙidaya?

 Sun yi yawa malam ka je ka ga aya,

 Ga ƙiyasin yawansu sai dai a yi ƙarya,

 Kai na wasusnsu masu sa manyan kaya,

Duk da hakan ga sun biɗayo na Hausawa.

 

683. Nan a cikin gida Fulani sun yarda,

 Sun lamunta ga abin nan ga takarda,

 Ba su da ja da Hausa kowa ya shaida,

 Sun yi aro gare ta, sun ɗau al’ada,

Sun zama kaɗo tun da nan aka lelewa.

 

684. Dubi Kanuri ba alanguburo yanzu,

 Can a ƙasarsu Borno komi ya canzu,

 Al’adunsu sun ɓace, du sun cazu,

 Harshen Hausa ya yi ƙarfi can yanzu,

  Birnin Yerwa Hausa ɗai ke haskawa.

 

685. Yarbawa suna gani an ka wuce su,

 An zaka har ƙasar su an zarta su,

 Sun saki nasu sun aje ɗan harshen su,

 Al’adunsu Hausa yanzu du ta canye su,

  Badun, Oyo, ga sarautun Hausawa.

 

686. Su Igbo sun aminta mun zan zozozo,

 Kun san su suna riƙo ga su da ƙwazo,

 Sun riƙe nasu, kafin Hausa tac ci Uzo,

 Duba abinci lokacin da Hausawa suka zo,

  Sun bar eba yau tuwo suka tuƙawa.

 

687. Inda gafara nan kar a kiɗe ka,

 Hausa gabanka to gayamin ra’ayinka?

 Ka ba da gari? Ko ko sai an ta da ka?

 Ku ka maƙwabtaka da suwa ku ag ga iyaka,

  Yau Neja ina kwatancin Hausawa?

 

688. Zarma da Borgu Hausa yau ta taushe su,

 An kakkaɓe harsunansu du an kwashe su,

 Borgu da Hausa Zarma ko an zarta su,

 Al’adunsu yanzu du sun ya da su,

Gun suturar jikinsu sun zan Hausawa.

 

689. Sai shukura mu ƙara gode Ilahinmu,

 Ya ɗaukaka Hausa ta zamo tsaninmu,

 Ya tattara harsuna ƙasanta abin sonmu,

 Ga mu da godiya ga Allahu Karimun,

Nasara wadda yaz zubo gun Hausawa.

 


 

Post a Comment

0 Comments