Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 5)

Waya baba ya miƙomin da nake zaune ina wanke wanke a tsakar gidanmu karɓa na yi da ina duba wa na ga alamun an Kira wayarne ina ƙoƙarin tambaya waye Baban ya ce

"Kiyi magana ɗan uwanki ne Samir, ki kawon wayar idan kin gama ɗaki”

Nayi murmushi da na ƙaƙarosa don tuni na gano wannan Samir ɗin ne mai tambayarnan na ce ma Abba

"To"

Nayi 'ƙoƙarin kara wayar a kunnena

" ƙanwata ya kike”

Maganarsa ta katse tunanina na maida hankalina ga wayar

Ban basa amsa ba na canza zancen

"Yaya Samir ina yini”

"Lafiya lau yasu Mama” hakan da ya faɗa na ayyana a raina Allah ya sa kar tambayar ta zarce

"Lafiya lau ya kowa da kowa”

Yace min

"Alhamdulillah"daganan shirun 'yan sakanni ya rasa tsakaninmu Samir ya yi 'ƙoƙarin sauke numfashi

"Hala tsoron mutane kike ko?"

Na tsaro ido kamar yana ganina

"Ni ɗin kuma?"

"Eh mana ina kallon yanayinki wancen karan saboda tsoro haka kika tafi ba mu gama gaisawa ba”

Nayi murmushi kamar yana ganina

"Kai Yaya Samir ban da gaisawar da mukayi

"Ina wata gaisawa bayan tambayata tasa kin gudu"

Nayi dariya na ce

"Waya faɗama saboda tambayarka na gudu"

"Saboda na san hakanne, dan haka nake duk inda naje don duk na fara manta mutane tun da na dawo daga karatu kin san ba a nan ƙasar na yi ba, ko 'yan Gwarzo saida suka yi zancen tambayartawa, to bare ke da mukayi nesa da juna, yaushe za ki zo Katsina?"ya ƙarasa maganar yana tambayata

"Babu rana”

"Ah haba dai idan kun gama ƙualifying zan zo na tafi dake?"jim na yi jin abin da Yaya Samir ya faɗa sai da ya sake magana

"Ko bakya son kizo gidanmu, bayan kuma yanzu muka gama magana da Abba ya ce min saina zo"

Bani da zaɓi jin Abba ya amince sama da ni ma na amince

"To shike nan Allah ya kaimu lafiya”

Yace

"Amin amma yaushe za ku gama ƙualifying ɗin"

Kamar ba zan basa amsaba

"On 20"

"Ok zan zo On 25 sannan kin shirya komai ko?"

Shiru na yi Masa

"Shike nan tun da ba za ki magana ba na lura har yau baki gama sabawa dani ba” ban basa amsa ba

"Sai anjima” kawai na faɗa na katse wayar na kaiwa Abba wayarsa na dawo na ci gaba da wanke wanke na a raina ina tunanin ko wanne zama zan yi gidan Baban Katsina muna nesa da juna ba su taimaka mana bare kuma naje inda suke na ɗora musu nauyi, inada yaƙinin Baban Katsina bai san da zancen zuwana ba kawai Yaya Samir ya shirya zancen zuwan nawa, amma dai a yadda na san babu mai sonmu a dangin Abba babu wanda zai buƙaci muje inda yake haka nan ba tare da wani daliliba da ni ma na san dalilin Yaya Samir da na fahimci yanasan zumun ci zanje haka na karasa aikin da nake jikina a sanyaye ɗakinmu kawai na shige na kwanta ina tuno wayata da Yaya Samir ban san dalili ba tun bayan gama wayarmu na ji hankalina bai kwanta da zuwana Katsinan ba

Sallamar Halima ta katse min tunanin da nake yi da sai yanzu na san ta zo gidannamu amsa mata, na yi gefen tabarmar da nake kwance ta zauna tare da cewa

"Hala dai lafiyarki ƙalau kizo kika kwanta haka ke kaɗai”

Nayi murmushi

"Bakomai, na yi aikine na gaji”

Hararata ta yi tace

"Wanne irin gajiya, yanzu Mama ta faɗamin kika shiga ɗaki bayan kin gama wanke wanke, dan Allah ki faɗamin damuwarki”

Na ɗan ja numfashi Halima ba ƙawar da za a ɓoyewa wani abu bace don tafi ƙarfin a kirata ko da aminiya saidai 'yar uwa na dubeta na fara magana

"Halima ɗazu Yaya Samir ɗan Baban Katsina yayan Abba ya kirani waya a wayar Abba a kan cewa mana gama ƙualifying zaizo ya ɗaukeni mu tafi Katsina, shi ne hankalina ya kasa kwanciya”

Halima ta zaro ido tace

"Katsina fa nidai bana yi miki sha'awar zuwa dacen da kuke ƙananu waya taɓa tunanin ya ɗauki wata cikinku sai yanzu da kuka fara girma, dama zaman bauta kaɗai za ki yi da sauki amma wulakancin da zai rika biyo baya nake gudarmiki da za a riƙa shimfida miki, shi Yaya Samir ɗinma akanme zai tunanin hakan"

Na girgiza kai nace

"Wallahi ban saniba Halima amma shi bai san duk abin da ke faruwa ba, ta yiyuma Baban Katsinan bai san abunda Yaya Samir ɗin ya yi ba”

Halima ta ɗaga kai tace

"Eh haka ne amma dai Mama ya kamata ta yi magana a kan ba za ki ba”

Na dubi Halima nace

"Halima Mama fa ta yi magana kika ce to ai tanayi abun zai zama abun magana, dama ita da hakannan ma ba tsira ta yi ba a gurinsu, Kuma Abba fa ya amince”

Tsaki Halima ta yi daga bisani tace

"Allah ya kyauta zance kawai don nidai na san ba wani farin ciki za ki acanba dan da zaman da za ki yi acan wallahi gwara na nan ko ba kullum za ku ci ba”

Da haka muka ci gaba da fira da Halima da muna cikin firar wayar ta yi ƙara da wayar duk da keypad ce ta ba ni sha'awa saboda ni ko kamarta ba ni da ita da ita ma yayanta Yaya Baffa ya bata tsohuwar tashi daya canza sabuwa duba wayar ta kalle ni ta yi murmushi tana 'ƙoƙarin ɗagawa ta ce min "Malam Hamid ne ɗazu ma ya kirani waya, yana tambayata naje gidanku na ce masa a'a zanzo dai anjima shi ne kin ga yanzu ya sake kirana”

Daganan ta ɗaga wayar Sallamar da ta yi a wayar na ji daganan na ji ta ce "to" ta miƙomin wayar

Na karɓa kawai na kara kunne ba tare da na ce komai ba Malam Hamid na ji yafara magana cikin muryar da ban ma san ya iya irinta ba tun da bantaɓa ji ya yi ba kamar mai jin barci ya ce

"Sumayyahty babu magana”

Jin sunan na yi banbarakwai nanma dan nasa ba da Sumayyahty yake faɗamin shiru na yi don ban san amsar da zan bashi ba, shirun da yaji na yi ya ci gaba da cewa

"Nayi laifine”

Kaina girgiza kamar yana ganina na ce

"A'a”

Ya ɗan marairaice murya

"To mai na yi”

"Ka canza” kawai na iya faɗa

"Dame kuma” ya ba ni amsa

Nace” da komai”

Ya ɗanyi 'yar dariya da na ji sautinta a waya ya ce

"Kin ba ni dama na sanardake dalilin canzawartawa”

Nace masa” Eh"

Sai kawai na ji ya ce

"To kece sila”

Zaro ido na yi kamar yana ganina tare da cewa

"Ni kuma saboda wanne dalili Malam"

"Dalilin inasanki, tun farkon ganina dake Sumayyah na ji hakan da a yanzu nafi tunanin lokacin sanarmiki yayi. . . . "

Ba tare da na ƙarasa jin mai zai faɗa ba na katse wayar hawaye suna wanke min fuskata da ban san da taruwarsuba saidai zubarsu kawai

Halima ta dube ni bayan miƙa mata wayar da na yi da duk abin da nake faɗa tana ji

"Lafiya Sumayyah mai ya faɗamiki Malam Hamid din"

Hawaye na na ci gaba da zubarwa na dubeta

"Halima so na ya ce yanayi, ba zan iya haɗa rayuwata da mutum kamar Malam Hamid ba”

Kallona ta yi cikin nuna danuwa

"To saboda ance ana sonki kike hawaye, to sai dawa za ki iya soyayyar, gaskiya Sumayyah ki tsaya ki nutsu kima kanki faɗa haba, dan ance ana sonka ba'abun gwama numfashi ba ne, so dai game hankali ga wanda ya nuna yana sanshi ai shi akeso, babu alaƙa tsakaninmu amma buri na ki yi aure”

Na girgiza kai

"Eh na sani amma Halima ke kanki kin san kina kallon Hamid kin san rayuwarsa tafi tawa koma da ya ne, ni Kuma na fison auren wanda rayuwarmu ta yi dai dai da juna”

Tsaki Halima tayi

"Wannan ba hujja bace kwata kwata, kuma banga aibun Malam Hamid, bare kuma na ga wani alamu na da zai nuna Malam Hamid yafiki ba, ki tsaya ki nutsu ki fahimci hakan dai tukun"

Murmushi na yi da ba ni da zaɓi da ya wuce yadda amma dai ni haka zuciyata tafi tunani ni kuma nafison auren wanda rayuwarmu ta yi dai dai da juna

"Shike nan na amince to"

Dariya ta yi

"To ai ba ni za ki faɗawa ba, kuma baki shawara da zuciyarki ba ta ina za ki amince masa”

Nima dariya na yi nace

"Aike radiyonsace, kuma kamar zuciyace ke a gurina, ke kin mafi zuciya saboda zuciya ba lallai duk abin da ta tsakani na aiwatar ya zama daidai ba, amma ke zuciyace mara sirki da duk wani abun da zai jawo aikata da na sani, dan haka shawararki ita ce abar ɗauka, danko Mama ita ma na san hakan za ta fadamin"

Murmushi tayi

"Wato kin janye min ko?"

Nayi dariya

"Ai dole a janye wa ƙawar kwarai da kowa ke fatan samu a rayuwarsa, ke na faɗamiki ko aminiya na faɗamiki sunan baidace da keba”

Kai Halima ta girgiza

"Sumayyah banison yabofa, komai na yi miki cancantarki ce hakan"

Na dubeta

"Cancanta fa kika ce”

Ta ɗagamin kai

"Kwarai kuwa, Sumayyah kinada halin da kowa zaiso zama dake, ya kuma ƙarar da komai gurin don son zama dake, kina da juriya, tare da sanin darajar wanda duk kike tare dashi”

Dariya na yi

"Idan harna ka sance hakan to kece sanadiyyar zamo wata haka, Halima da a ce zan rubuta littafi akanki littafi ɗaya ya yi kaɗan gurin bayyanarwa da jama'a halayyarki, halinki ya girmema kyawunki da shekarunki, kin tallafamin a lokacin da kowa ya nuna bayason mu hatta a dangi kin yi tarayya dani bisa tsantsar ƙauna da gani har zuriyyata kuma kin zauna dani bayan kin fahimci mu talakawane da kullum suke neman abinci yau da gobe, kikan iya ƙin ci ki ba ni ni naci, duk abin da kike da shi nawane ni dake, Halima ban san ta ina zan biya ki ba”

Murmushi tayi

" Ai Sumayyah ƙawa ta gari ba dubawarta abin da kika mallaka ba ne dubawarta cancantarki ya ɗabi'unki suke kyawawane ko kuwa, shin kina umarni da kyakkyawa ko kuwa, kuma yaya soyayyarki da duniya take, kina tuna Allah a dukkan lamuranki, ni a nawa tunanin sune abin dubawa bawai arziƙi ba domin su ababene masu ƙarewa, a lokacin da akace ba zaka yi ƙawance da wadda ka fita wani abu a duniya ba to ta ina za ka fahimci ta inane za ka tallafi rayuwar wasu kuma idan kace sai da waɗanda suka fika zaka yi mu'amala ta ina za ka san kanada wani matsayi a gurin wasu, idan ba ka mu'amala da waɗanda kafi su wani abu ba ba ma za ka fahimci Allah ya yi ma baiwar da wasu ba su samu irinta ba kullum tunaninka yadda zaka yi kakai gurin da waɗanda suka fikan suka kai shike nan sai ka fara rashin godiyar Allah ni a ganina kayi Mu'amala da kowa ta yadda tsoron Allahnka zai riƙa ƙaruwa malam mai ahalari yana cewa idan za ka so mutum ka soshi domin Allah, kuma dukkan musulmine ai ɗan uwan musulmine”

Na jinjina kai alamun gamsuwa

"Amma Halima 'yan uwana sun kasa fahimtar abin da ke ɗin kika fahimta”

Kafaɗata ta dafa

"Yi hakuri Sumayyah za su fahimtane wata rana, domin talaka da a ce an tanbayesa Yaya yakeso ya rayu a duniya da ba zaice yanaso ya yi rayuwa cikin talauci ba, kuma arziƙi nufin Allah ne idan zagayenka ya zo za ka iya samu idan Allah ya ƙaddara za ka samu, shi ya sa kullum addu'ar da ya kamata mu riƙayi idan Allah baisa za mu samu shiga wata ni'imaba a duniya Allah ya ba mu dacewa ta shiga cikin ni'imar aljannah, a wannan duniyar idan akace talaka bai kyautata bautarsa ga ubangiji ba bana tunanin zai samu hakan"

Jinjina kai kawai na yi alamun ina gamsuwa da maganganun Halima.

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604

Na Cancanta 

Post a Comment

0 Comments