Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 3)

Koda na dawo gida saida na labartama Mama duk irin abin da ya faru da kawai ni tabawa hakuri tare da nuna min yadda nake tunanin halayyar wasu daga cikin 'yan adam tafi irin yadda Aunty Asma'u ta nuna min tata halayyar

A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya garemu har Ahmad kanina yasamu adaidaita sahu ta haya da akwanakin baya ya wani makwabcinmu Alhaji Yassar Makama da yake raba adaidaita sahu ya zo garin da ba zaman Kanon yake ba yana Abuja da zama nan ya rabawa matasan layinmu adaidaita sahun da Allah ya yi da rabon Ahmad wanda kana gama biyan kuɗin adaidaita za ta zama taka, bawai dan Ahmad yakai shekarun da zai iya tuƙa ba, sai dai na ce Allah ne ya sa zai samu ɗin Alhaji Yassar yana da alkhairi sosai dan Tahfiz din da muke zuwa shiya ginata mallakinsa ce kuma a kyauta muke zuwa danasan ban da hakan karatun addinima gagararmu zai yi, sai gashi Allah ya dubemu a lokacin ginata mu da muke makwabtansa a kyauta muke islamiyyar da kullum na yi sallah nakan masa addu'a da fatan alkhairi duk da ban taɓa ganinshi ba amma tarun alkhairinsa ya sani hakan, nakan ji a raina inama duk wani mai kuɗi ya zama kamar Alhaji Yassar ɗin, inada burin na ganshi fuska da fuska duk da ba zan iya sakamasa da abunda ya yi mana ba amma dai zan ji daɗi a ce na san mutumin da yake mana alkhairi, da danginmu suka kasa yi mana a dalilin Alhaji Yassar na yarda ashe akwai masu kuɗin da ba su ƙyamar talaka

Ahmad yana samo adaidaita sahun da duk muka cika da murna da sai washe garin ranar za su je su anso a kamfani da za a haɗa musu ita gefen Mama ya zauna yana ba mu labari da muka shimfida tabarma tsakar gida na dubi Ahmad ɗin

"Wai niko Ahmad ka ga Alhaji Yassar Makaman"

Ya kalle ni kallon baki da wayau ɗinnan

"Wannan mutumin kike tsammanin za a gani, ai ganin sa saikin cike Form Yaya”

Nima dubensa na ƙarayi

"Allah ya kyauta saboda kallon ɗan adam kamarni na tsaya cike form"

Mama sai yanzu tasa baki ta dube ni

" ɗan adam ne Sumayyah amma dai Allah ya bashi matsayin da bai ba mu ba, kin ga shi ya sa saikama cike form ɗin ba lallai ka gansa ba” .

Na jinjina kai dan gaskiya Mama ta faɗa dan waɗanda ba su taka ƙafar arzikin Alhaji Yassar ɗinba suke wuyar gani bare kuma wannan mutumin da nidai har tsayawa nake Iina yarinya kallon irin tsarin ginin gidansa, saida na girma na saba da kallon gidan na daina”

Maganar Ahmad ta katse min tunanina

"Ki barta Mama gani take wasa ne, managernsa ma kwananmu biyu muna zuwa sai ana biyu muka ganshi bare kuma shi, da cewa ma aka yi ranar da ya zo garin ya koma a jirgi an kirasa Abuja kiran gaggawa, ai irin waɗannan saidai ka gansu a hoto, dan ko da sunso suga talakawa ba lallai su samu lokaci ba, shi mafa mai kuɗin bafa a hutu yake ba”

Mama tace

"Haka ne Ahmad, fatanmu dai a kullum Allah ya ba mu arziƙi mai albarka dan tarin dukiyar nanma ba wani abu ba ne, wani lokacinma ita ke halakar da kai”

Muka jinjina kai alamun gamsuwa da maganar da Mama tayi,

Na dubi Mama

"Amma dai irin waɗannan masu kuɗin Mama zako a samesu da wata damuwa a ransu"danni tunanina a kullum yakan ba ni damuwa ta talakawace irinmu

Maganar Mama ta katse min tunanina

"Sumayyah ke nan ai ba wanda baida damuwa, saidai ta wasu ta ɗararma ta wasu, akwai wanda damuwarsa kuɗinsa ba za su magance masa damuwar dake damun sabama, kawai dai mu cika zuciyarmu da godiyar Allah"

Mu duka muka kalli Mama muka ce

"Alhamdulillah" haka muka ci gaba da firarmu.

Ahmad da yake aji uku a secondary hakan ya sa Abbanmu ya daina zuwa kasuwa ya koma jan adaidaita sahu ka'in da na'in dan dama zuwa kasuwar anayine kawai ba dan ana samun wani abuba.

A lokacin abubuwa suka fara sauyawa a rayuwarmu a lokacin na shiga aji biyar a secondary muna ƙoƙarin zana jarabawar Qualifying a lokacin Mama ta haifi 'yarta mace da aka sa mata suna Aisha muna ce mata Humaira da sunan ya ka sance na Mamarsu Abbanmu.

Ka sancewar haihuwar Maman da sallah ne hakan ya sa 'yan uwan Abbanmu suka zazzo harma waɗanda ba Gwarzo suke da zama ba dalilin zuwan sallar da suke, da muma a baya muna zuwan saboda ƙananun maganganu ya sa tun ina primary rabonmu da zuwa da ƙaramar sallar saidai Abba ya je, mu kuma da Babba muje mu da Mamanmu.

Tun ana gobe suna ƙannen Mama su biyu Aunty Jamila da Aunty Asiya da yaransu da kowacce ta zo da wanda suka take goyo suka fara zuwa dan ma gidan namu baida girma hakan ya sa biyu ne suka zo a 'yan uwan Mama, da indai hidimar Mama ta tashi suna yi mata Kara hakan ya sa ba laifi inason 'yan uwan Mama da rashin wadata ya sa na san basuyi mana abubuwa, amma duk da hakan da Mama ta haihu sunzo mata da kaya da yawa da wanda za ta yi fitar suna da na girkawa

Ranar suna dangin Abba da Mama sun haɗu da dangin Abba ba yabo ba fallasa suke amsa gaisuwar da muke musu ƙawata Halima da ta zo tun safe muka shiga ɗaki da ita da sai ƙarfe biyu muka fara ƙoƙarin yin wanka bayan an gama aike aikenmu da harda Haliman ake aiken namu.

Baban Katsina da ya zo da matarsa da 'ya'yansa da tun ina yarinya rabon da na gansa sai dai sunansa da muke ji a gwarzo shi Abba ya zo ya kiramu mu gaisa da ko minti biyar basuyi ba a gidanmu suka fito za su tafi damu lokacin muna ɗakinmu muna shirin fitar suna nida ƙannena haka muka biyo bayan Abba har zuwa waje inda Baban Katsinan ya yi parking ɗin motarsa haka nan na ji bana so na gansa saboda tunowa da na yi a dangin Abba ba wani wanda muke da matsayi a gurinsa ga wannan kuma da duk ya fisu kuɗi dan ina ji ana maganar irin kuɗinsa a Gwarzo idan mun je hakan ya sa na ji zullumin ganinshi domin na san ba za mu samu wani kallon arziƙi a gurinsa saboda na san yadda masu kuɗi suka ƙi jinin su ga talaka, da wannan tunanin muka ƙarasa inda motar tasu take Abba ya yi sallama Baban Katsinan da ƙafarshi take waje daga cikin motar ya fito da ƙansa ya kalli Abba yana amsa sallamar, ina ganin Baban Katsinan na gane shi dan ko da ban sanshi ba yana kama da Abba sosai zan iya ganesa

Gaishesa mu kayi ya amsa fuskarsa ba yabo ba fallasa matarsa da take bayan motar ta leƙo muka gaisa da ita ma na ganeta 'ya'yansa ma duk mun gaisa da wanda yake jan motarsa da nafi tsammanin ɗansa ne duk da ba wata kama yake da Baban Katsinan ba na ji yana cewa

"Abba Abdallah Ina Sumayyan taka”

Abba ya yi murmushi ya nuna ni

"Gata nan Samir"

Shima murmushi ya yi wanda aka kira Samir yana kallona

"Abba ta yi girma, kamar ba ita bace na santa tun ana goyonta ba”

Abba ya sake yin murmushi ya ce "ka san girman ba wuya”

Kallon sa na yi da ni ma ni yake kallo a lokacin ido muka haɗa yayi min murmushi ni ma na maida masa da murmushi nawa yake haɗe da mamakin Samir ɗin da na ji ya ce

"Tunma ana goyona yasanni”

"Abba ajinta nawa yanzu" na ji Samir ya sake jifan Abba da tambaya

Abban ya ce masa

"Ta zana ƙualifying wannan shekarar"

Kai wannan akwai tambaya na bawa kaina wannan amsar a cikin zuciyata dani duk tambayata wani lokacin idan yaro na yiwa babba tambaya haushin mai tambayar nake ji amsar Samir ta katse min tunanina da na ji ya ce

"Allah ya ba da sa'a”

Addu'a kawai muka musu

"Allah ya kiyaye hanya”

Muka baro gurin muka baro Abba da Ahmad da Sadik dan tambayar Samir ta fara damuna kodan rashin sanin da ba muyi musu ba ne bansaba da suba ya sa na ji hakan

"Oho"

Muna ƙoƙarin karasa shiga cikin gidannanmu na tuna Khadija za ta siyomin ruwa pure water na bawa Halima da ta ci abinci ba ruwansha ruwan gidan namu saboda hidimar suna duk ya ɓaci a ƙofar gida muka tsaya Khadijan da na san Khadijan idan ban tsaya na ansa ba tana iya ba wani

Naji muryar Aunty Luba ƙanwar Abbanmu tana cewa

"Kin san me Fati wallahi Yaya Hashim yayi min daidai daya tafi, to zaman mai mutum zai yi a rasa mai za a girka gidan suna sai danbu kaɗai shi ma kona shinkafarnan na zamani bai samu ba, sunan ana zaune a binni, yara sai sunzo Gwarzo su cika mutane da iyayi”

Muryar Aunty Maimuna na ji ta dora da cewa

"To mai za ki gani, bayan yana tare da mai ƙashin tsiya, anyi anyi ya rabu da ita yaƙi, ni kin ga ma mu koma ciki muyi musu sallama, mu tafi gidan Asma'u mu kwana acan dan na ga kamar Asma'un ba za ta zo ba dan nan dai banga gurin kwana ba”

Aunty Mabaruka da sai yanzu na ji muryarta ita ma na ji tana cewa

"Ke aini yau nake jin labari ashe Yaya Hashim ya sama masa aiki a Katsina tuntuni ya ce ya zaɓa ko aiki ko Hauwa'un ya ce wai ya zaɓi matarsa ku jifa?"

Dawowar Khadija tare da miƙomin saƙon ya sa ba muji amsar da za su bawa Aunty Mabarukar ba da sallamar mu ta sa suyin shiru da bakin su, a raina ina ayyana rashin mutuncin dangin Abba har yakai haka a ce Baban Katsina da shi ne Yaya Hashim ya hana Abba aiki saboda Mamanmu, har sunfiso su gansa a irin rayuwarmu haka saboda ya nuna ba zai rabu da Abba ba kuma har ake Kiran Mama damai ƙashin tsiya hawaye na goge da suka zubomin, da muna shiga ɗakinmu da ƙanne Mama ke ciki da Halima da Batul wadda bayan fitarmu ta zo muka tararda cin mutuncin da ƙannen Abba sukayiwa Mama da 'yan uwanta, da gama rigimar ke nan muka shigo, Allah sarki Mama da ban da ƙaddarar aure na san ba za ta auri Abba ba ake yiwa wulaƙanci kuka na yi sosai jin labarin da Rumaisa ma takeyi hakama Khadija, dama taron masu kuɗima ana tashi da ƙananun maganganu bare wannan da kamar dole aka yiwa 'yan uwan Abba gurin zuwa sai Yamma lis Aunt Asma'u ta zo gidan suna da lokacin tuni su Batul da Halima sun tafi harna dawo rakasu, banma ganta ba muna ɗaki da 'yan uwan Mama muka ji muna tattauna rashin mutuncin irin na 'yan uwan Abba, da abun biyar a cikin matan ba wanda ya kawo masa, mukaji anacewa ta zo da ba daɗewa na ji ana cewa harta fito da na san yanzu 'yan uwanta za su ɓuya gidanta kwaɗayi da su ɗinma ba susan ba su tsira a gurinta ba.

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604

Na Cancanta 

Post a Comment

0 Comments