Ticker

6/recent/ticker-posts

Sameer Da Sameerah (Complete Book)

💍💍💍💍💍💍

SAMEER DA SAMEERAH

💍💍💍💍💍💍

(Hot love and short story)

Free book💍

Mallakar
Rukayya Buhari Sauwa
(Rukee Sauwa)💍

Page:1️&2️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

A babbar University ɗin da ke Kano, wasu kyawawan yan'mata na hango su ukku sanye suke da kaya iri ɗaya, doguwar abaya ce maroon colour sai sukayi rolling ɗin ƙaramin mayafinta, sai wasu school bag ba ka da suka rataya ɗayan hannu, sun yi kyau matuka domin kuwa ya haska white skin ɗinsu. . .

"Please dear ku yi sauri mukarasa kun san halin lecturer nan ba mutumce ne da shi ba zai iya yimana walaƙanci” cewar ta tsakiyansu. . .

"Mtssss ke wallahi Sameh kin cika mugun tsoro bafa dukan ki zan yi ba all what he can do ya ce he will not allow you to enter and so what"

"Haba Leemah yanzu idan yaƙi barinmu mu shiga yaina soza mu yi ko yabari sai ya kusa fita ya ce mu shiga kin san dai ba ganewa ina soza mu yi ba haba, ga Physical Psychology ya nada rikitarwa " cewar ta gefen damanau. . .

"Gaya mata dai Feenah may be she will understand" cewar Sameerah dai dai suna shiga class ɗinsu. . .

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

. . . . Wani gaye na hango ba zai wuce 20 years ba sanye yake da white juns and red t-shirt sai Facing Cap white ya sa ta gaba baya sai wata school bag black daya goya a bayanshi, wayar shi ce rike a hunnushi kirar Xplus. . .

"Baaba! Baaba!! Baaba!!!"tsayawa ya yi tare da kin juyawa domin yasan mutum daya ne zai kira shi haka, wani matshi ne wanda ba zai wuce shiba a shekaru ya karasu tare da faɗin. . .

"Yane ya ake ciki "normal ne Faruk muyi mu shiga tun bai shiga ba " ok Sameer muje” tafe suke suna tattaunawa har suka shiga class ɗinsu. . .

Sameerah ce bakin window tana hango lecturer ɗinsu tafe da sauri ta tashi domin kumawa mazauninta, don batasun abin da zaisa ya kureta waje. . .

Wajen saurin da take ne jinta kawai ta yi ajikin mutum, shi kowa ganin ta buge shi ne kuma tana ƙoƙarin faɗuwa kasa ne ya sa yayyi saurin riƙo kafaɗunta. . .

Sosai suke kallon cikin idanun juna zuciyuyinsu suna bugawa at the same time, da sauri ya saketa ba wai don ya gaji da kallonta ba a'a sai dan jin gyarar muryar da lecturer ya yi ton bakin kufa. . . .

"Sorry shi ne abin da suka faɗa atara kafin kowa ya zauna sakamakon shigowar lecturer. . . .

Yaudai ta kasa gane kanta gabaɗaya bata gane komai ba har lecturer ya gama suru tunsa ya fice. . .

Ɓangaren oga Sameer ma haka ne kawai da ya zauna class ɗinne bawai dan ya fahimtaba, ka sancewar yau Friday kuma lecture ɗaya me dasu ya sa yana fita kuwa ya watse. . . .

Idan kun ji daɗinsa to in ga ruwan comments. 💍

Comments and Share fisabilillah💍

Taku har kullum

(Rukee Sauwa)

For WhatsApp and Call, contact me at💍

07030446917💍

Page:3️&4️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

. . . . . "Wallahi na gaji sosai "cewar Feenah tana yamutsa fuskanta kamar ta yi kuka” wai dear me yake damunki ne na ga gabaɗaya kin wani sauya lokaci ɗaya” cewar Leemah tana tsayuwa gaban Sameeh "nima dai na fahimci hakan" cewar Feenah dukansu ido suka tsura mata.

"Uhm baaa komai fa " ta yi maganar a rarrabe " sure” suka faɗa tare ba wai dan sun yadda ba ne "yeah"tace dai dai suna isa inda sukayi parking.

Motarta ta shiga tana mai ɗaga musu hannu " wait" Leemah ta ce mata tana mai ɗaga mata hannu tsayuwa ta yi " uhm dama na ce za mu zu muyiwa Dady ya hanya anjima za mu kwana ranar Monday sai mu shiga school" ohk wallahi ma rose ya yi fushi kuma ba zai haƙuraba har sai kun kawo alawar madara " ta yi maganar tana dariya.

" Uhmum kawai dai ki ce a taimaka miki da abu basai kinyiwa rose ƙarya ba bye” ta yi maganar tana dariya haɗe da shigewa motarta.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

A wani babban gate ta yi horn gate man ne ya buɗe get ɗin, shiga ta yi da mitar parking space ta nufa bayan ta yi parking ne ta fito direct wajen gate man ɗin ta nufa.

"Baba ina wuni ya aiki” ta faɗa tana mai duƙawa” kallonta ya yi da murmushi a fuskarshi ya ce " lafiya yar'albarka ya makaranta” Alhamdulilla "to madallah Allah yataimaka "ameen Baba ni zan shiga ciki " to a fito lafiya "

Tashi ta yi ta nufi ƙofar da za ta sadata da cikin gida, sosai Baba mai gadi yake mata addu'o'i kala kala tare da yaba tarbiya irinta yarinyar oganshi.

A parlour ta iske Momy zaune tana kallon BBC News gefenta fruit ne masu rai da lafiya ta ke sha " salamu alaikum" wa'alaikus salam " ina wuni Momy "tayi maganar tana rungumeta "lafiya waike bikisan kingirma ba ko sukike ki ɓalla ni ni matsa can"

Momy ta yi maganar tana dungure mata kai " uhm uhm kin ga matsalarki ko Momy inda Dady ne ba zai ce zan ɓalla shiba duka duka nawa na ke bafa ƙina ce daniba "

Tayi maganar tana yamutsa fuskanta kamar za ta yi kuka " to ai saiki je ki sameshi "a'a lafiya wayake ƙuƙarin samin sugar 🌹 kuka "

Cewar Dady da shigowarshi ke nan parlourn" yauw 🌹 ka ga Momy ku wai zan ɓalla ta " kin ga kyaleta " dariya ta yi haɗe da zuwa da gudu ta faɗa ƙirjinai” ka gani ko ni inbata ɓallaniba kaita karyaka " ba komai 🌹 yanzu ki je ki yi wanka kici abinci ki huta kizo na goya ki "

"Da gaske Dady " eh mana " yes! yes!! yes!! " ta yi maganar tana tsalle sosai " kin gani ko Momy ga shinan za a goyani hooo"

Tayi maganar tana cika hannunta da yankakken tuffa ɗin da Momy ta ajiye tana kaiwa bakinta tare da yima Momy gwalo da kuma nufar steps da gudu at the same time.

" Allah ya shiryaki " cewar Momy tana girgiza kai " ameen Dady ya ce " ai dama kai kake ɗaure mata gindi take wannan sha shanci yaushe yarinya kamar wannan za ta yi ci gaba da yin wannan yarintar "

Momy ta yi maganar tana kallon Dady daya haɗe hannayenshi a ƙirjinshi yana kallon Momy matsowa ta yi har kan kujerar da take ya zauna kusa gareta tare da rungumeta yana jin ƙaunar matar tasa har cikin ransa ya ce " is ok kibarta lokaci ne”

Luf ta yi ajikinsa tana sauraron bugun zuciyarsa tana mai ƙara ƙaunar mijinnata. . .

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

Tana shiga room ɗinta ta cire kayan jikinta tana mai tura sauran tuffa ɗin daya rage a hannunta tana jin ƙaunar iyayen nata har cikin ranta akowane lokaci takan godewa Allah daya bata iyaye na gari tare da family mai cike da nutsuwa tarbiya kwanciyar hankali wadata tare da fahimtar juna.

Bayan ta yi wanka fitowa ta yi ɗaure da towel iya guiwa wani ƙarami tana goge gashin kanta wajen tafkeken mirrow ɗinta ta nufa mai cike da kayan shafawa na mata tare da turarukka.

Maikawai ta shafa wadrob ta buɗe ta ciru wata doguwar riga ta ruba mara nauyi tasa sallaya ta shimfiɗa ta kabarta sallah azahar tana gamawa Ƙur'ani mai girma ta ɗauka cikin zazzaƙar muryarta ta fara karantawa saida ta yi hizib biyu sannan ta ajiye.

Frij ta nufa ta ɗauki yogurt guda ta shanye sannan ta kwanta a saman lafiyyayan bed ɗinta da yasha pink and white bedsheet da niyar ta huta kafin su Leemah su zo. . . . .

Page:5️&6️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

. . . . " Madam kitashi baccinya isa haka nan bamota kawai” cewar Feenah tana kallon Sameerah dake shimfiɗe a kan bed ahankali tafara buɗe idanunta dasuka mata nauyi tashi ta yi toilet tashiga wanka ta yi tarefa a'lwala fitowa ta yi wadrob ta buɗe dugowar riga ta fidda jar atamfa ba tada wani style undies ta fara sawa sannan rigar sallaya ta shimfiɗa ta kabarta sallah saida ta idar sannan ta kallesu ta ce " please ku yi haƙuri wallahi bacci ne ya kwasheni kunga Momy parlour" eh Feenah ta faɗa tare tareda hayewa bed" Dady dai ba mu ganshiba” cewar Leemah tana ajiye wayar hanunta” eh na san yanzu ya fita saidai idan ina soza mu yi dinner za ku ganshi ta yi maganar tana linke sallayar hanunta” ku tashi mu shiga kitchen muyi girki please” cewar Leemah tana tsayuwa gaban bed ɗin.

" Msssss daman dan kada na yi bacci ne za kici muje kitchen" Feenah ta yi maganar tana fita daga ɗakin dariya suka sa sannan suka bi bayanta.

Momy ce zaune a parlour tana lazimi da counter gaidata sukayi saida ta idar sannan ta kallesu tace” harkun fito ina zakuje haka " Momy dama kitchen za mu shiga muyi dinner me za mu girka ne” Leemah ta yi maganar tana rungume Momy ta baya " aida kunbarshi daughter domin na san biyunnan ba su sun aiki "

" Aiko Momy ku yanzu ita waccan wai barci takeji " ta yi maganar tana nuna Feenah" na sani ai Allah dai ya shiryasu kawai ku girka abin da kukesu sai ku yiwa Dadynku abinci marar nauyi ni komai aka girka zani”

" Ameen suka faɗa a tare suna shiga kitchen.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

A ɓangaren Sameer kuwa kuda ya fito dubata ya farayi ku ina baiga wannan kyakyawar yarinyarnan data hanashi sakat amma ya yi a'lƙawarin cewar rannan Monday zai yimata magana.

Motarshi yanufa sai guest dake cikin garin Kano a wani danƙareren gida ya yi horn gate man ne ya buɗe get ɗin shiga ya yi da motar ciki parking ya yi ya nufi ƙofar da za ta sadashi da parlourn gidan da sallamarshi ya shiga cikin parlourn Abba ne zaune yana karanta jarida ɗagowa ya yi yana kallon ɗannashi da murmushi a fuskarshi ya amsa masa.

" Son kadawo sannu da zuwa ya makarantar" ya yi maganar yana rungumeshe tare da zaunar da shi " lafiya Abba yau ba ka fita office ba ne” ruwan daya tsiyayo a cup ya miƙamishi amsa ya yi yana kafa bakinshi.

" Eh kawai yau banajin daɗi shi ya sa ban tafiba” lafiya miyake damunka ko muje hospital ne ko nakira likitanmu ne ya zo"

Yayi maganar damuwa ƙarara a fuskarshi” a'a kawai ciwon kai ne yanzu ka tashi kaje kayi wanka kaci abinci saika fito mutafi masjid tashi ya yi jiki ba ƙwari ya nufi ɗakinshi direct toilet yanufa wanka ya yi yayi brush tare da ɗauro a'lwala fitowa ya yi ya faɗa kan bed ɗinshi yana murmushi tunawa da ya yi da fuskar kyakyawar yarinyarnan data kwance mishi lissafi dariya ya yi lokacin data ware manyan idanunta masu ɗauke da zara² eyeslersh baƙiƙirin murmushi ya yi tare da lumshe idanunshi ahankali ya furta " primer amor ( my first love)". . .

Idan kun ji daɗinsa to in ga ruwan comments. 💍

Comments and Share fisabilillah💍

Taku har kullum

(Rukee Sauwa)

For WhatsApp and Call, contact me at💍

07030446917💍

Page:7️&8️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

. . . . . Sai wuraren magriba suka kammala girkin ɗaki suka koma wanka sukayi haɗe da ɗauro a'lwala sallah sukayi bayan sun idar ne suka zauna suka fara fira.

" Dear ya kamata muje shopping tomorrow fa musamo wasu kayayyaki " cewar Feenah" gaskiya ne " cewar Leemah

Nisaw ta yi haɗe da faɗin" ohk zan yiwa Rose magana " muje muyi sallah isha'i”

Tashi sukayi sallah suka gabatar bayan sun idar fitowa sukayi domin yin dinner duk suna zaune a parlour suna jiransu da gudu ta faɗa jikinshi tare da faɗin

" Rose barka da yini " anyini lafiya sugar" cewar Dady yana shafa gashin kanta daya lafe a fatarta " lafiya ƙlau alhamdulillah"

 "Dady barka da yini” Feenah da Leemah suka faɗa a tare suna mai zaunawa kusa da Momy" lafiya ƙlau yaran Dady ya gida " ya yi maganar yana faɗaɗa murmushinshi "Safeenah ya mahaifin naki dan garama takwarana( mahaifin Haleemah) muna haɗuwa ku dazu mun yi meeting amma Dadynki baya ƙasar duk da muna magana akai²"

"Lafiyanshi ƙlau Dady ya mace ya kusa dawowa " to Allah yamaisheshi lafiya” muje muyi dinner" cewar Momy tana nufar daining dukkansu zama sukayi a kan kujerun daining.

"Yauwa Rose dama mumason zuwa shopping tomorrow" Sameeh ta yi maganar tana kai lomar abinci bakinta " to ya yi bari na yimiki transfer saikuje” angode Allah ƙara girma " suka faɗa a tare” ameen" ya furta ahankali.

Yau da wuri suka tashi sukayi abin da ya kamata suka shirya domin zuwa shopping driver ne ya kaisu ya maidasu yayinda suka sayo kaya masu yawa.

Weekend ɗinga sun yi shi ne cikin farin ciki da ƙaunar juna.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

Tashi ya yi ahankali ya shirya domin zuwa juma'a bayan sundawo kuwa gaba ɗaya yaka sa gane kanshi komai yake ganin ta yake kuda kuwa yana maganane da mahaifinshi.

Shi sam wannan weekend ɗin baiji daɗinshi ba.

Yau ta kama Monday dayake su Leemah ranar lahadi da dare suka koma sakamakon zazzaɓin daya kama mahaifiyar Feenah suduka suka je bayan sun duba tane shi ne ita Sameeh ta dawo gida.

Duk saurinta kuda taje har anshiga musu gashi yau accounting suke da test kuma baya bari mutum ya shiga idan ya shiga.

Kumawa ta yi kusa da wata bishiya ta zauna ta haɗe fuskarta da guiwa tana kuka.

Yau gaba ɗaya bayajin ƙarfin jikinshi ahankali ya shirya wucewa ya yi da sauri domin yasan ba zai samu test ɗin accounting ba amma yasan zai samu second lecture.

Hakan kuwa aka yi kuda ya je anshiga yana zuwa ya samu bishiya ya jingina bayanshi yana mai dafe saitin zuciyarshi daka bugawa da sauri da sauri.

Ita ma sosai zuciyarta ke bugawa amma ta rasa dalilin hakan, sautin kuka yaji bayan bishiyar yana juyawa ya ganta ta duƙe bilhakki kuka take.

" Aslamu alaikum" shi ne abin da ya furta sosai zuciyarta ke bugawa a hankali ta ɗago idanunta da lashes ɗinta suka jiƙe da hawaye " amsa sallamar ta yi ahankali sun yi shiru na tsawon lokaci ya katse shirun ta hanyar faɗin.

" Sunana Sameer Muhammad canji " murmushi kawai ta yi sake cewa ya yi " ba za ki gayamin sunan naki ba ne ku yana da tsada ne sosai " uhm sunan ba daɗi shi ya sa ban gayamaka ba ne " daga ganin ki kyakyawa dake sunankima zai yi daɗi” sunana Sameerah Abubakar Daula " Wow ni ce name can I be your friend please” gyaɗa kanta ta yi ahankali” murmushi ya yi mai taren ma'anoni.

"Dear meyasa kika makara yau " Leemah ta yi maganar cikin damuwa” wallahi kawai ban tashi da wuri ba ne " hmmm kin ganki ko da mugun bacci " Feenah ta faɗa tana dungure kan Sameeh.

" Yauwa ga kawayene yan'uwana aminaina kuma jinin jikina” ta ƙarashe maganar da alamar tana faɗin abin da ke zuciyarta " kishi ne yafito ƙarara a fuskarshi ahankali ya daure ya ce " sanunku " yauwa” suka faɗa.

" Muje ka mutar kwandala can yanzu na ga wucewarta kagin ya shiga " wucewa sukayi gaba ɗayansu bayan antashi ne gidansu Feenah suka nufa domin ƙara duba lafiyar mahaifiyarta. . . .

Idan kun ji daɗinsa to in ga ruwan comments. 💍

Comments and Share fisabilillah💍

Taku har kullum

(Rukee Sauwa)

For WhatsApp and Call, contact me at💍

07030446917💍

Page:9️&🔟

Bismillahir Rahmanir Rahim.

. . . . Jiki da sauƙi kwanansu biyu ko waccensu ta kuma gida.

Sunsamu hutun firs semester hakan ya sa suka rage shaƙuwa amma suna haɗuwa akai².

Shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin"SAMEER DA SAMEERAH" duk ranar da ɗaya baiga ɗaya ba tufa ranar ba kwanciyar hankali sosai suke sha'aninsu duk da mutane da dama na cemusu suna soyayya amma sam sunkasa gasgata haka amma shi Sameer yariga da ya yadda cewa yana son Sameerah kuma ya yi a'lƙawarin cewar yau zai sanar mata.

Zaune take saman makeken bed ɗinta wayar ta ce tafara ringing bata ɗauka ba har ta tsinke domin tasan mai kiran domin special ringtone ne tasan idan ta ɗaga ba za ta samu damar yin wanka yanzuba tashi ta yi tashiga wanka bata ɓata lokaci ba ta fito ɗaure da towel mirror tanufa stole ta jawo ta zauna wayarta ce tasake ringing ɗauka ta yi tare da sa wayar hanspree ta ci gaba da shafa ma laulausar fatarta da mayukka masu ƙamshi.

Daga ɗaya ɓangaren Sameer dake zaune saman bed naunauyar ajiyar zuciya ya sauke ahankali amma har Sameeh saida taji magana yafara kamar wani mai kuyun magana.

"Dear shi ne kika ƙi ɗaga wayana kin san irin mawuyacin halin da na tsinci kaina kowa” ya ƙarashe maganar tare da damuwar sosai.

" Am sorry ina wanka ne please” ta yi maganar tana kama kunnenta kamar yana ganin ta " alright ba matsala dama na ce bari na kiraki domin ina son na ganki gaskiya” ohk ina za mu haɗu" inda muka saba haɗuwa around 4pm " Allah yakaimu shi ne abin da ta furta.

Kashe wayar ya yi tare da tashi ya shiga toilet domin shiyawa tun da yanzu har 3pm tayi.

Wadrob ta buɗe abaya ce ta fitar Marron tare da ƙaramin gyalenta plan shoes black and black bag ta fitar, nidai na fahimci tanason Marron colour sosai.

Kayan tasa sun yimata kyau sosai rolling ɗin ƙaramin gyalenta ta yi Jakarta ta rataya wani agogon gwal ta sa da wasu ƙananan Ring's masu kyau sosai hannayenta suka haska.

Fitowa ta yi Momy da Dady ne zaune suna fira da murmushinta ta iso zama ta yi tare da gaishesu amsawa sukayi Dady ne yafara tsokanarta " a'a Rose irin wannan wankan fa kudai-kudai " kudai me " faɗa kamar za ta yi kuka” bakomai ina za ki je ne haka " uhm dama zanje wajen su Dear ne " to ya yi Allah ya kiyaye hanya” ameen tafaɗa ta amshi makullin motarshi tafita.

Nisawa Momy ta yi haɗe da faɗin" Alhaji wannan yarinyar ta canza kwana biyu ina lura da yawan wayar da take yi kuma wannan adon hmmmm" to mene ni ma nafahimci haka saidai kawai ina so ne na ga gudun ruwanta har zuwa yaushe ne za ta ɓoyemon" to Allah yataimaka” ameen" suka ci gaba da firarsu.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

Fitowa ya yi mai ya shafa tare da garwaye laulausan gashin kanshi da mayukka bayan ya gama tufafi ya fitar Marron yadi mai taushi anyimishi ɗinkin kaftan amma rigar bata kai guiwa ba agogon gwal white ya ɗaura black cover shoes yasaka tutare ya feshi jikinshi da shi car key yaɗauka tare da zuba wayarshi a aljihunshi fita yayi.

Abba ne zaune a parlour yana karanta jarida ɗagowa ya yi ya ƙure tilon ɗanshi da idanu " son ina za ka je haka ne " dama za mu fita nida friends ɗinane " murmushin manya Abba ya yi tare da faɗin" kudai za ka je wajen surukata ce " zare ido ya yi kafin ya ce” haba Abba nifa na yi ƙarami” shike nan Allah yakiyaye " ameen" ya ce tare da fita daga gidan.

Direct DALILIN KU RESTURANT ya nufa dake cikin garin Kano lokaci ɗaya suka isa kowa kallon dan’uwansa yake cike da shauƙi ɗaya zama sukayi lemo da ruwa aka kawo musu sun kai 30mnt ba wanda ya ce komai sai kallon-kallon suke daurewa ta yi a hankali ta furta.

" Kace ina soza mu yi magana amma kayi shiro " uhm I want to tell you my heart secret" kallonshi ta yi cike da rashin fahimta ci gaba da magana ya yi kamar haka.

" SAMEERAH am ready to secrify my heart for you, tun ranar da na fara ganinki na ji ajikina wata rana hannuwanki za su ka sance riƙe da nawa na tsawon rayuwa,

Zuciyarki za ta zamo makwancina na har abada.

Kece ƙaddarar da na jima ina tsimayin tarar da ita a rayuwata, zan ka sance a duk inda kike, zan tsaya a duk inda kika tsayar dani, ina sonki adadin son da kalmomi ba za su iya siffantuea ba. . . . . .

Idan kun ji daɗinsa to in ga ruwan comments. 💍

Comments and Share fisabilillah💍

Taku har kullum

(Rukee Sauwa)

For WhatsApp and Call, contact me at💍

07030446917💍

Page:1️1️&1️2️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

. . . . . "Bazan taɓa mantawa da wannan ranar ba, wadda dare ya yi naka sa bacci acikinta saboda tsabar tunaninki, wato ranar da na fara ganinki”

Numfasawa ya yi ahankali kafin yaci gaba da faɗin.

"Idan har ba kyajin irin yadda nake ji akanki a yanzu to tabbas na san za kiji irin hakan bayan na mace”

A razane ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta sake dukar da kanta.

" Sameehna ke kaɗai ce nake gani kullum a cikin barcina, ttytyggb kece abar begena kuma kece wadda nakeso, domin a wurinki nake tsammanin farin ciki da nake fata ina sonki”

Ahankali ta sauke ajiyar zuciya da ta yita ba adadi kafin tace.

" Ina matuƙar ƙaunarka ina sonka kuma na daɗe ina mafarkin wannan ranar na karɓi soyayyarka no matter where we are i will never left you ina tare da kai” ta ƙarashe maganar tana barin wurin motarta ta shiga a 360 tabar wurin.

Direct gida ta nufa sosai take farin ciki da ka ganta ka san tana cikin shauƙi Momy ta tarar a parlour ita ɗaya faɗawa ta yi a kan jikinta tana dariya haɗe da sumbatar kumatunta "Momy yau ina cikin farin ciki sosai fa” ta yi maganar tana ware manyan idanunt.

" Nidai ki ɗaga ni inba sokike ki karya niba " ta ƙarashe maganar tana dunguremata kai " kin gani ko Momy" ta yi maganar tana tura baki " ohh sorry daughter meyake faruwane uhm gayamin " albishirinki "

" Goru fari ƙal" kin yi suriki” ta yi maganar tana kulle fuskarta da tafukan hannayenta” to Masha'Allah haka ake so ya sunanshi kuma daga wani gida yake "

"Uhm sunansa Sameer Muhammad canji” dafe gaba Momy ta yi tare da maimaita sunan " lafiya Momy akwai wata matsala ne " uhm babu komai Allah ya kyauta ki gayawa Dadynki idan yadawo " batare da wani tunaniba ta miƙe tare da faɗin" to nizanshiga ciki” bata jira amsar taba ta haye steps.

Numfasawa ta yi kafin ahankali ta ce” Allah kazaɓa mana abin da ya fi zama alkhairi” amma tana tunanin yadda mijin nata zai karɓi wannan al'amari.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

Tashi ya yi ahankali ya nufi motarshi ya daɗe zaune cikinta kafin ya tafi sosai yake farin ciki kuda ya' isa gida Abba nanan zaune gading yana shan iska ta baya ya rungumeshe tare da faɗin.

" Abba na tun bayan rasuwar mahaifiyata ban taɓa farin ciki irin wannan ba wannan yarinyar alkhairi ce a rayuwata "

Juyu da shi Abba ya yi kafin ya ce” son wannan wace yarinya ce haka zanso ganin ta zankuma so sanin wace ce ita " karka dama Abbana sunanta Sameerah" Masha'Allah ya sunan mahaifinta " uhm na manta " to kusan yamana rana muhaɗu da mahaifinta nanda ƙarshen satinnan kafin na yi tafiya " to ya yi bari na shiga ciki "

Tunani yafara yi cikin nutsuwa da kuma tunu matarsa da abunda ya faru tun bayan rasuwar ta ɗanshi ƙwalli ɗaya a duniya bai taɓa farin ciki irin wannan ba don haka ko wa ce ce wannan yarinyar yazama dole ta zama mallakin ɗanshi indai suna son juna.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

Ƙarar cukali ne kaɗai ke tashi a dening kallon ta Dady ya yi cikin ƙaunar yar' tashi ya ce” Rose ɗazu ummanki ta gayamin wani albishir mai daɗin gaske da gaske ne " eh 🌹" to ya yi ta ce sunan yarun Sameer ko" kaɗa kai kawai ta yi " shi ke nan ki sanar mishi cewa ina son haɗuwa da shi kafin end of this week saboda zan yi tafiya” to Rose” uhm uhm SAMEER DA SAMEERAH ke nan" dariya ta yi tashi ta yi da gudu ta bar wurin tana shiga room ɗinta ta kira rabin ranta domin shaida mishi sakon Dadynta ring biyu ya ɗaga tare da faɗin.

" Amincin Allah yatabbata agareki yake masoyiyata abin alfaharina farin ciki na hasken dake haskaka zuciyata farin wata mai haskaka sararin samaniya” lumshe idanunta tayai tana jin daɗin kirarin da yayimata " kaima haka dama Dady ne ya ce na gayamaka kasamu Abba ku yi magana yanason mu haɗu kafin end of this week saboda zai yi tafiya”

" Alhamdulillah ni ma haka Abba ya ce " Wow Masha'allah to yaushe za mu cemusu " uhm muce musu ranar Friday kawai” to ya yi mezan samo " saurin katse wayar ta yi tana murmushi.

Shima murmushi ya yi kafin ya je ya sanar da Abbanshi ya yi farin ciki da hakan sosai.

Kiransu Feenah ta yi ɗaya bayan ɗaya ta ce musu suzu akwai magana ai kamar jira suke suka fara shiri. . . . .

Idan kun ji daɗinsa to in ga ruwan comments. 💍

Comments and Share fisabilillah💍

Taku har kullum

(Rukee Sauwa)

For WhatsApp and Call, contact me at💍

07030446917💍

Page:1️3️&1️4️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

. . . . . . Bajimawa suka isu Feenah ce ta kasa haƙuri da zaman da suka daɗe suna yi kamar wasu kurame ta ce " Dear kince akwai magana amma kin yi shiru" gaskiya kam ki gayamana " Leemah ta faɗa tana gyara zamanta.

" Hmmmmm kudai ɗazu mun haɗu da mutumenku " wa Sameer" Leemah ta ce " to idan ba shiba waye kin ga kyaleta ci gaba " Feenah ta faɗa tana yiwa Leemah hararar wasa.

Nan tabasu labarin duk abin da ya faru har wayar da sukayi yanzu, shewa suka sa suna tafawa " to Allah yatabbtar da alkhairi” suka faɗa a tare” ameen shi ne abin da ta furta” ci gaba da firarsu sukayi a nan gidan suka kwana da safe suka wace.

Ta gayawa Dady yadda sukayi da Sameer ya yi farin ciki sosai.

Shaƙuwa ta ƙara shiga tsakanin SAMEER DA SAMEERAH wanda yanzu sun kuma makaranta sosai suke zuba love abinsu yau ta kama Friday dayake ba su shiga school ba da wuri suka shirya saidai gaba ɗayansu zuciyuyunsu na yawan faɗuwa basusaan dalilin hakan ba a DALILIN KU RESTURANT suka shirya haɗuwa.

Abba na gani zaune gefenshi kuma Sameer ne dukkaninsu sun yi shiga ta alfarma sai duba watch ɗin dake ɗaure a hannunshi ya yi a karu na ba adadi ya ce " Anya kuwa za su zu Sameer" eh Abba ka ƙara hakuri wata kila gusulu ne ya yi yawa amma yanzu za ka gansu "

" Yauwa gasunan" tashi sukayi suka nufi motar buɗewa Dady ya yi yafito saidai me juyuwar da zai yi wa zai gani.

Nuna juna suka dingayi da yatsa amma sunkasa furta komai” Abba ina wuni” cewar Sameerah tana duƙawa, ku kallonta baiyiba saima wani mugun kallon dayake binta da shi " ta ɓangaren Sameer ma gaida Dady ya yi amma ko ƙala baice mishi ba saima magana daya fara da mahaifinshi.

" Dama kaine Allah yarabani da haɗa zuru'a da kai " ni wallahi da na haɗa zuru'a da kai na gwammace shi ma Sameer ɗin ya mutu mtssss" ya ja tsaki tare da fara jan hannun Sameer yana ƙoƙarin sakashi a mota sai tirjewa yake yi kwacewa ya yi yanufi Dady dake ƙoƙarin saka Sameerah mota har ya buɗe murfi " Abba kataimakeni dan girman Allah ba zan iya rayuwa babu Sameerah ba ka taimakeni kamar yadda Allah yataimakeka " wallahi ku mutuwa zaka yi ba za ka aure taba " kuka sukeyi sosai wanda dole mai karatu ya tausaya musu.

Suna isa gida Sameerah ta buɗe murfin motar ta nufi cikin gidan, Momy dake zaune tana jiran dawowarsu ta tashi ta nufi ƙofa, saidai me tana buɗewa Sameerah ta faɗa jikinta tana kuka mai tsuma zuciya.

" Ke lafiya me yafaru haka ina magana kin yi shiru ina Alhajin yake” duk ta rikice, Dady ne ya shigo ba ku sallama” Alhaji lafiya ya na ga Sameerah tana kuka wai me yafaru ne " ki tambayeta mana " ya yi maganar yana nuna Sameerah dake durkushe tana rusa wani irin marayan kuka.

" Ai tun ɗazu nake tambayarta ta yi shuru to kai kayi min magana mana haba” kin san waye take so kin san ɗan gidan waye to ɗan gidan maƙiyinane duk duniya banida maƙiyin dayakai Alhaji Muhammad canji, wai shi take so"

Ya ƙarashe maganar yana huci da alama abin da ya furta har jikin zuciyarshi yake faɗa” to saime udan ɗanshi take so ka ajiye kiyayyarka a gefe ka fuskanceta mana haba” Aisha” ya furta maganar da karfi” wallahi kin ji ne Allah zan iya sakinki a kan wannan maganar dama ke kike hure mata kunne ko to wallahi dukkanku zan yi maganinku " ya yi maganar yana barin wurin.

Sosai maganar shi ba iya Momy ba har Sameeh saida abin ya firgitata domin tun tana karama mahaifinta bai taɓa kiran mahifiyarta da sunantaba sai yau har yana furta kalmar saki kai cuna shi ne abin da ta ke furtawa a cikin zuciyarta.

Lallashinta Momy ta fara da kalamai masu daɗi nan ta samu ta shawo kanta har ta yi shuru rakata ta yi har ɗakinta ruwan wanka ta haɗa mata bayan ta yi abinci ta bata kadan ta samu ta ci sai bacci.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

"Haba Abba miye haka na gayamaka cewar ina son Sameerah Ina kaunarta har cikin zuciyata amma wannan abu miye shi wace irin gaba ce da ba za ka iya a jitaba saboda ni " yafada daidai suna shigowa parlourn.

" Tasss kakeji ƙarar marin da Abba ya wanke Sameer da shi nunashi ya yi da yatsa kafin ya ce” wallahi ka kiyayeni saboda ka ga na kyaleka ko to ka ci gaba ka gane” . . . . . . .

Page:1️5️&1️6️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

. . . . . sosai yake mamaki miyayi zafi da har Abbanshi ya dakeshi bayan ba zai iya tuna rabun Abba ya dukeshi tun bayan rasuwar mahaifiyarshi.

Kuka yake sosai tashi ya yi ya na jan ƙafa har ya isa room ɗinshi faɗawa ya yi kan bed fillow ya rungume bai taɓa kewar mahaifiyarshi irin na yau ba magana yafara yi cikin dasheshiyar muryarshi.

" Da'ace Mama tana raye da na san yau ba za ta yi nesa daniba, Mama ina matuƙar kewarki a halin yanzu" yaka sa ƙarashe maganar domin kukan da yaci karfinshi.

Tashi ya yi ahankali ya shiga toilet wanka ya yi haɗe da ɗauro a'lwala fitowa ya yi sallaya ya shimfiɗa sallah yafara yana gamawa Ƙur'ani mai girma yaɗauka yafara karantawa ahankali yafara samun nustuwa tashi ya yi bayan ya mayar da kumai mazauninsa kwanciya ya yi ya daɗe yana saƙa da warwara kafin bacci ɓarawo ya ɗaukeshi.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

Fara buɗe idanunta dasuka mata nauyi ta yi ahankali ta tashi daga saman bed ɗin bango tafara raɓa domin kanta dake barazanar tarwatsewa toilet ta shiga wanka ta yi haɗe da ɗauro a'lwala fitowa ta yi sallaya ta shimfiɗa sallah ta yi tare da karatun littafi mai tsalki.

Tashi ta yi ta gyara ɗakinta kwanciya ta yi amma tana tunu abin da yafaru ɗazu sai kawai tafara rera sabon kuka.

Gaba ɗaya yinin yau ta yi shi ne a cikin ɗaki ku dinner bata fita ba Momy ta yi matuƙar damuwa datayiwa Dady maganar cewa ya yi ta dena damuwa za ta gaji ne tafito domin ita yunwa ba abun wasa bace.

Shima kanshi Dady kawai yana daurewa ne a zahiri amma a baɗini yafita damuwa domin shi ma kasa cin abinci yayi.

TWO DAYS LETTER

Abubuwa da dama sun faru ciki harda rufe kanta da ta yi a ɗaki ba abinci ba abin sha bata komai sai kuka gashi Dady ya kwace wayar ta balle ta samu damar ganawa da rabin ranta.

Dady ya kasa jure ganin ta cikin wannan halin hakan ya sa ya yanke hukuncin zuwa ya same ta spare key ya sa ya buɗe ƙofar zaune take lungun gado ta dukar da kanta gashin kanta duk ya hargitsi kamar wata mahaukaciya duk wanda yasan Sameeh yar'wanka yar' gayu ya ganta ba zai taɓa yarda ita bace duk wanda yaganta a irin wannan halin saiya tausaya mata, kusa da ita ya zauna rungumuta ya yi jikinshi ƙoƙarin kwacewa ta ke amma ya sa iya karfinshi ya riƙe ta magana yafara yimata cikin kwantar da murya.

" Why daughter kina kallon kanki a madubi kuwa kin ga yadda kika dawo kamar wata marar gata duk a kan wancan marar hankali kin ga ki yi hakuri ki zabi duk kasar da kike so a faɗin duniya zankaiki zan yimiki abin da kike so idan har zan daina ganinki a cikin irin wannan halin" ya ƙarashe maganar yana dubanta.

 Ɗago idanunta dasuka zurma ta yi alamara ciwo na cinta saida ya tsorata da ganin ta amma ya maze maganar ta ce tadawo da shi duniyar tunanin daya lula.

" Dady bana tunanin duk duniya akwai wanda yakaini rashin gata domin kuwa da a ce inada gata da ba zan zama haka ba ashe duk soyayyar dakake nuna min ta ƙarya ce kuma ka sani duk ƙasar daka kaini duniya ba zan iya fita daga wannan halin ba matuƙar bansamu Sameer ba ina ƙaunarshi fiye da yadda kake tunani kuma ko da a ce za ka dinga yankar naman jiki nane ba zan dena cemaka ina son Sameer ba, domin sonshi acikin jinina yake shi ne ruhina” ta ƙarashe maganar tana kallon Dady ido cikin ido.

Tassss ƙarar marin da Dady ya wanketa da shi ne ya tashi magana yafara kamar haka” ohk ashe haka ne to ki mutu kin ji kuma wannan shasha sha ba za ki sake ganinshiba " ya ƙarashe maganar yana barin ɗakin wani kukan ta sake fashewa dashi.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

Sameer duk yafita a hayyacinshi ya rame ya yi baki sosai Abba ya tada hankalinshi ganin ɗanshi ƙwalli ɗaya a wannan halin yarasa yadda zai yi.

Momy duk ta rikice ta rame kamar wata mai ciwo har su Leemah ta kira domin ganin Sameeh ta fita a wannan halin amma abin yaƙi ci yaƙi canyewa kwanansu ɗaya suka kasa zama domin yana yin Sameeh ita Feenah zazzaɓi ne ya kamata saboda halin da Sameeh take ciki dama Leemah ce mai ƙarfin hali.

Sunje sun ruƙi Dady amma ya nuna fushinsa sosai haka suka tafi.

Zazzaɓi ne ya kama Sameer wanda hakan ya sa mahaifinshi ɗaukarshi zuwa asibiti likita ya tabbatar cewa ciwon zuciya ya kama shi kuma idan har baisamu abin da yakesoba zuciyarshi tana gab da bugawa.

💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍💍

Yau tun da Momy ta tashi takejin wani sauyi ajikinta haka kawai ta tashi ta nufi ɗakin da Sameeh take tana buɗewa me za ta gani. . . .

Mu je zuwa dan ganin mai Momy za ta gani.

Page:1️7️&1️8️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

. . . . Sameeh ce kwance babu alamar numfashi a tare da ita "inalillahi wa'inna ilaihir raji'um" shi ne abin da Momy ta ke iya faɗa ke nan da ƙarfi.

Dady dake parlour da sauri ya isa gurin su Momy ɗaukan ta ya yi kamar jaririya mota ya sakata sai wani hospital private dake kusa da unguwarsu.

Dasauri aka karɓesu ɗakin gaggawa za a fara bata taimukun gaggawa ne Alhaji Muhammad yashigo rungume da Sameer kamar mattacce haɗe su sukayi room ɗaya domin sumfahimci lalurarsu iri ɗaya ce.

Ana shuga da su hannayensu ya sarƙe da na juna da sauri suka buɗe idanunsu murmushi suka sakarma juna mai tsada mai ɗauke da manufufi masu yawa daga bisani likitoci sun shirya domin fara aiki

"Likita kawai ka kiramin Abbana shi ne maganina kuda kun yimuna aiki ba zamu tashiba batare da muradin junanmuba” Sameer ya yi maganar yana tarin jini, da sauri likitan ya fita su Alhaji sunanan tsaye likitan ya sanar musu sakon su, da hanzarinsu suka shiga room ɗin, ko wannensu bakin bed ɗin yaransu suka zauna kowa ya kama hannun nashi Sameeh ce tafara magana kamar haka.

"Dady please try to understand your daughter am fell in love and ajinina son Sameer yake ba zan iya rayuwa babu Sameer ba kuda kuwa anyi min wannan aikin" ta ƙarashe maganar tana rungume hannun Dady a ƙirjinta saida Dady ya firgita domin yadda yaji heart beat ɗinta, maganar Sameer ce ta hana Dady magana.

" Abbana dan Allah ka barni da Sameerah wallahi ina sonta I can't life whitout her please ku ubangiji yana son mu ka sance tare and why ku saboda wani abu da bai taka kara ya karyaba please” yakarashe maganar yana fitar da jini a bakinshi.

Likitan dake tsaye wurin ne ya zo har wurin su Abba dafa kafaɗarshi ya yi kafin ya ce” haba wannan wani irin rayuwa ce sabida wani abun duniya kuna ganin ya'yan ku cikin irin wannan halin amma kukasa taimaka musu haba wace irin zuciya ce daku" yakarashe maganar yana dubansu.

"Dady gaba ɗaya jikinshi ya yi sanyi da ganin yana yin yar'shi ƙwalli ɗaya a duniya a wannan halin, Momy ce ta shigo a firgice kuka take yi ba ji ba gani rungumeta Dady ya yi ahankali ya fara magana " shiiiiii calm down please kikama kanki " haba Alhaji kana ganin halin da yarinyata take ciki sannan ka kalli cikin idona kacemin I should calm down" ahankali ya raba jikinshi da nata wurin Alhaji Muhammad yanufa.

"Assalamu alaikum" ya faɗa kawad dakai Abba ya yi bai damuba yaci gaba da magana” as a Muslim ya kamata ka amsamin sallama any where am here to scarify my everything to my daughter, ni Alhaji Abubakar Daula na zubar da makaman yaƙi ina son ka ba ni dama na nemi auren ɗan ka” rungumeshi ya yi kafin yafara magana ahankali” kayi haƙuri aminina kayi haƙuri ni Alhaji Muhammad canji a yau basai gobe ba zan ɗaura auren SAMEER DA SAMEERAH" afurgice suka Mike tsaye kamar basune a halin mutuwa ko rayuwa ba duk abun ya ba su mamaki hatta likitan dariya kawai sukayi tare da girgiza kai.

"A'a to kubari ayi aikin mana " cewar likitn Yan kallonsu " a'a ranaka ya daɗe ai mun warke " suka faɗa a tare dariya suka sa su dukkansu fita sukayi domin kumawa gida gidansu Sameer suka wuce kuda sukaje masu aiki sun yi girki na alfarma suna zuwa zama sukayi lemo da ruwa suka sha tashi sukayi masallaci suka tafi annanne dunbin al'umma suka shaida daurin Auren SAMEER Da SAMEERAH a kan sadaki naira dubu ɗari lakadan ba ajalan ba. . . . .

Idan kun ji daɗinsa to in ga ruwan comments. 💍

Comments and Share fisabilillah💍

Taku har kullum

(Rukee Sauwa)

For WhatsApp and Call, contact me at💍

07030446917💍

Page:1️9️&2️0️

Bismillahir Rahmanir Rahim.

One Month letter.

. . . . . Abubuwa da dama sunfaru ciki harda tarewar su SAMEER DA SAMEERAH zama suke na so da ƙaunar juna kuma suna ci gaba da zuwa makaranta daya ke dama suna last year ne kuma second semester hakan ya sa yanzu suka kammala karatunsu Sameerah ta samu ciki sosai take samun kolawa daga kowane ɓangare yayinda Abba da Dady suka ci gaba da aminintakarsu dama muna furcin secretary Dady ne koma yanzu komai yazama normal Dady yaso ya hukunta secretary amma Abba ya hanashi ya ce ya je can da halinshi.

Ɓangaren su Leemah kuwa duk sunsamu mazajen aure masu abin hannu sun yi aurensu cikin kwanciyar hankali da soyayyar juna.

8 Month letter

Zaune take saman one sitter da katon cikinta Wanda ya yi kasa sosai ahankali tafara ciccize lebbenta amma Ina taka sa jurewa kuwa ta buga tare da fara ambatun sunan Allah, Sameer ne yafito da sauri daukanta ya yi duk da nauyinta mota yasata sai hospital dasuri aka turu gadon tura mara lafiya aka shiga da ita labour room waje likita ya tsayar da shi kiransu Dady ya yi ya sanar musu ba jimawa asibiti ta cika da Yan uwa da abokanan arziki ta jima bata haihuba har ana cuku cukun yimata CS da ikon Allah ta haifi yarinyarta kyakyawa babba domin kuwa ya ganta yasan tana cikin koshin lafiya murna wurin iyalai biyu ba’a magana.

Ranar likita ya ba su sallama domin saidai mu ce Alhamdulilla Mai jigo lafiyarta ƙalau ranar suna mai jego da yarta sunsha kyau cikin kaya na alfarma Sameer saida ya nemi shawarar Sameeh kan sunan da za a sama yarinyar amma sai ta ce ya sa sunan mahaifiyarshi yaji daɗin sosai yarinya ta ci suna Amina ana kiranta da Mami haka suka ci gaba da zama cikin so da ƙaunar juna.

A NAN NAKE CEWA ALHAMDULILLAH TAMMAT BI HAMDALLAH ALHAMDULILLAH.

Taku har kullum

Rukee Sauwa
07030446917
A kullum ina so ku sani cewa
✍️Alƙalami ya fi takubi🗡️
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m. facebook. com/story. php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo   

 
Soyayya

Post a Comment

0 Comments