Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Baya Kulani, Sai Nake Kiran Tsohon Saurayina Awaya Muna Ɗebewa Juna Kewa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam Dan Allah gatambaya malam kanwatace wani saɓani yashiga tsakaninta da mijinta malam adalilin ta gayamai gaskiya akan wani abun da yake Wanda bai dace ba taimai nasiha yaji tsoran Allah yadaina shi ne yake fushi da ita bayacin abincinta baya mata magana baya kusantarta kuma ta ba shi hakuri akan ɓatan ran da tai yau sati ukku kenan suna haka malam ko kiranshi tai awaya baya dauka to wannan kuncin datake ciki haryakai ta tsani mijinnata ba ta kaunarshi yanzu to dama akwai tsohon saurayinta tanada lambarshi shi ne take kiranshi suna dan ta debe kewar bakin cikin da take ciki hartana tunanin tanemi saki gurin mijinta dan ta je ta aureshi wancan saurayinnata shi ne takeneman shawara Dan Allah ataimakamata ngd.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To abin da mijin yayi bai kyautaba indai ayanda tambayar ta zo haka abin yake azahiri to hakika tafishi gaskiya domin tsakanin mace da miji akwai shawara da wa'azi da nasiha da kowa yake da hakkin yayiwa abokin zaman alokacinda yadace.

Sannan kaurace mata dayayi wannan saɓawa dokar Allah ne daya san uqubar da Allah ya tanada akan abin da yayi dabai aikataba lallai yaji tsoran Allah yadawo gareta tareda neman afuwarta.

To itakuma matakinda ta dauka bai kamataba itama haramunne abin da tayi ta saɓawa Allah taketare dokar Allah lallai inaso tasani yanzu zunubinda take dauka yafi wanda yake dauka kamar zina takeyi domin zina kala kala ce munyi bayanin cewa akwai zinar baki akwai ta ido akwai ta hannu akwai takafa akwaita farji to koshakka babu tayi kuskure.

Anan kuma ni Abusalmah inaso nace wani abu "wato dagajin matakinda tadauka kasan cewa itama dama bamai tsoran Allah bace to wacce ba ta da tsoran Allah taya zatace wai tayiwa mijinta nasiha yaji tsoran Allah? Kaga wannan akwai alamar tambaya watakilama to mijin yafita gaskiya domin dana lura da tambayar sosai sainaga dama gashi already tanada lambar saurayinta to akanme take ajiye da lambar saurayinta? Maye yake tabbatar mana cewa dama basa waya saiyanzu da aka samu saɓani? Idanma basa waya akanme take ajiye da lambar? Amsa shi ne dama kenan ta ajiye lambarne randa ba mijinta shi ke nan tanada safaya daling to kuma kaji wai waccea takeda wannan halayyar ita ce zatace kuma wai taga mijinta yanayin abin da bai kamataba tayimar wa'azi yaji tsoran Allah to yaya bazakiwa kanki wannan nasiharba? matakinda kika dauka saimuka fahimci kamar kema bakya tsoran Allah ɗin".

Shawarata anan shi ne lokacinda haka tafaru saiku shigar da manyanku ciki iyaye waliyai suyimuku sulhu abashi hakuri adaidaita tsakaninku asamu masalaha dahaka kikai dayanzu wani zancan akeyi ba wannanba amma saikema kikadau mataki marakyau to yanzu kindau matakin saɓawa Allah kuma ahakan kikeso Allah yakawo miki dauki akan wannan saɓanin dakuke ciki, Lallai kuyi kokarin samun gyara maikyau Allah kuma yadaidaita tsakaninku.

Allah shi ne masani

JUNAIDU BALA ABDULLAHI

Abu Salmah

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments