Ticker

6/recent/ticker-posts

Sababben Lokaci

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

304. Sababben lokaci idan mun gane shi,

 Shi kullum ake ta famar aikin shi,

 Yau a yi, gobe ma ana yi tsarin shi,

Kowane al’amar idan an saba shi,

  Za ka ga ya zamo jikin mai sabawa.

 

305. Kalmomin da ke da sigar sabawa,

Mun ji akwai su, harshen Hausawa,

Su ke nuna ayyukan duk da ka yowa,

 Lura da su idan ka zo gun zanawa,

  Ba a raba su don ka zan mai ganewa.

 

306. Ka ga akan, nikan, mukan, ga bayaninsu,

 Ba a rubuta ‘a’ daban ‘kan’ a raba su,

 A mukan ma a duba dukkan tsarinsu,

 A bi doka a harhaɗa su ga zana su,

Su da sukan, takan, yakan, bai dainawa.

 

307. Makarantun Kano akan hana yin wasa,

Ɗalibban Gusau sukan shiryo gasa,

A gidan ƙwallo mu mukan hana sa – in – sa,

Duk mai kamfani yakan buɗe ressa,

  A gidana nikan ci doyar soyawa.

 

308. Ranar Laraba akan yo muna gumba,

 Sai mu aje ta Alhamis nan muka tarba,

 Kowace kasuwa sukan yi mana zamba,

‘Yan banga mukan haya kowace Larba,

  In suka zo sukan yi aiki da cikawa.

 

309. Ladidi takan yi waina da maraice,

 Yaran zamanin ga nan sun lalace,

 Kullum sukan taho don su yi zance,

 Gun rancen kuɗi kamar dai su yi ƙwace,

Mai shara’a yakan hana masu walawa.

 

310. Kalmomin da mun ka sa in ka fahimce,

 An saba da aika aiki ya kasance,

 Dudduba da kyau ya zan ka daidaice,

 Ayukan duk da an ka yo je tantance,

  Su ne lokacin da ke ƙin cinyewa.

 

311. Kowane lokaci a tare ake sa su,

 A rubutu ka zan kula ba a raba su,

 A haɗe kar a saɓa dokar nahawunsu,

 Zanka kula da ƙa’ida sai ka haɗe su,

  Ba a raba su don ka zan mai sabawa.

 

312. To dai mun ga wagga doka a taƙaice,

 Ita ce malumanmu duk sun ka amince,

 Ba su da ja a kan hakan sun lamunce,

In ka raba su sai bayanin ya sihirce,

  Ko bokan garinku bai iya ganewa.

 

313. Kai kuma ɗalibi bayanan ga riƙe su,

 A rubutunka ko’ina zan ka kula su,

 Kai kuma malami ka duba ka biya su,

In ka kula ka gane tsarin nahawunsu,

  Ba wahala idan ka zo gun koyarwa.

Post a Comment

0 Comments