Ticker

6/recent/ticker-posts

Assalatu Khairun Minannaumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin akwai ingantaccen hadisi akan fadin ASSALATU KHAIRUN MINANNAUMI acikin kiran sallar asuba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

An Samu faɗin ASSALATU KHAIRUN MINANNAUMI a kiran Sallar Asuba acikin hadisai masu yawa, kuma ingantattu daka cikin Wadannan hadisan akwai:-

1- Hadisin Abu Mahazura Allah yaqara masa yarda ya ce; Na kasance Inaiwa Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam kiran sallah, Na kasance akiran Sallar farko, idan nace ( Hayya Alal Falah) Ina faɗin Assalatu Khairun Minannaumi Sau biyu. Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha ilallaah. Abu dauda (500) da Nisa'i (647) Albani ya Ingantashi acikin Sahihu Abu dauda.

2- Daka Ibnu Umar Allah yaqara yarda dasu ya ce: ( Akiran Sallar farko bayan Hayya Alal falah ana fadin Assalatu khairun Minannaumi Albani ya ce: Addahawi ya fitar da shi (1/82) da sanadi Kyakkyawa, kamar yanda Alhafiz yafada acikin Talkees (3/169) Saboda Haka Assalatu khairun Minannaumi Abune Sananne acikin addinin musulunci wanda saboda ingantuwarta tafi qarfin wani yai kokwanto ko inkari akan shar'antuwarta.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments