Ina ƙoƙarin ƙarasa ajin su Rumaisa da mu mun gama Exam ta ƙualifying da muka zana chemistry ranar, zan je na faɗa mata saƙon da Mama ta ba ni na kaimata da Rumaisa ta rigani ta howa a yau
Malam Hamid na hango jikin
birandar ajinsu Rumaisa da waya kunnensa da alama waya ya fito amsawa daga
cikin Library ɗin da
ya ka sance gurin zamansa dako kiransa za ayi aji a nan ake samunsa, a yadda na
fahimci Malam Hamid bai fiye son hayaniya ba duba da yadda ko yana koyarmana yake
yi
Ban san ya hango ni ba shi ma da
ina ƙarasowa
inda yake tun kafin na gaishesa ya faramin magana da yake ƙoƙarin
cire wayar kunnensa
"Sumayyah"
Na amsa da
"Na'am Malam ina yini”
Ya dube ni
"Lafiya lau, ina za ki haka”
Nace
"Gurin ƙanwata”
Malam Hamid mutum ne mai son ɗalibansa musamman indai
kana gane subject din da yake koyarwa hakan ya sa muke mutunci sosai dan nidai
inason physics sosai maganarsa ta katse min tunanina don ban yi ƙoƙarin
tafiya ba har lokacin da ban san dalili ba
"Kin dai hanani number ɗinki, kawayenki duk sun ba
ni gashi saura kwanaki ya rage nabar Kano"
Kallonsa na yi don indai ban
manta ba a ƙarshen
shekararmu Ss1 ya zo makarantarmu kuma gashi yanzu muna Ss2 karshen shekara
"Kina ta kallona ba za ki ba
ni ba ko, to kimin kwatancen gidanku na zo"maganarsa ta katse min tunanina
na kuma sauke kaina daga kansa
"Ba hanaka na yi ba Malam ba
nida waya ne, batun gidanmu kuma. . "
Ban ƙarasa zancen ba ya yi magana
"Ba a bari irina ya zo
ko?"
Murmushi na yi Jin kalamansa ta
don ta ina talaka kamarni za a ce saika zaɓi
wanda zaizo gidanku ba tare da kana da dalili Mai karfi ba, duk da bawai na san
rayuwar Malam Hamid ba amma inada yaƙinin rayuwarsa tafi tamu inganci
"A'a Malam kawai dai na ga
ba’a Kano kakeba ba lallai ka gane kwatance naba”
Ya ɗan
zaro ido
"Waya faɗa miki, ni ɗan kanone ina gidan
kakanninane a Katsina”
Na dubesa alamun na tabbatar ɗinnan
Kai ya ɗagamin alamun eh ya ce
"Anan ma unguwar Gandun
Albasa Babana yana da gida amma gidan wani abokin Babana nake zaune tun da na
zo shi a can Nasarawa GRA gidansa yake, kin ga ko ni ɗan gari ne”
Na dubesa nace
"Haka ne amma dai yanzu mune
'yan gari”
Ya harareni
"Bayan na ji ance zuwa kuka
yi ko daga ina kike gwarzo ko gwarzaye ne namanta Halima ce dai ta faɗamin"
Nayi murmushi
"Gwarzo ne”
"Ok yanzu ba za ki ba ni number
ɗinba kota Mamace” na
dubesa
"Mama ba tada waya saidai ta
Baba”
Yace
"A'a barta ma rinƙa
gaisawa a wayar Halima”
Na ɗaga
kai alamar eh ba wai dan na gaji da hira da Malam Hamid ba mu kayi sallama, ban
san daliliba bana taɓa
gajiya da hirarsa duk lokacin da muka haɗu
haka harso nake period ɗinsa
ta shigo jinina da Malam Hamid sai na ce ya haɗu
ka sancewar Malam Hamid ya iya tsara zance, dalilin da ya sa ba ko yaushe
nakeson haɗuwata da
shi ba musamman ba tare da su Halima ba fassarar ɗalibai
tuni a fassara maganar da muke a cewa muna soyayya ne da malamai sun yi dokar
hakan a makaranta ko malami saurayin ka ne
to ku bari ki fita can waje ku yi firarku idan ya zo gidan ku, ajinsu Rumaisa
na ƙarasa
na faɗa mata saƙon na
fito da na yi sa'a na tarar ba malami
Batul da ta gama kufula na tarar
da ita inda na barta da shaf na manta da batun wata Batul da na ce ta zo muje
ta rakani faɗawa
Rumaisa saƙo
taƙi
ta ce min dai bari ta jirani a nan na dawo mu tafi ka sancewar tare muke tafiya
da muna karasawa layin gidanmu take tsayawa ta samu napep hakurin da nakeso na
bata ta katse zancena
"Kin ga ba abun da za ki
cemin taho kawai mu tafi "
Bayanta na bi da ita har ta yi gaba
ina sauri har na ƙarasa gurinta muka ci gaba da tafiya da shiru ya ratsa tsakaninmu
"Yi hakuri mana ƙawata”
Batul ta dube ni da hararata
"Ba wani haƙuri
kina can kin samu Malam Hamid, ban ma san wacce tattaunawar kuke ba”
Na kalleta
"Wai dama kina hango
mu"
Ta ɗaga
kai
"Eh man da na yi niyyar zuwa
to saina hango ana kallon love shi ne naki zuwa”
Wata muguwar harara na gallawa
Batul
"Banasan wulaƙanci
Batul, wanne irin kallon love”
Dariya tayi
"Nufinki ba musan komai ba, nifa
na san danke Malam Hamid ke kirana waya, tun da kullum in yana kirani tambayarki
kawai yake”
Na ɗan
ja tsaki
"Wannan matsalarkice ni
soyayya ma bata dame ni ba, bare kuma har na yi da malaminmu"
"Kanki ake ji mudai 'yan kai
amarya ne Katsina dama ban taɓa
zuwa ba” faɗin Batul
tana dariyar shaƙiyanci da na san halin Batul ba ma ka mata komai ba tana zolayarka
bare na ɓatamata rai
amma baisa na ƙi tankamata ba
na sake haɗe fuska
"Batul ban san irin wannan, ke
kanki kin san tsarin mijin da nakeso Malam Hamid bai kala da su ba kuma ma kin
san bana sha'awa soyayya da malami nasha faɗamiki
ina gudun kar wasu su ji su Kama”
"To sai me dan sunji aibu ne
hakan, ko harammunne kika aikata, kuma batun kala aike ma kin san Malam Hamid
komai ajin budurwa ba zatace ta girmi Hamid a wanda za ta so ba” ta karasa
zancen tana gyara littafan dake rungume hannunta
Cikin ɓacin rai
"To ke mai zai hana ki sosa”
Ta sa dariya
"Ai dan ba ni ya nuna yana
so ba”
Shirun da taji na mata yasata
sassauta murya
"Gaskiya Sumayyah wannan ba
tsari ba ne ban san kalar mijin da za ki ce ya yi miki ba, Yaya Hakeem da yake
tamkar yayanmu shi ma kin nuna bai miki ba da ya nuna yana sanki, haba Habiba ban
san wanne kalar miji kike son aure ba, tun da kinada tabbacin ba ci gaba za ki
yi da karatu ba ya kamata ki aje komai ki zaɓi
miji ki yi aure tun da kina samun maneman, sai dai kuma ban sani ba ko mai kuɗi kike jira”
Batul na kalla da ba dai abin
haushi ba ana fara magana tiryen tiryen za ta bauɗe
"Batul bana tunanin Malam
Hamid da Yaya Hakeem tafiyarmu za ta daidaita ba dan na san asalin Hamid ba
amma na san na Yaya Hakeem, kuma kema sanin kanki ne ban taɓa tsammanin zan samu dacen
auren mai kuɗinba, amma
darajata nakeso bayan aurena”
Batul ce taja ta tsaya da ni ma
banida zaɓi ban da tsayawar
"Wacce daraja ce da idan
baki tunanin za ki samu gurin Malam Hamid ba kike tunanin ba za ki samu gurin
Yaya Hakeem yayan Halimanki da kowa ya shaida kaunar da take miki da ita da
nata iyayen dama duka 'yan uwanta, da kowa ma shaidane kedai kawai ki ce baki
son Yaya Hakeem ɗin"
Nayi murmushi dan gaskiyane Batul
ta faɗa kawai bana
sha'awar auren Yaya Hakeem da ko Batul bata san daliliba bayan Halima da ita ce
ta yi ƙoƙarin haɗa ni da Yaya Hakeem kawai
don ta nuna soyayyarta gare ni, duk da ƙawance tunna yarinta har zuwa yanzu ya haɗa Halima da Firdausi
budurwar Yaya Hakeem da suke son junansu amma ta yi ƙoƙarin canza akalar
soyayyarsu take ƙoƙarin azata akaina, shi ma Yaya Hakeem don ya farantawa Halima
yake ƙoƙarin
biye mata, da a kan hakan muka fara ƙoƙarin kai ruwa rana da Halima da har yanzu
ba mu dawo daidai ba, don na faɗawa
Halima ba za a haɗa
baki dani gurin cin amanar Firdausi ba da take ni ma ƙawa gareni saboda dalilin
Halima na daban na san kawoni cikin danginsu. . .
Maganar Batul ta katse min
tunanin da nake
"Shike nan tun da kinƙi don
Allah ki amince da Malam Hamid yanzu"
Nayi tsaki na ci gaba da tafiya
Batul ba dai matsala ba sam bata gane karatun kurma, kamar na faɗa mata aurenne a gaba na
kome ma oho toma auren ma ai daidai ruwa daidai ƙurji dan ko da gani ma ido ba mudu ba
yasan kima ina zan haɗa
kaina da Malam Hamid duk da ban san asalinshi ba na lura dalilin hakan, ina jin
kiran da Batul keyi min na shareta na ci gaba da tafiya cikin sauri harna ƙarasa
layin gidanmu na shige kwanar gidan namu.
**** ****
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.