Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba Ni Da Tsayayyen Saurayi - Wanda Ya Zo Da Niyyar Yana So Na Ba Ma Daɗewa Da Shi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum.Malam don Allah shawara da addu'a nake nema. Nakai shekara ashirin da biyu amma ba ni da tsayayyen saurayi wanda in aka ce ya fito ayi aure zai fito. Akwai wanda ya taɓa neman aurena har manya sun shiga cikin maganar daga baya ya ce ya fasa. Duk wanda ya zo gurina da niyyar yana sona bama dadewa da shi sai ya daina zuwa ba fada ba komai. Akwai wani mutum a layinmu ya ce mun inzo ya kaini gurin wani malami in amshi taimako, ni kuma ban yarda da shi ba shi ne nike neman shawara da addu'a a bakunanku masu albarka.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum salam wa rahmatullahi

Hakika kinyi zurfin tunani da baki biye ma wannan mutumin ba. Domin kuwa acikin masu bada irin wannan taimakon ana samun da yawa waɗanda sukan aikata shirka da kuma haramtattun abubuwa iri-iri waɗanda shari'a ba ta yarda dasu ba.

Yara 'Yan mata da yawa suna fama da Irin wannan matsalar taki. Amma dai wasu tasu matsalar ba ta rasa dangantaka da matsalar nan ta jinnul ashiq (Namijin dare).

Wani irin Shaiɗanin Aljani ne wanda yake addabar Mata. Yakan zo ma mata acikin mafarkinsu yana saduwa dasu, ko kuma yana nuna musu abubuwa iri-iri. Kuma yakan shiga zukatan samarinsu yana chusa musu waswasi game dasu, yana shiriritar dasu, ko kuma ya chusa Qiyayya atsakaninsu.

Wasu kuma matsala ce wacce ta danganci irin gidajen da suka taso, ko kuma yanayin Mu'amalarsu da jama'a. Amma dai dukkan matsalalolin biyu babban maganinsu shi ne addu'a tare da jajircewa wajen nafilfilin dare da rana.

Idan har abun ya tsananta kuma, akan yi Ruqyah wani lokacin ma har akan tarar da shi Aljanin dake jikin.

Don haka kema shawarar da zan baki anan ita ce ki dage wajen yin azkar ɗin safe da yamma da karatun Alqur'ani da zikirin Allah ko yaushe. Sannan ki yawaita ayyukan biyayya na nafilfili kamar sallolin dare da rana da yin azumi da kuma Sadaqah don neman yarda Allah.

In Shã Allahu zaki ga biyan bukatarki da yayewar damuwarki cikin sauki. Amma kada ki rika bibiyar Malaman duba ko bokaye da 'Yan bori.

Allah ta'ala ya tsare mana imaninmu.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments