𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslm. Malam ya
kokari wlh ina cikin damuwa, Yar'uwa ta ce za ta jefa kanta cikin halaka da
auranta, wlh malam ni na san tana cikin damuwa tun ba yanzu ba tun da komai
tana gayamin nice me ba ta hakuri kuma hadda shi nasha yin sulhu, auran shekara
2 kenan kuma ba tare suke da mijin ba sai weekend yake zuwar mata amma duk
zuwan nan nashi fa har ya tafi ba Shi da lokacinta koda yaushe yana joint na
shan SHISHA har cikin dare, ita da iyayenshi wallahi sai fama suke akan wannan
halin nashi amma yaki bari babanshi har baki ya ce zai mishi amma yaki yayi
hankali ya daina, yanzu dai jiya ma ta ce min ta kamashi da kwaya a gidan, kuma
hakuri idan ya dawo hankalinshi ba irin wanda baya ba ta sai ya ce tayi ta
mishi addu'a zai bari amma fa har yau bai taɓa
kokarin daga kafa ba, dama zancen hakkinta na aure sai idan ta nema shi ma sai
in yana hayyacinshi da safe don bacci kawai yake zuwar mata gidan kuma tana
masa complain dan ta ce tana cutuwa dan Allah yayi ta mabukaciya ce dan ta ce rashin
sa a tare da ita har blue film take gani, yanzu dai malam inda matsalar take
wallahi har ta fara kula tsohon saurayinta suna waya shi ma kuma yanada aure
kaddara ce ta raba su basu auri juna ba, kuma a binciken da nayi har sun fara
shirin yadda zasu haɗu,
wallahi malam a yadda na san soyayyar da sukai a baya komai zai iya faruwa
wallahi za ta ba shi kanta su lalace ne dan Allah malam meye shawara duk da
jiyan na mata faɗa
sosai kuma na ba ta rashin gaskiya amma da abin na kwana Wallahi. Mijinta komai
yana mata na dawainiyyar da Allah ya dora mishi ba ta rasa komai ba wallahi sai
wannan matsalar tashi yaki ya gyara..
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Da yawa Mata
sun Tsinci Kansu cikin irin wannan Mawuyacin halin na Rashin Tarbiyyar
Mazajensu. Sakamakon Addu'ar iyaye da Addu'ar Waɗannan
Matan nasu kuma Cikin Taimakon Allah sai kiga sun Gyaru, sun shiryu sun dena Abin
da suke yi na shaye-shaye ko Shiririta. Sabida Haka Abin da ya dace shi ne ki
Dukufa da yi Masa Addu'ar Shiriya ke da iyayensa. Lokaci ɗaya sai kiga ya zama
Mutum Kamili ya dena duk Abin da yake yi. Wannan shi ne Nawa Shawarar. Tinda ba
ya dukanki. Baya Wulakanta Ki, baya hana ki Ci da Sha da sauran hakkokinki. Da
ace kafin Aure ne, zan baki shawara akan kar ki Aure shi. Amma Tinda kin riga
da kin Aure shi kuma har da yara. Ga shi Kuma Baya Wulakanta Ki, baya tauye
miki Hakkinki na Auratayya. Inaga sai ayi Hakuri ake yimasa Addu'ar Shiriya.
Sai dai fa idan yana dukanki ko yana Gaya Miki bakaken Maganganu zaki Iya cewa
ya sake ki. Anan Baki yiwa Allah Lefi ba. Sabida haka acigaba da Addu'a.
Maganar Kula
Wani Saurayi Kuma bayan Aurenta da Wani ai Bai Wuce Hauka ba da kuma Rashin
Tunani. Ina mamakin Mata. Sabida ta yaya wani yana Ikirarin yana cewa yana son
ki kuma Bai Aureni ba. A Haka wani ya Rufa Miki Asiri ya Aureki. Amma kuma kina
harin wanda bai Aureki ba.? Wannan zaisa ki Wulakanta Aurenki, ki Wulakanta
Rayuwarki, Ki Wulakanta Rayuwar 'yayanki. Ki bar Musu Abin Magana. Har a gidan
Aurensu. Domin in kika sake aka kai Diyarki gidan Kishiya. Alhalin kin taɓa aikata wani Abin Kunya
da wani Namiji daban wanda ba Mijinki ba. Wallahi sai wannan kishiyar taki ta
sami Labari, kuma an dinga Yiwa Diyarki Habaici akan wannan. Kinga kenan kece
kika wulakanta Diyarki.
Ga Kuma Azabar
da zaki Haɗu da ita
a Lahira. Sakamakon Abin da Kika Aikata. Zaki Rayu a duniya Kuma Kina cikin
Fushin Allah. Ai Masifar tayi Yawa. Kuma duk Namijin da yayi Iskanci da ke. To
zai Iya yi da Kowacce Kalar Mace. Ma'ana zai Iya Yin Iskanci da lafiyayyiyar
Mace da wadda ma ba Lafiyayyiya ba. Wanda kuma zai Iya dakko wannan Jinyar ya
Goga Miki. Ke kuma ki Gogawa Mijinki na Asali. Masifa Kan Masifa Kenan.
Haramunne ga
musulmi namiji ko mace kallan batsa. Wajibine ga musulmi yaruntse ganinsa daka
dukkan abun da Allah yaharamta kallansa, Allah madaukakin sarki ya ce:
قُلْ لِلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ
لَهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ
خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ
kace da
mumuinai maza da mata su runtse idanuwansu ganinsu daka haram, sukiyaye
farjinsu ( daka aikata zina) wannan shi ne abun da yafi tsafta agaresu lallai
Allah mai baiwa mutane labarin abun da suka aikatane ranar alkiyama.
(Suratun-Nur: 30)
Saboda haka
kallon blue film ta kowacce irin hanya bai halatta ba.
Allah ya Gyara
Halayenmu. Ya kare mu, ya kare Mana 'yayanmu da Matan Mu da Gidajen Mu.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi
Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.