Na Cancanta (Kashi na 1)

    Dukkan godiya su tabbata ga Allah tsira da aminci su kara tabbata ga annabi Muhammad (SAW)

    Sumayyah Abdallah Khalil sunana ni hafaffaffiyar garin Gwarzo ce, da ta ke karamar hukuma ce dake Æ™arÆ™ashin jahar Kano da sana'a ta maida mahaifina cikin birnin Kano bayan haihuwata da muke yanzu zaune a cikin birnin Kanon unguwar Gandun Albasa mahaifina Malam Abdallah Khalil da mahaifiyata Hauwa'u ni ce diyar fari a gurinsu sai kannena Ahmad shi ne mai bina daganan Rumaisa, Khadija, SadiÆ™, Khalil da a yanzu shi ne Æ™araminmu, mahaifina Æ™aramin karfi gareshi yadika yake saidawa ficis a kasuwar kantin kwari a gefen kasuwa da runfarsu take wani lokacin kuma zagayawa yake cikin kasuwar, tun tasowata da na soma fahimtar yanayin yadda rayuwarmu take na fara janye jiki ga duk wanda ya fimu karfi, haka burina na zama ma'aikaciyar jarida duk na ajiyesa gefe, burina yau ace na kammala secondary da nake yanzu SS1a government Girls Gadun Albasa na cikin garin Kano ba dan komai ba saidan hidimomi su fara sauki daga kaina, Mamarmu macace mai zurfin ciki ko da garinmu mu kaje sam ba za kaji ta fadawa 'yan uwanta babu ba haka za mu yi kwanakinmu mu dawo duk da ka sancewar danginta ba masu kudi ba ne haka suke Æ™oÆ™arin hadomu da kayan abinci da na sawa idan mu kaje, a gurin mahaifiyata na koyi boye sirrina zai wuya maganganuna masu muhimmanci na fadawa wasu musamman rayuwar da muke ciki a gidanmu, danginsu Abba kuwa babu laifi duk masu kudine sai dai suda Abban sam babu taimako idan muka je gidajensu ko da mun je Gwarzo ko gidajen waÉ—anda suke a nan cikin Kanon babu kyauta tsakaninmu sai jifanmu da maganganu marasa dadi, na sani tun ina karama Abbanmu mai zuciyar neman nakanshi ne sai dai har yau Allah bai kaddara zai yi arziki mai yawa ba, duk da ka sancewar ya yi karatu aikin ne garesa ya yi wuyar samu, ba zance Abba bai da sa'ar rayuwa ba, tun da yanada lafiyar fita ya samo na kansa harma ya ishi iyalansa mu shida da shi da Mama suka ka sance na takwas kawai abin da na sawa raina arziki ne Allah bai kaddara zai tara ba, irin yanayin da muka tsinci kanmu na hantarar dangi ya sa muke zaune guri guda babu mai sha'awar zuwa dangi da gani har kannena, duk da ka sancewar mu din talakawane amma sam ba muda kwadayi irin na wasu daga cikin talakawa kamarmu, kai idan ba kazo gidanmu ka gani ba dan ka gan mu waje tunaninka ba zai ba ka mu talakawa ba ne sosai duk da bawai kaya ba ne masu tsada jikinmu amma kullum za ka gan mu kayan jikinmu wanke goge, da ya ka sance aikin Mama tun ina yarinya har na girma na dora da yiwa kannena, haka batun abinci babu maiwa Mama korafin abinci a gidanmu musamman idan mun yi baki ko da muna jin yunwar har sai sun tafi, duk da saimuyi watanni ba mu ga bakin ba domin dai da masu kudi akafi harka a yanzu mu kam idan an zo kudin mota ma ba za ka samu ba, masu kudi kuwa sam indai ba haihuwa ba Mama ta yi ba ba mai zuwa gurinmu shi ma haihuwar ba za a zo suna da wuri ba da duk dangin Abba ke hakan to mai za suci daga garemu, dan sanin kowane irin rayuwar da talaka yake cikin dangi ba ma sai an fada ba, Mama idan ta yi maganar ba’a zuwa gurinta mamarsu takance

    "Hauwa'u idan an zo nauyi za a dora muku, kin san 'yan uwanki suma ba karfi garesu ba wata da kyar za ta hada kudin zuwa, kuma tana zuwa daga gareki keda Abdullahi zatace tana jiran nadawowa”

    Jin maganar Gwaggo da Mama taji gaskiyace ya sa ta hakura da batun son 'yan uwanta suzo gurinta, batun gidan da muke na haya ne ina tausayin Abba da yadda yake biyan kudin hayar da sai Mama ta hada da nata kudin da take sana'ar cikin gida gishiri, ashana, maggi, Omo da sauransu duk da ka sancewar cinikin kayan jefi jefi akeyi dan yawanci unguwar tamu mazajensu ajiyemusu kayan abinci suke komai sunadashi idan ba abun ya kare ba kafin a siyo a nan ale cinikin, wasu kuma da su siya gurinka gwara su tafi bakin titi su siyo

    Batun kawa sam ni ba maison tara kawaye bace dan kawata daya ce wadda muka shaku ba laifi Halima Farouk tun daga JS 1 muke tare da yanzu muke SS1 Halima ce kawai tun farkon haduwarmu na fahimci tamkar rayuwarmu za ta zo daya wannan ya sa kawancenmu dorewa, ka sancewar ita ma Haliman bawai 'yar masu kudi bace, bawai ziyartar Haliman nake ba dan da tazara tsakaninmu, sai dalilin auren da kanwar Abbanmu Aunty Asma'u ta yi unguwarsu Halima take ganina shi ma nakan dade banje gidan Aunty Asma'un ba dan mijin da Aunty Asma'un ta aura mai kudi ne ita ma kuma Aunt Asma'un tana auren ta fara business har kasar waje take zuwa hakan ya sa naja baya da zuwa gidanta danni banison shigewa wanda muke da tazara da shi ta arziki dan na girmama tawa rayuwar, kuma Aunty Asma'un zan iya kirgawa tun aurenta a Kano baifi zuwa biyu ta yi gidanmu ba shi ya sa ni ma naja baya da zuwa gidanta dan dama ita ma baso take aje gidantaba hakan ya sa bana sha'awar zuwa, dan tun daga Gwarzo za ta yi waya a zo a taya ta zama idan mijinta bayanan muda muke a guri guda sam ba za ka ji ta kirani ba saboda kada na shafawa rayuwarsu talauci nafi yakinin dalilin da take hakan ke nan

    Batun tarbiyyarmu iyayenmu suna tsaye kanmu ni da kannnena hakan ya sa komai namu yakanzo da sauki dan ko su Khadija da Rumaisa idan angansu waje saidai makaranta ko aike, basa kulafucin zuwa makwabta kwadayi, kai ko da an aikesu sunje ruwan gidanma basa sha, idan ko za mu tafi makaranta tare muke tafiya sai sun fara zuwa tasu nake wucewa tamu

    Yau ma kamar kullum mun fito tare nida su Khadija da tun fitowarmu take kunkunai na dubeta

    "Wai ke mai aka miki ne Khadija”

    Ta É—an bata fuska

    "Yaya yau ma babu, kudin tara, ga makarantarmu da nisa kuma ba kudin Napep, gashi mun makara” tayi maganar tana duba agogon hannnunta

    Na sake dubenta

    "Haba Khadija cikinmu mu hudu wa aka bawa kudin taran, kuma ai mun ci abinci ko, kuma da za ki maganar kudin Napep ko tafiyar kasa da makara baga SadiÆ™ ba shi da yake Æ™aramin yaro baiyi magana ba, Dan Allah ki canza”

    Baki Khadija ta turo

    "To shike nan amma Yaya ciyayya muke da kawayena kullum suke kawo abin da za mu ci da za mu ci idan anyi break ni babu abin da nake kawowa, sai suga kamar wayau ne”

    Na dubeta sosai

    "Khadija ciyayyya fa, ai kema kin san wayon ne kike, ke da ko kudin tara a sati baifi ki samu sau É—aya ba za ki yi ciyayya da mutane, dan Allah ki daina Kin ga koni banayi”

    Tace

    "Maiyasa Yaya?"

    "Kawai bana san gori shi ya sa, kin san idan kanacin na wani ba acin naka watarana sai anyi ma gori”

    Da wannan hirar da muke da Khadija muka karasa special primary dinsu suka shiga su biyu ita da Sadik sai ni da Rumaisa muka wuce tamu da Rumaisa take aji É—aya a Secondary Rumaisa bata da surutu gata da hakuri halayyarta da Khadija ta banbanta Khadija yarinyace mai son gayu sosai da son ace ita ajin farko take a komaima, kyau dai Allah ya bata dan kaf cikinmu ba mai nunawa Khadija kyau, sai dai duk da hakan Khadija bata jure wulakanci, kuma ita ba mai san gori bace

    Har muka karaso makarantarmu da har an fara taron makara Rumaisa batayi magana ba

    "Rumaisa Abdallah"naji Sajida kawar Rumaisan ta fada da mukaci karo dasu gurin makarar suma an taresu Rumaisa da bata kula da ita ba sai lokaci gurinta ta karasa, bulalar makarar aka yi mana, muka wuce ajijuwanmu, sallama na yi na shiga da a bencinmu ni kadaice na zo, zamana ba wuya Halima ta shigo ita ma tana aikamin sakon hararar harta zauna

    Na fara tambayarta

    "Haba Halima mai ya yi zafi ido zaici wuta mai na yi Miki”

    "Ban sani ba 'yar rainin wayau, tun da na hango ki nake kwala miki kira kikayi banza dani” Haliman ta karasa fadar hakan tana ajiye jakarta gefen tawa

    "Yi hakuri Halima Kena kin san ban jiki ba ne, amma ya za ayi na yi miki shiru, daga wajen ina kika kirani”

    "Kofar makaranta mun sauka a Napep"

    Nace

    "Yi hakuri Sady banjiba hankalinmu ya yi gurin taron makarar da akeyi”

    "Kice dai baki jiba dan Rumaisa ko taji na san ba za ta fadamiki ba, yarinya mai nauyin magana”

    Nayi murmushi da dariya ta jin Halima ke korafin nauyin bakin Rumaisa da ita dinma hakan take

    "Ai halinku É—aya da Rumaisan"

    Ta dubi kanta

    "Allah ya kyauta, ni ai ba sunanmu guda ba ke ce kika koya mata halinki Kika mata wayau"

    Sallamar Batul Ahmad da take ita ma 'yar bencinmu ta katse firarmu data shigo wadda ita kawancenmu baikai kawancen da nake da Halima ba Batul na zama malaminmu na physics ya shigo mikewa mukayi muka gaishesa daganan muka fara lesson da ba laifi ana gane karatun Malam Hamid da yake bautar kasa ta kawo shi makarantarmu, sai dai bahaushene É—an aalin garin Katsina ne

    Bayan watanni

    Haka rayuwarmu ta ci gaba da ka sancewar cikin godiyar Allah dan sai na ce yanzu al'amura sun sake rincaɓewa fiye da da, dan yanzu Abba saiyaje kasuwa ya yini baiyi cinikin dari ba, wannan abun idan na tuno yakan sani hawaye tare da tuno makomarmu a haka

    Sallamar Halima da na ji ya sani sauke tagumin da na yi da hannu biyu na kirkiri murmushi na dorawa fuskata, ganin Haliman da na yi da nake zaune tsakar gida ina tsare gida Mama ta fita makwabta barka, yara suna É—aki suna kallo ka sancewar akwai nepa garin, sallamar na amsawa Halima ta zauna gefena a kan tabarmar da nake kai gefena ta aje kula

    "Halima mene ne wannan"

    Na nuna kular gefen nawa

    Halima ta yi murmushi

    "Abin da kike so na kawo miki”

    Na dubeta da zaro ido

    "Dan Allah fa Alala ko faten doya?"

    Tayi dariya

    "Faten doya ne, ina komawa gida na ga shi muka yi shi ne na ce Mama ta zuba Faisal ya kawo miki, to Mama ta aikesa kasuwa, kawai shi ne na taho ina fitowa na ci Karo da yaya Baffa ya dawo cin abinci shi ne ya kawoni”

     

    Ba ƙaramin dadi na ji ba dan yau babu abin da muka girka tun safe sai ruwa da nakesha da cikina ya fara kullewa da muka dawo makaranta ma ba mu tarar an girka komai ba, Halima na kalla ina jin a raina Halima ta kara matsayi a gurina duk da dama tana da shi hawayen da ban san sun zubo ba sai duminsu na ji na yi saurin gogewa na dubi Halima

    "Halima na gode”

    Haliman ta girgiza kai

    " godiya babu tsakaninmu, kuma kukan mai kike, na sani, baki taba ƙoƙarin fadamin abin da ya shafi rayuwarki ba amma ni ina ƙoƙarin fahimta, Sumayyah idan kina farin ciki na sani, haka idan kina sabanin haka, mene ne na hawayen"

    Nayi murmushi

    "Babu komai”

    "Kya ji da shi dai, ina Mama” cewar Halima

    "Ta shiga makwabta, barka yanzu za ta shigo"

    "Aiko dai sauri nake ki gaidata, ta yi maganar tana mikewa

    Na dubeta "badai tafiya za ki yi ba, ba za ki jira ta zo ku gaisa ba”

    "tare da Yaya Baffa muke shiya kawoni a adaidaitarsa, kar ya yi ta jira na, ko gida bai shiga ba na ce ya kawoni ba zama zan yi ba”

    Hijabin Rumaisa dake kan igiya nasa na rakata har gurin adaidaita Yaya Baffa

    "Ina yini yaya Baffa”

    Ya amsamin da cewa

    "Lafiya lau, ya karatu?"

    "Alhamdulillah Yaya”

    Daganan Halima ta shiga adaidaitar ya ja suka tafi bayan mun yi Sallama

    Yaya Baffa ba mutum ne mai surutu ba iyakacin ka da shi gaisuwa ce, ko da gidansu naje

    cikin gidan na dawo inda na tashi na koma na zauna ina jiran Mama ta dawo a kasafta faten dan ba iya yunwar kowa ke jinta musamman Mama da take goyon Khalil a lokacin na sani duk ta fimu ji, ban san a wanne mataki zan aje Halima a cikin zuciyata ba tana ba ni kulawa da tausayina fiye da 'yan uwanmu da suke watsar damu saboda mu din ba wasu ba ne idan an zo gurinmu mai za a samu dan ko a yanzu kafin ka ga mai kudi yana mu'amala da talaka za ka shekara da shekaru kana bincike kafin ka samu, amma Halima tana tare dani tun kafin tasan wace ce ni kuma har ta sani hakan bai canza ba, duk da Haliman talakawanne amma a hakan take ƙoƙarin kyautatamin, kafin na fadamata matsalata take fahimta idan tanada maganin hakan tana ƙoƙarin yi min, hawaye na goge tunowa da Aunty Asma'u da kaf layinsu Halima da unguwarsu baki ɗaya ba gida irin nata amma da biyar bata taɓa tunanin kawo mana na nuna kyautatawarta garemu ba, sai Halima da kaf layin gidansu ne na kasa dake zagaye da langa langa, yayyenta maza guda uku ke yin komai na gidan ka sancewar mahaifinsu baida cikakkar lafiya hawan jini da ciwan sugar ke damunshi, amma a haka take ƙoƙari duk ranar da taga wata damuwa fuskata take ƙoƙarin kawomin abinci data koma gida, saboda zuwan da take gidanmu ta fuskanci rayuwartamu.

    **** **** 

    Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
    Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
    Lambar Waya: 08124915604
    Na Cancanta

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.