𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam
Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, mene ne hukuncin mijin da yake buɗe wa matarsa ‘blue film’
don su kalla tare?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Musulmin
gaskiya shi ne wanda ya miƙa wuya gaba-ɗaya, watau ya jawu ga bin dokokin
Ubangijinsa (Tabaaraka Wa Ta’aala) cikin imani da tsoro da neman lada a
koyaushe kuma a cikin komai na rayuwarsa, tun daga farkawarsa daga barcin safe
har zuwa komawarsa barci da dare. Yana yin iyakan ƙoƙarinsa
wurin kaucewa bin zugar shaiɗaninsa
ko sha’awar ransa wurin aikata saɓo
matuƙar
iyawarsa. A kullum yana tsoron Ranar Tsayuwarsa a gaban Mahaliccinsa wanda zai
tambaye shi a kan yadda ya yi da gaɓoɓin jikinsa da Allaah ya
ba shi amanarsu, kamar ta irin waɗannan
kalle-kallen da ya yi, ko ya nuna aka kalla. Allaah ya ce:
إِنَّ
ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولࣰا
Haƙiƙa ji
da gani da zuciya kowanne daga waɗannan
abin tambaya ne a kansa. (Surah Al-Israa’i: 36)
Sannan kuma
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi tsawa a kan wannan
mummunan aikin kamar inda ya ke cewa:
« لاَ يَنْظُرُ الرَّجُلُ إِلَى عَوْرَةِ الرَّجُلِ ، وَلاَ الْمَرْأَةُ
إِلَى عَوْرَةِ الْمَرْأَةِ ، وَلاَ يُفْضِى
الرَّجُلُ إِلَى الرَّجُلِ فِى ثَوْبٍ وَاحِدٍ ، وَلاَ تُفْضِى
الْمَرْأَةُ إِلَى الْمَرْأَةِ فِى الثَّوْبِ الْوَاحِدِ ».
Kar wani
namiji ya kalli al'aurar wani namiji, kuma kar wata mace ta kalli al'aurar wata
mace. Kuma kar wani namiji ya lulluɓa
da wani namiji a cikin maya fi guda, kar kuma wata mace ta lulluɓa da wata mace a cikin maya
fi guda. (Sahih Muslim: 794).
Idan har ya
hana wannan a tsakanin namiji da namiji ko a tsakanin mace da mace, ashe ya
hana shi a tsakanin namiji da mace a wurin kallon tsiraici ko lulluɓar shi ya fi cancanta,
don shi ya fi tsanani.
Kuma ko ba
komai wannan kallon yana daga cikin hanyar kusantar zinar da Allaah ya hana a
cikin maganarsa cewa:
وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا
Kuma kar ku
kusanci zina, haƙiƙa ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israa’i: 32).
Domin kuma a
cikin hadisin Muslim (6925), Annabin Rahama (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya ce:
« الْعَيْنَانِ زِنَاهُمَا النَّظَرُ ، وَالأُذُنَانِ زِنَاهُمَا
الاِسْتِمَاعُ ، وَاللِّسَانُ زِنَاهُ
الْكَلاَمُ ، وَالْيَدُ زِنَاهَا
الْبَطْشُ ، وَالرِّجْلُ زِنَاهَا
الْخُطَا ، وَالْقَلْبُ يَهْوَى
وَيَتَمَنَّى»
Idanu zinarsu
ita ce: Kallo, kunnuwa kuma zinarsu ita ce: Saurare; harshe kuma zinarsa ita
ce: Magana; hannu kuma zinarsa ita ce: Kamawa; shi kuwa ƙafa zinarsa ita ce:
Tafiya; sannan kuma zuciya ita ke sha’awar
hakan kuma take nemansa.
Bayan duk waɗannan, akwai waɗansu munanan ta’adi da
wannan kallon ke haifarwa ga masu yinsa, kamar haka:
(1) Zunubi ne,
wanda yake ƙeƙasar da zuciya, ya nisanta bawa daga Allaah Ubangijinsa, ya
afkar da shi a cikin fushinsa da azabarsa tun daga nan duniya kafin makoma
lahira.
(2) Aikata
wannan laifin yana nisantar da Mala’iku daga bawa, ya kusantar da shaiɗanu gare shi, masu ƙara
zuga shi da tura shi ga dukkan hanyoyin hallaka.
(3) Kallon
tsiraicin waɗanda ba
su ba, yakan sanya ma’aurata su fara kushe wani abu na halittar tsiraicin da
Allaah ya yi wa junansu, wanda kuma hakan ke iya kai wa ga ƙiyayya
da ƙyamar
juna.
(4) Bayan
kallo fima-fiman babu abin da ke biyo baya sai ƙoƙarin kwatanta irin abin da aka gani. Don
haka ba abin mamaki ba ne su fara ƙoƙarin saduwa ta dubura ko ma ta baki,
kamar yadda suka gani!
(5) Rashin iya
aiwatar da saduwa daidai da abin da suka gani a fim, wannan kan kai su ga
da’awar rashin gamsuwa da juna, mai kai wa ga rashin jituwa da yawan faɗa, kuma mai kai wa ga
rabuwa.
(6) Ƙoƙarin
aikata yadda suka gani a cikin fim kan kai ga cutar da jikkunansu ko ma
hallakarsu, domin sukan manta da cewa abin da suka kalla shirya shi kawai aka
yi, ba haƙiƙa ba
ne.
(7) Yaɗuwar waɗannan fima-fiman a yau na
daga cikin dalilan yawaitar zinace-zinace da fyaɗe
da sauran ayyukan assha a tsakanin jama’a manya da yara, maza da mata, har ma
da dangi da ’yan uwa.
(8) Masu irin
wannan aikin sukan zama abin koyi ga wasu ma’aurata irinsu, ko kuma ma ga
yaransu, waɗanda kan
fara koyon wannan ɓarnar
tun suna ƙanana.
A ƙarshe
dai abin da yake wajibi a kan duk wanda ya faɗa
a cikin irin wannan masifar ita ce:
(i) Ya yi
saurin nadama da tuba ya daina wannan aikin, ya nemi gafarar Ubangiji Ta’aala
tun kafin zuwan mutuwarsa.
(ii) Ya lalata
duk wani abu na waɗannan
fima-fiman da ke tare da shi, ya daina kallonsu, ya daina nuna wa wani daga
cikin mutane, ko da kuwa matarsa ce.
(iii) Ya ƙara ƙoƙari
wurin janyo hankalin duk wanda ya san shi ne ya koya masa kallon waɗannan fima-fiman, don shi
ma ya tuba kamar yadda shi kansa ya tuba.
Allaah ya
tsare mu daga dukkan zunubai na fili da ɓoye,
ya gafarta mana gaba-ɗaya.
WALLAHU A'ALAM
Shiekh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.