Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 2)

Yau da ta ka sancewa asabar tun da kannena suka tafi tahfiz na yi shirina na zuwa gidansu Halima da ni yau na Sallama tahfiz din ka sancewar shirin da mukayi da Batul za mu gidansu Halima da Batul din nake jira da za mu dubo jikinta da tun laraba rabon Haliman da makaranta da tunaninmu bai ba mu Halimar batada lafiya ba, saida class master namu ya fada a aji a jiya data ka sancewa juma'a da cewa litinin za a dubata gaba ɗaya ajin namu dalilin da ya sa mukayi shirin zuwa yau ke nan

Sallamar Batul da na ji na kuma ji muryarta tana gaida Mama da take aiki a tsakar gidan ya sa na karasa daura dankwalin da tun dazu nake fama da shi na kasa daurashi

Ina ji Mama tana cewa Batul

"Sumayyah tana dakinsu"

Dakinmu ta shigo tare da sallama

Na amsa sallamar gami da harararta

"Sai yanzu kikayi niyyar zuwa wajen sha biyu saura da na san ba za ki zo da wuri ba da na tafi makaranta kawai”

Batul da ta zauna kusa dani tace

"Kai Sumayyah kina da matsala ba gani na zo ba, kin san unguwarmu wuyar adaidata sahu ake”

Na kalleta

"Kai Batul daɗina dake akwai share guri, yanzu Magashin ce ba’a samun napep kamar kauye”

Tayi dariya

"Ai ta shigo kauyen gandun Albasa ne basa son yi”

Na mike ina yafa mayafina dan na daka ta Batul ba za mu tafi yanzu ba

"Kin ga muje da wannan firar taki mara ƙarewa”

Mama mu Kama sallama ta ba ni kudin Napep naira dari har za mu fito Mama ta kirani ta fadamin na biya gidan Aunty Asma'u na gaidata, ba dan na soba na amsa mata da cewa zamu

A dari da hamsin daga gidanmu aka kaimu zoo road har kofar gidansu Halima

A ɗakinsu muka tarar da Haliman itada Mamarsu bayan mun gaisa da Mama Haliman da mukewa sannu ta juyar dakai mamarsu Haliman ta yi dariya ganin taƙi kulamu Haliman

"Ai dama ta ce ba za ta kula kuba ko da kunzo, kwana da kwanaki bata da lafiya ba ku zo dubata ba”

Nice na kalli Haliman da duk ta rame

"Mama ba mu sani ba, sai a jiya, ki bata baki”

Mama ta miƙe ta ba mu guri tana cewa

"Kunsan dai halin Halima sai dai ku lallasheta tun da kune kuka mata laifi” da haka ta fita tabar mana dakin

Dakyar muka lallashi Haliman ta hakura mun dade muna fira da ita har wajen uku saura a lokacin na tuna da zani gidan Aunty Asma'u, Batul na kalla

"Kin ga sai yanzu na tuna zani gaida Aunty Asma'u"

"Lah ni ma na manta”

Har na miƙe na kalli Batul data sake gyara zamanta

"Ba za ki rakani ba ne”

Ta girgiza kai

"Sai kin dawo, dan gaskiya ko da take kanwar Abbanku ba zani inda za a wulakantani ba, da dai 'yar uwata ce da sai na ce ta zamarmin dole, watarana ta yiyu na sake zuwa gidanta”

Sosai na ji haushin maganganun Batul amma na sani ita ba ruwanta abunda ke ranta ko baida daɗi saita faɗama, wannan ɗabi'a ta Batul ya sa ba ma shiri sosai, Halima ce tawa dako mai abunda za a mata idan mun je dangina bata nunamin taji haushi, bare harta faɗawa wani, duk da ita ma Batul ni da ita take faɗamin ba wani take fadawa ba, amma hakan ba daɗi

Zaman mayafina na sake gyarawa da banji haushin abin da ta fadamin ba

"Nace karki je, dama Halima ta fiki mutunci”

Hararata tayi

"Eh na ji”

Halima ta dubi Batul

"Yanzu Batul da gaske kike ba za ki ba, ni da zan iya tafiya mai nisa da na rakata”

Batul ta harari Halima

"Halima nafa rantse ko Mamarmu ɗaya da Aunty Asma'u ba zan sake zuwa gidantaba haba kin manta wulakancin data yi mana, muna zaune a gidan ko ruwa bata ba mu ba, ƙannen abokan mijinta na zuwa, ta aje musu soyayyun kaji da ruwa da yoghurt saboda su suna da wadata, haba nifa kin ganni ko da ubana baida komai ba wadda ta isa ta riƙa wulakantani, da na fahimceki zan ja miki layi ko ya muke”

Haliman data ja zancen tace

"Ya isa haka Batul mene ne na tada abunda ya riga ya wuce, tun da kika ce ba za ki ba ai shike nan, ɗan uwa fa ɗan uwa ne”

Murmushi ta yi

"Halima ke nan wani ba”

"Kowanne ma”

Jin zancen ba zai ƙareba na sani barin ɗakin dan kaina ma zai iya ciwo ba kasafai nakeson hayaniya ba, kuma ni ma na tuna wulakancin data mana da sai da waɗacen baƙin nata suka tafi taja mana farantin ƙasusuwan naman da suka rage, wai a matsayina na 'yar wanta uwa ɗaya uba ɗaya talauci ke nan 'ya'yanta kuwa babu wanda ta bari ya zo gurinmu suna can saman bene ba ma su sauko ba dan dama can kayan wasansu yake da komai da tun da nake so ɗaya na taɓa hawa up din

Da wannan tunanin na karasa fitowa daga cikin gidansu Halima da ina fitowa na ci karo da Yaya Hakeem yayan Halima yana ƙoƙarin shiga gidan ni kuma na fito gaisawa mu kayi ya dube ni ka sancewar jinina da shi ya haɗu fiye da sauran yayyen Haliman biyu da Yaya Hakeem ɗin shi ne babban a gidannasu

"Badai sai yau Kika zo duba ƙawar taki ba”

Na ɗan rufe fuska alamun kunyar abunda na yi

"Eh Yaya Hakeem ban san da rashin lafiyar Haliman ba sai jiya”

Yace

"Ban saniba jiya har unguwarku naje gurin wani abokina, kin ga da na san baki sani ba da na biya na faɗamiki, ko da ke ma idan naje bakiso na zo gidanku"

Na ɗago kai na kallesa

"Eh mana, kwanaki da naje unguwar na ga Ahmad a waje nasa ya kiraki mu gaisa, ƙin fitowa kikayi” ya ƙarasa maganar shi ma yana kallona

Nace

"Lokacin aiki nakewa Mama, kuma bata nan lokacin"

Ya harareni

"Daɗina dake daɗin baki, har kin fito za ki tafi?"

Na girgiza kai

"A'a zanje gidan Aunty Asma'u ne, tare da Batul mu kazo"

Yace

"To shike nan saura ku wuce ba ku min sallama ba”

Murmushi na yi

"A'a za mu yi ma insha Allah"

Daganan ya shige ciki ni ma na wuce ina tunanin halayyar su Halima duk gidansu suna da kirki ba su da matsala takowanne fanni, duk abin da wani daga cikinsu ya nuna yanaso suma suna sonshi, Yaya Hakeem kuwa kamar Yaya haka yake a gurina, yadda muke shiri da shi ko da Halima basayi haka, duk abin da ya yi wa Halima to ni ma saiya yi min Batul ma yana yi mata sai dai ba kamar ni ba ina tafe ina wannan tunanin har na karasa gidan Aunty Asma'u

Sai da na buga gidan mai gadi ya leƙo duk da ba wani sani yayi min sai dai yadda nake zuwa gidan jefi jefi ya sa ya ganeni da kuma kamar da muke da Aunty Asma'u dani dangin mahaifina na ɗebo sosai ba abunda ya banbantani da Aunty Asma'u saidai ita hutun data samu yanzu ya sa kyawunta ya fito sosai, kofar ya buɗemin da murmushinsa ciki na shiga ina gaida mai gadin

Ya amsamin

"Lafiya lau, 'yar hajiya ashe kina nan, yaushe rabonki da zuwa”

Nace

"Baba makaranta”

Ya ɗaga kai

"Haka ne Allah ya taimaka”

Na amsa da Amin na wuce

Saboda kamar da muke da Aunty Asma'u Baban ya tanbayeni alaƙarmu da Aunty Asma'u ya muke na shaidamata tun daga ranar yake faɗamin 'yar hajiya, harabar gidan da motoci a kalla uku suke kuma duk masu tsada na wuce kofar falon na karasa na yi knocking ka sancewar gidan upstairs ne na yi sa'ar ina knocking na ji kofar buɗe na tura kaina falon da ƙamshi Mai daɗi ya bugi hancina Aunty Asma'u tanada tsafta sai dai matsalarta ɗaya rashin san talaka duk abin da talaka zai yi mata baya burgeta ko da ɗan uwantane tun ina yarinya idan mun je Gwarzo nake ganin hakan waima ni dalilin da ya sa bata min wulakanci kamar ƙannena saboda kamar da nake da ita amma dai duk da hakan bawai tsira na yi ba a gurinta, da 'yar aikinta da bata wuce tsarata ba na ci karo, tana goge center table da ya ka sance na glass, sallamar da na yi ta amsa, tana yi min

" sannu da zuwa” muka gaisa ta shige ciki da towel din goge gogen a hannunta tana cewa bari ta kira Aunty Asma'un "to" kawai na ce na bita da kallo, ina ayyana wannan Harira da yake sunan 'yar aikin wanne irin zama take gidan Aunty Asma'u dan Harirar ba wata wayewa tare da ita gaskiya tana hakuri dai da Aunty Asma'u a raina na ayyana hakan faɗan Aunty Asma'u da na jiyo ya katse min tunani

"Sai akace ki ce mata bari ki kirani, Wai maike damunki Harira”

Naji muryar Harirar

"Ya hakuri Aunty gani na yi 'yar uwarkice”

Cikin faɗa Aunty Asma'u na ji ta ci gaba

"Da take 'yar uwata mai zan yimata ni ma ba wani abu gareni ba, idan ma wani abu ubanta ya turo ta karɓa masa danni ba ni na ce yaƙi neman nakansa ba, koya zauna da mace mai ƙashin tsiya, tun da Allah ya rufamin asiri dangi duk an zuramin ido"

Banga laifin Aunty Asma'u ba saboda NA CANCANTA ta faɗamin hakan laifinane a karo na barkatai na sake tun karar rayuwar da gininta bai dace dani ba, karar takalmanta da na ji ya sa ni maida dubana ga matakalar benen da Aunty Asma'u take sakkowa da takunta na kasaita daka ganta za ka tabbatar kuɗi sun zauna mata duba da kalar kayan jikinta da yanayin jikinta fatarta sai sheki take alamun hutu ya ratsata da murmushin da nake da tabbacin ƙirƙirarsa ta yi ta karaso cikin falon tana ƙoƙarin zama kujera tace

"A'a Sumayyah kece a gidan nawa yau"

Na ɗan murmusa ni ma

"Eh Aunty ina yini”

"Lafiya kalau, ya mutanan gidan ya hanya” ta faɗi haka tana danna remote ɗin da ta ɗauka a kujerar da take zaune

Nace” Alhamdulillah, Aunty dama gidansu Halima na zo bata jindaɗi shi ne na biyo mu gaisa "

"Allah ya bata lafiya” ta faɗa

Na amsa da

"Amin", daganan na miƙe ina gyara zaman mayafina tamkar babu komai na ji tace

"A'a ba dai har tafiya za ki yi ba ko ruwa ba’a kawo miki ba”

Nayi murmushi mai ciwo

"Alhamdulillah, da batul muke tana jira na ne”

Ta miƙe ita ma

"Eh duk da hakan dan Allah koma ki zauna na kawo miki kudin ko napep saiki hau da su"

Nace

'A'a Aunty ki barsu da kuɗi a hannunta”

"Eh duk da hakan nawa dabanne” ba tare da na sake cewa komaiba ta sake hayewa sama ban jira dawowartaba na yi saurin ficewa daga gidan a raina ina ayyana nida gidan Aunty Asma'u ko ba har abada ba zan daɗe ban jeba dan wanna abun da take min tunaninta na ji abin da ta ce ne shi ya sa yau bata yi min rashin mutuncin data sha yi min ba, a haka na iso bakin gate ɗin ganin banga mai gadinba ya sa na buɗe kofar na fice dan raina ɓace yake ba zan iya jira ya dawo banbarmata gida ba, a haka na fito a raina ina mai takaicin rayuwa irin wannan saboda damar da Allah ya ba ka hatta danginka saika zaɓi da waɗanda zaka yi huldar zumun ci dasu nida kaina na sani muba masu dukiya ba ne da abinci yau da gobe yake gagararmu bare har a zo inda muke dan kyautar dubu ashirin ba za mu iya bayarwaba da itako Aunty Asma'u ɗari ma ta bayar ba abun a tambaya ba ne dalili mai ƙarfi ya sa ta ɗauki duk mai zuwa gurinta kwaɗayayye muddin ba mai kuɗi ba ne, niko a nawa ra'ayin duk da idan aka ba mu muna buƙata amma ba zanje inda za aci fuskata ko aƙi darajani ba duk da NA CANCATA a yi min hakan a tunanin mafi rinjaye a cikin al'umma amma ni anawa tunanin da yardata Allah ke rabawa ni ma zai iya rabawa ya bani, duk da ba kudi gareni ba a hannuna amma na gwammace na tafi a kasa saboda maganganun marasa daɗin da kunnuwana suka jiyemin, koma ba haka ba nasaba zuwa biyar bata hadani da ita kawai inaso Aunty Asma'u ta fahimta a cikin talakawanma akwai wanda yasan darajar kansa, ban san irin yadda zan misalta canjin rayuwarnan ba da ƙarƙarin ko da kyautar muce ga 'yan uwan Abba dubu biyar shi ma sai Mama ta haihu dan mai kuɗi inda yake kai kyautarsa inda yasan za su dawo, bawai gurinmu talakawa ba, amma na sani Allah yana tare damu hawayen da suka zubomin nagoge ganin na karaso gidansu Halima, ko minti goma ba mu ƙaraba bayan komawata gidan muka fito a ƙasa muka fara tafiya dan ba kuɗi hannunmu ragowar hamsin ta rage mana da sai mun je unguwarmu Batul za ta hau napep ta karasa gida da sai bayan fara tafiyarmu na tuna da Yaya Hakeem ya ce na masa magana idan za mu tafi. 

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments