𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Magidanci ne yake da matar
aure mara sha’awa, yana shan wahala sosai wurin neman biyan buƙatarsa
a wurinta. Takan tsara masa wasu abubuwan da sai ya cika su kafin ya samu biyan
buƙatar,
wasu lokutan ma sai ta gama lamarrunta kafin ta saurare shi. Abin har yakan kai
shi ga bin wasu hanyoyi kamar kallon haram domin gamsar da buƙatarsa.
Wai wace shawara za a ba shi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Da farko dai
wajibi ne ma’aurata su san cewa biyan buƙatar juna ta hanyar saduwa yana daga
cikin manyan dalilai ko maƙasudan yin aure.
Kauracewa
Shinfidar Miji ba Tare da Wani Karɓaɓɓen Uzuri a Shar'ance ba
Yana Daga Cikin Manyan Zunuban da Saboda Girmansu Har Ubangiji Ya La'anci Matar
da take Aikata Haka. Hadisi Ingantacce Ya Tabbata Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam Yana Cewa:
عن أبي هريرة
رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم-: ”إذا دعا الرجل امرأته إلى فراشه فأبت فبات غضبان عليها؛ لعنتها الملائكة حتى تصبح“
{مسلم: ١٤٣٦}
An Karɓo Daga Abi-Hurairah (ra)
ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Idan Miji Ya Kira
Matarsa Zuwa ga Shinfidarsa Taqi Zuwa, za ta Kwana Ana Fushi da Ita; Mala'iku
za su Dinga tsine Mata Har Gari ya Waye”.
{Muslim: 1436}
Haƙƙi
ne mai girma a kan mace ta zama a cikin shirin biya wa mijinta wannan buƙatar
a duk lokacin da ya yi buƙata, matuƙar dai ba tana cikin yanayi ko halin da
shari’a ta hana saduwa
a cikinsa ba ne, kamar a lokacin rashin lafiya ko haila ko nifasi. Har a waɗannan lokutan ma malamai
sun yarda cewa matar tana taimaka wa mijin wurin jin daɗi da duk inda ya so a jikinta, ta hanyar
shafa ko runguma ko sumba da makamantansu, in ban da saduwar ta wurin da aka
hana. Watau, bai halatta ya yi amfani da al’aurarsa a cikin gabanta a lokacin
haila ko nifasi ba, haka ma ta cikin duburarta, ko ta cikin bakinta ba a kowane
lokaci.
Amma a lokacin
da miji ya ga irin wannan matsalar a cikin matarsa, abu na farko da ya kamata
ya fara dubawa shi ne: Ta yaya aka samu hakan? Matsalar daga wurin ta ne, ko
kuwa daga wurin sa ne?
Abin nufi a
nan shi ne: Me yiwuwa matar tana da wata matsala ta damuwa ko rashin lafiya ne shi
ya sa take gudun saduwar. Ko kuma ba ta da sha’awar saduwar da namiji ne,
saboda ta riga ta shiga ƙungiyar masu maɗigo
da suke neman yawaita a wannan zamanin! (Allaah ya kiyaye).
Haka kuma
matsalar tana iya kasancewa saboda dalilin yadda shi ya fara mu’amalantarta a
karon farko ne, ko kuma yadda yake mu’amalantarta har a yanzu. Watau, me yiwuwa
a karon farko da ƙarfi ya yi mata, ba tare da kulawa da ƙoƙarin
janyo hankalinta ko motsar da sha’awarta
ga buƙatar
ba. Ko kuma me yiwuwa ba ya damuwa da ko ita ta samu nata biyan buƙatar
ko ba ta samu ba. Shi dai kawai idan ya gama buƙatarsa shike nan, babu ruwansa!
Shi dai
mu’amalar saduwa a tsakanin ma’aurata, kamar yadda masana suka yi bayani, ba
abu ne da za a ɗauke
shi irin yadda wasu sabbin angwaye da amare suke ɗaukarsa
ba: A riƙa
neman shi a kullum da safe, da rana, da yamma, da daddare kamar ibadar Sallah
da Salati! Abin da babu wanda zai ƙwace maka, kuma babu ranar da zai ƙare
har zuwa mutuwa, menene na haɗama
ko gaggawa a kansa?
Shi ana zuwa
masa ne a lokacinn da buƙatarsa ta taso kawai, kamar dai abinci. Amma sai ka ji wasu a
kan haka wai har magani suke sha, domin ya nuna mata shi namiji ne! Ko wai ta
nuna masa ita ba ƙaramar mace abar wasa ba ce! Irin wannan shi ke janyo matsala
a tsakanin ma’aurata
idan ba a samu daidaito a tsakaninsu ba.
Maganin wannan
dai ma’aurata su zauna, ko dai su kaɗai
ko tare da wani amintaccen masani, domin bayar da shawarwari masu amfani a kan
wannan matsalar. Muhimmi dai su riƙa la’akari da yanayi da halin buƙata ko rashinta daga
juna a kowane lokaci, kafin neman biyan buƙatar. Ita dai mace, kamar yadda na faɗa a baya, a kullum ta
zama a cikin shirin biya wa mijinta buƙatarsa.
Al-Imaam
Muslim (1403) da Al-Imaam Abu-Daawud (2151) da Al-Imaam At-Tirmiziy (1158) sun
riwaito hadisi sahihi daga Sahabi Jaabir (Radiyal Laahu Anhu) cewa:
Watarana
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ga wata mace a waje,
don haka sai ya tafi gida wurin matarsa Zainab (Radiyal Laahu Anhaa), ya same
ta tana aikin jeme wata fata. Sai ya biya buƙatarsa a wurinta, sannan ya fito wurin
Sahabbansa, ya ce:
« إِنَّ الْمَرْأَةَ تُقْبِلُ فِى صُورَةِ شَيْطَانٍ ، وَتُدْبِرُ فِى
صُورَةِ شَيْطَانٍ ، فَإِذَا أَبْصَرَ
أَحَدُكُمُ امْرَأَةً فَلْيَأْتِ أَهْلَهُ ، فَإِنَّ ذَلِكَ
يَرُدُّ مَا فِى نَفْسِهِ »
Ita mace tana
fuskantowa a cikin siffar shaiɗani
ne, kuma tana juyawa a cikin siffar shaiɗani
ne. To, idan ɗayanku
ya ga wata mace, sai ya koma gida ya sadu da matarsa. Wannan shi zai mayar da
abin da ke a cikin ransa.
Wannan ya
nuna:
(i) Mace a
gidan mijinta tana zama a cikin shirin biya masa buƙatarsa ta saduwa ce a
duk lokacin da ya yi buƙatar hakan daga wurinta.
(ii) Zama
cikin wannan shirin ba ya hana mace ta ci gaba da wasu ayyukanta na yau da
kullum a cikin gidan, kamar yadda ya same ta tana gyara fata.
(iii) Ba
daidai ba ne mace ta zauna haka nan kawai, ba ta aikin komai sai latsa wayoyi
da kallon tashoshin nuna fitsara iri-iri.
(iv) Wannan
shi ke haifar da matsaloli a cikin gidajen auren za munan yau, domin ma’aurata
suna yin watsi da haƙƙoƙin da suka zama wajibai zuwa ga abubuwan da ba su da
muhimmanci a rayuwarsu!
(v) Bai
halatta mace ta tsara wa mijinta wasu abubuwan da wai sai ya gama yi mata su,
sannan ne za ta amince ta biya masa buƙatarsa ba.
(vi) Idan kuma
ta tsaya a kan yin hakan, to bayan zunubin hana shi haƙƙinsa, akwai kuma
taimakawa wurin buɗe
ƙofar
yin zina a wurin mara tsoron Allaah, musamman ma a wannan zamanin.
(vii) Sannan
yaya matsayin irin wannan matar zai kasance a lokacin da mijin ya samu damar
auro wata matar kirkin da ba ta yi masa irin wannan?
Allaah ya faɗakar da mu.
Kallon
tsiraici domin wai samun biyan buƙata da kwantar da sha’awa shi ma matsala ce.
Domin bayan ya saɓa
wa koyarwar Addini, akwai kuma koyon munanan ɗabi’u
da halaye a cikinsa. Wani namijin kan iya ƙoƙarin kwatanta duk abin da ya gani a cikin
waɗannan hotunan,
wanda kuma ba gaskiya ba ne, domin tsara su ake yi a fim kawai. Wannan shi ke
kai wani ga cutar da jikinsa, ko kuma ma ga hallaka kansa. Kamar yadda wata
macen ma kan kasa gamsuwa da mijinta, saboda bai iya yi mata irin yadda ta ga
ana yi a cikin irin waɗannan
fima-fiman ba!
Abin da ya ke
magani dai shi ne, duk mu ji tsoron Allaah kawai a cikin zamantakewarmu a
gidajen aurenmu. Kar mu sake mu bi hanyoyin son-kai, ko cutar da abokin zamanmu
ba da haƙƙi
ba. Kar mu ɗauki
al’amarin saduwar aure ya zama kamar abincin da babu makawa a rayuwa sai an ci
shi, mu riƙa
yin haƙuri
da juna, mu nisanci shaye-shayen magungunan ƙarin ƙarfi, ko masu janyo ƙarin
sha’awar saduwa ba da
wata larura ko umurnin masana ba.
Amma idan duk
waɗannan hanyoyin da
makamantansu sun gaza kawo maslaha a tsakanin ma’aurata, to suna iya ɗaukar matakin rabuwa da
juna, ko dai ta saki ko kuma ta khul’i a ƙarƙashin koyarwar Sunnah.
Da fatar
Allaah ya zaunar da gidajenmu lafiya, mu iya haƙurin tarbiyyar ’ya’yanmu
tarbiyyar musulunci sahihiya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.