Ticker

6/recent/ticker-posts

Makauniyar Shari'a [Kashi na 4]

Ya Allah ina godiya da bisa dukan ni'imominka a gareni. Yanda na fara Lafiya ka ba ni ikon gamawa Lafiya. Alkhairan da ke cikinsa ka ba ni ladansa, sharrin da ke ciki ka yafe min.

Allah ka dauka Alkalamin marubuta a duk in da suke

Gaisuwa ta musamman gareku na hannu dama ta.

  • Besty (Sarat Alkasum)
  • Maman Amatullah
  • Ummu shkura
  • Fadila Sani Bakori
  • Maman Sharifa
  • Mamashu
  • ABBA Yakubu
  • Dan Salma
  • Da Autan Jarumai.

Waɗanda ban samu damar kiran sunansu ba, duk ina mika sakon gaisuwata a gare ku.

Yayyena abun Alfaharina

  • Hadiza
  • Hussaina
  • Hassana
  • Maryam

Gaisuwa ta mussaman gareki

Anty Zulai, mutan Kano, surukar Auta na.

Jarumai Writers Association, marubuta masu aiki da Jarumta wajen Fadakar da Al'umma

MAKAUNIYAR SHARI'A

MAKAUNIYAR SHARI'A

IKILIMA ADAM (Kyauta daga Allah)

09069080725 ko +22953726162 (Whatsapp kaɗai ban da kira)

Marubuciyar da ta nishaɗantar da ku a littattafanta kamar haka:

  1. Kai ka ja wa kanka
  2. Kanwata
  3. RAI DAYA (Jan Za ki)
  4. RUDANI (mai tafiya daukan rai)

Da sauran su.

Yanzu ga ni ɗauke da sabon littafina mai suna MAKAUNIYAR SHARI'A

****

SHAFI NA SHA UKU

Suka bata amsa da mun kawo muku sammaci ne daga kotu ". Cewar Dsp Faisal Haruna yana mai kallon yanda Yasmin ta rikice lokaci daya.

Yasmin cikin zazzare idanu da tsoro da fargaban abunda ba ta yi zato ba ta ce " a kan wani laifi ake karar mu". Muryanta na rawa ta karashe zancen, nan da nan taji cikinta ya murda gudawa na son barke mata, cikin matse kafa da fitar hayyaci da sassauta murya kada Mamy taji ta ce " Yallabai munyi muku kama da yan daba ne, ko barayi ko yan Kidnapping ne, nayi tambaya kunyi shiru kuna zuba min idanu ". Ta karashe zancen murya na rawa.

Dps Faisal shi da yaransa kallonta suke kana suka kwabe baki, cikin tsare gida Dsp Faisal ya ce " ko alama sam baku kama da barayi ko yan daba da sauransu asalima ke Yasmin kina kama da Mahaifin Alhaji Isah, watau Alhaji Taufik Sharifai, sai de hausawa sunce kama da wane bata wane, shari'a sabanin hankali ce, amshi takarda sammaci daga kotu inda ake zargin ku ba ya'yan Alhaji Isah ba ne sannan kuna zaune gidansa, kunki tashi, kunsan akwai rayuwa akwai mutuwa kada ya mutu aci gadonsa bayan ba ya'yansa ba ne ku ". Ya kai karshen zancen tare da mika mata papper.

Tana karban papper daga hannunsa suka juya suka tafi suna girgiza kai, ita kuwa cikin daukan salati ta koma dakin kamar an mata albishir da ranar mutuwarta, tana karasa dakin taga Mamy tsaye kikam, tsayuwar da bata taba ganin ta yi ba duk tsawon rayuwarta irin tsayuwa me nuni da zuciyarta ta kyakyashe babu maganar sauran kuka a gabanta. Cikin razani Yasmin ke fadin " Mamy dan Allah ki zauna na ga sai jijjiga kike, kinsan lafiya be isheki ba pls dan zauna in miki bayani ". Ta karashe zancen tare da ƙoƙarin kama hannun Mamy. . .

 Mamy kauda hannunta ta yi tana mai kallon Yasmin cikin idanu.

" naji komai kuma na shirya da muje kotun dai, ba mu da karfin daukan lauya ". Juya kwayar idanunta sama ta yi tana mai cigaba da fadin " muna da babban Alkali ne shi ne Allah, kuma nasan baze kyalemu ba zebi mana hakkinmu ". Ta karashe zancen idanun ta na kallon saman cikin rawar jiki

 

" Yasmin kada wannan ya daga hankalin mu, daga yau mu fara hada kayayyakin mu, muna jin karshen zaman kotu sai mu kama gabanmu ". Kukan da take dannewa ne ya kamata batare da ta ankare ba.

 Cikin kuka ta ce " Alhaji Isah yau ni A'isha ni ce na haifa masa shegu, mutumin da nice silar arzikinsa bayan wahalar da muka sha na rayuwa ni dashi, mahaifinsa yabar masa makudan kudade na gado, yan uba suka hana masa kudin har kudaden suka salwanta, da kudin sana'ata na atamfofi na bashi ya yi jari dashi a lokacin ko naira dari yana gagararsa amma yau ya nuna nice banza, ya shirin tona min asiri a garin nan, in mun bar gidan nan ina za mu raba ". ta karashe zancen cikin kuka mai cin rai da bakin ciki.

 " Yasmin kiramin yayyenki su Fauziyya da safiya amma pls kar ki kira Firdaus dan tanada ciwon zuciya kuma tsohon ciki ne da ita, sun san halin da ake ciki, dan susan yanzu ba suda gidan Uba.

Yasmin sosai ta fara jin takara tsanar Alhaji Isah, cikin kuka ta ce " zan ari wayar baba mai gadi in kirasu, amma pls ki bari anty Firdaus ta san halin da ake ciki".

Mamy cikin damuwa ta ce " ba za ki gane ba ne, Firdaus mijinta ba me karfi ba ne kuma unguwar su akwai nisa da cikin gari, baya ga haka batada isasshen lafiya, so kike tashin hankali ya sa nakuda ya tashi lokaci beyi. . . . . ". Shiru ta yi jin muryan Firdaus tana shigowa daga dakin sanye cikin doguwar riga fuskarta babu walwala bakinta na rawa ta ce" da Haihuwa da aure da mutuwa da kaddara lokaci gare su, in kinga na haihu ki tabbatar lokaci ne ya yi mayan". Ta ƙarshe zancen tare da kaiwa Mamy runguma.

Cikin kuka ta ce" Mamy duk abin da ake ciki na sani, ina daga bakin kofa ina jinku, Mamy dan Allah ku in gudu da ku cen unguwarmu akwai wani dakin bukka sai na kama muku haya, Mamy nasan ba za ki taba yarda ba, da wallahi cikin gidana akwai daki sai ku zauna ".

 Mamy dago Firdaus daga jikinta ta yi cikin kuka ta ce"Firdaus mun gode da ƙoƙarinki amma kiyi hakuri bazan iya zama inda kike so ba, hakama bukkah ". Ta karashe zancen cikin raunin murya.

Firdaus zama bakin tsohuwar katifar dakin ta yi dakyar saboda nauyin cikinta, babbar wayarta mai kirar Samsung Galaxy ta fiddo tare da dannawa Fauziyya kira domin sanar dasu halin da ake ciki.

Cikin kuka da tashin hankali ta shiga baiwa Fauziyya labari daga haka sukayi sallama cikin kuka. .

Cen ɓangaren Fauziyya sosai ta fita hayyacinta har mijinta daya shigo dakin sai tambaya yake lafiya kuwa? amma ina ta kasa ba shi amsa ban da hawaye ba abin da ke kwaranya daga idanunta, kuka take mai nuni da bakin ciki, tun suna yara suke cikin kangin wahala har sun girma abun gaba yake.

 

ABUJA

Umar Faruk a gwarinfa zaune gidan Alhaji yana baiwa shukoki ruwa, cikin rashin walwalan rashin ganin ogansa ya zauna tsakar gidan yana karewa kyawun Gidan da tsaruwarsa kallo, amma a zuciyarsa yana fadin ai Gidan Alhaji Isah yafi wannan haduwa da komai, ganin sake sakensa bashi ne mafita ba, ya sa je gun mai gadi ya aro waya, daman ya saka kati aciki, dan gefe daya ya raba yana kiran number Bala mai Gadi na kwatano dan a kan wayarsa ake samun su, jin switch off ya sa hankalinsa tashi ba kadan ba, ya dade yana gwadawa abu daya suke maimaita masa.

So yake bayan sun gaisa ya sa a nemo masa lambar ogansa a cen garejinsa. Da wannan tunanin ya dan ji sanyi a ransa.

 Mai da wayar ya yi ya fara yunkurin dan fita waje ya dan ga gari, kasantuwa kullum yana cikin gida, shi kuwa be saba da hakan ba.

 

Sosai jikin Mama ta ji sauki, likita har ya ba su daki, Mansura ce zaune a gefenta tana chat, da dukan alamu ta yi nisa dan sai darawa take ita kaɗai, jin karar tsayuwar mota a farfajiyar gidan ne ya sa ta tashi domin lekawa ta window, cikin jin dadi take kallon Mansur da Ridwan sun fito daga motocinsu, dukansu suna sanye cikin shadda brown, " waouh ". Ta furta ya yin da ta ga Rid yana musabaha da wasu likitoci da dukan alamun akwai sanayyah sakaninsu, haka ma Mansur haka sukayi ta musabaha da likitoci maza masu wucewa, cikin fara'a da sakin fuska. Wayar Rid ne ya fara ring, hannunsa ya zira cikin aljihun wandonsa, yana zaro wayar ya kai dubansa a kan fuskar wayar, Ganin commissiner ne ke kiransa ya sa shi komawa da baya baya tare da dawowa kusan inda ya yi parking din motarsa.

Bayan sallama da sukayi bayan ya daga wayar daga cen bangaren, Commissiner da ke zaune a office kana computer na gabansa ya ce" Dsp Ridwan Muhammad Mai nasara dan Allah akwai aikin da zaka fara muna tun agida kafun ka dawo aikinka".

Ridwan jin ya ambaci kalmar aiki ya san aiki ne mai girma wanda shi kaɗai ake bai wa, ba su taba bashi me saukin yi ba, fesar da numfashi ya yi tare da jingina jikin motarsa kana idanunsa na kan Mansur da ke cen tsaye yana jiran isowarsa. Tattara nutsuwarsa ya yi wajen amsa wayar.

" Inajinka". Shi ne amsar da ya bayar yana kallon Mansur da ke daga masa hannu alamun zeyi gaba yana jiransa acen, shi ma kai ya daga masa hakan ya sa Mansur yin cikin asibitin.

Dagacen bangaren Commissiner ya ce " Ridwan nasan kasan Haruna Karfin Iko ".

Gaban Ridwan sai da ya bada rasss !!!!!! jin ya ambashi sunan. Nan take yaji kamar yana son ya kara ajiye aikin. Commissiner ne ya katse masa tunani ta hanyar fadin " ya kayi shiru ina magana?".

" Am sorry wai na tsaya saurarenka ne, kwarai kuwa nikuwa nasan karfin iko, wannan karan me kuma ya aikata? ". Ya yi tambaya cikin kadawar harshe.

 Nan dai Commissiner ya fara zayyano masa dalilin kiran nasa da kuma abin da yake son ya masa. Rid cikin gamsuwa da bayanansa sukayi sallama.

 Kasa barin wajen ya yi yana mai cigaba da jingina jikin motarsa, yatsarsa daya abaki yana juya kalaman Commissiner, jin wayarsa ta kara yin rîng ne ya sashi kai dubansa akai inda yaga Mansur ne ke kira, be daga ba illah kawai hanzarta yin cikin asibitin ya yi.

Mansura tana ganin Rid yabar wajen motarsa cikin hanzarinta tabar wajen window tare da bude jakarta dan karamin turarenta ta dan fesa ajikinta, tare da mai da sauran cikin jakarta, duk abin da take Mansur be san tanayi ba dan hankalinsa ya tafi a kan Mama da ke tari, ban da sannu ba abin da bakinsa ke furtawa. Ƙarar bude kofa ne ya tabbatar musu da Rid ne ya iso.

Mansura nan da nan ta fadada murmushinta tana mai jiran isowarsa, shi kuwa yana shigowa dakin fuskarsa ba walwala sosai dan wayar da ya gama ya sa duk kuzarinsa ya tafi, da sallama a bakinsa ya karaso tsakiyar dakin, cikin ban girma ya durkushe yana mikawa Mama gaisuwa. Mama cikinsanyin murya ta amsa masa tana murmushin ganinsa. Yana tashi daga durkushen kallon Mansura yake yanda take washe masa hakora kamar me tallan maklin ya sa shi tabe baki kamar ana masa dole ya ce" Mansura yan makaranta ya me jiki?".

" Jiki da sauki Alhmdulillah ". Cewar Mansura cikin yauki.

Lumshe idanunsa masu kwarjini ya yi kana ya dan budesu a kan Mansur da ke masa murmushi yana mai nuna masa kujerar kusa dashi, ba musu ya zauna, suna taba hira shida Mansur.

Mansura cikin iya bariki ta ce" wai kunga yanda kukayi kyau kuwa, bara na ɗaukeku hoton tarihi".

Ridwan najin haka kamar ya fasa ihuu dan kwata be yarda yan mata su ɗauke shi hoto, wata zuciyar ta raya masa ai babu komai, ita ma kanwarka ce. Da haka ne ya sa shi ɗan yin murmushin yake, ita kuwa soma daukarsu hotuna ta yi inda cikin dabara ta samu ta dauki Ridwan shi kaɗai batare da Mansur ba, cikin jin dadi ta koma ta zauna, shi kuwa Ridwan ji yake inda zega wayarta dasai ya dauka ya goge hotunansa tass.

 

Ridwan sai bayan isha'i ya dawo tsararren gidansu, babu abin da ke dawainiya dashi da yawuce gajiya, tafiya yake sam ba'a jin takunsa har ya kusa karasowa falon inda ya ci karo da Mamy da Aminiyarta Madina suna hira da dukan alamu sunyi nisa sosai, cikin zallan takaici da damuwa Mamy ke fadin " ai yanzu Ridwan be da gindin zama tunda kanwar uwarsa, Maman Mansur ba lafiya". Ta karashe zancen cikin takaici.

Madina kam sosai ta jinjina lamarin cikin ban hakuri ta ce " kedai barshi wanda yaki sharar masallaci ai zeyi na kasuwa, ban da tsabar gulma da kinibibi da neman suna yanzu ace. . . . . ". Ragowar kalamanta ne ta kasa karasawa ganin Ridwan ya raba ta bayansu ze fice, kallo daya ya musu cikin kasa da murya ya ce " sannunku da hutawa ". Mai da kallonsa a kan Mamy da shi din take kallo ya yi, cikin ban girma ya ce " Mamy ina yininku?!! ". Daga haka ya sakai ze fice ba tare da ya jira amsa ba.

Muryan Madina ya ji tana fadin " dan dakata Ridwan, baka sanni ba ne ita kuwa mamy bazaka zagayo ka gaishemu cikin mutuntawa ba ". Ta karshe zancen tana maganar zuci inda take fadin " Ai Rid sai na Aure ka wannan yaron haka ya kara yin kyau da haduwa". Ta karashe zancen tana kallon yanda yake tafiyarsa kamar besan da ita ba, dan ko waiwaye beyi ba bare tasa ran ya ji ta.

Cikin zallan mamaki Mamy ta ce" ai baze tsaya ba, na tabbatar in wasu kama gari ne da tuni ya tsaya wurin ".

 Bebi ta kansu ba, kai tsaye ya yi sashinsa domin a zuciyar sai fadi yake ban da lokacin amsawa wancen makirar matar amsa.

Madina cikin kaduwa ta ce " Anya Yaron nan beji firarmu ba? ". Ta kai karshen zancen cikin ayar tambaya.

Kar kada kai Mamy ta yi cikin shakku ta ce beji komi ba, ai haka yanayinsa yake musamman in har yana tare da gajiya. "

Kwabe baki Madina ta yi inda suka ci gaba da tattaunawa, itakuwa Madina babban burinta ta ga Rid dan ya tafi da imaninta, yanda kasan yau ne ta fara ganinsa.

Ridwan na shiga dakinsa ko wankar da ya saba beyi ba, hakanan ya fada gado ya kwanta, maganganun Commissiner ne kaɗai ke masa zarya cikin kwanyar kansa, haka nan ya ji sam baya jin ze iya barci, tashi ya yi ya zauna inda ya dauko laptop ya sa a gabansa, wayarsa ya dauka ya fara daukan wasu bayanai da numbobi yana mai kara matsowa da laptop din gabansa, ganin baya gani dakyau ya sa shi tashi dauko médical glass dinsa, sanyashi ya yi fara fara kallo dakyau. . .

Acikin computer sa wani kayataccen Gida ne yake kallon na Alfarma, yana kallon tsarin gidan da komai, kana ya kai dubansa a kan hoton da ya bayyana a gabansa ganin An rubuta Amatullah Haruna Karfin ikoh, zazzare idanu ya yi ganin hoton Amatullah ya bayyana, zumbur ya miji tsaye bakinsa na rawa cikin kidima kamar ba shi kaɗai ne a dakinsa ba ya ce " Wannan Yar kauyen. . . . . . . . . . . . .

Muje zuwa

Makauniyar Shari'a taku ce

Share and comment pls

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 

 Sai a lahira

 NA

IKILIMA ADAM

 (Kyauta daga Allah)

Kai ka Jawa kanka

Kanwata

Rai daya jan za ki

Rudani

RAYUWAR Ma'aurata

Kaicona

Duk wanda kuke so sai ku tuntuɓeni a kan wannan lambar

09069080725

Akwai rangwame sosai ga me buƙatar dukansu.

Kar ku manta Makauniyar Shari'a littafin kuɗi ne free page ya kusa karewa.

SHAFI NA HUDU

Wannan Yar kauyen Daguzau ce? me ya kawo hoton ta a nan " yake tambayar kansa cikin zallan mamaki, hannunsa na zoomin din hoton, nan da nan ya fara tariyo abin da ya faru a kauyen da kuma irin takaicin da ya daya kwasa akanta, cikin kadawar tunani yake ƙoƙarin nazari a kan lamarin anya kuwa ita ce? rasa me bashi amsa ya sa shi kara nusawa cikin tunanin son gano gaskiya, sai hamma yake. ciki kasala yake toshe bakinsa hade da fara lumshe idanunsa, idanunsa na cigaba da tariyo masa hoton cikin computer a kasalance ya yarufe laptop din, ba tare da ya kashe komi ba. Wannan karan kwanciya ya yi ba tare da ya yi adu'oi da ya saba na kwanciya barci ba. Yadauki awa biyu yana barci inda sosai barcin yau ya masa ma mugun kamu . Ahankali daga waje ake turo kofar dakinsa, sanin da aka masa baya kulle kofarsa sai weekend, suna tura kofar sannu ahankali cikinsandasanda suka fara leko kai, ganinsa yana kwance ya baje yana barci, alamun ya yi nisa sosai dan ko kwanciyar kirki beyi ba a bakin gado ya kwanta.

Mamy da Madina kallon juna su kayi suna rarraba idanu a kan dakinsa da sam babu takarce, computer da ke gabansa suke kallo, cikin kasa kasa da murya Madina ta ce " Saratu ko za ki iya fita dakin dan Malam yace ke Mahaifiyarsa ba za ki iya aikin ba dole sai an samo wani, da muje waje samun wani gwamma na yi miki mun rufawa juna asiri". ta yi magana cikin kasa da murya. Mamy jin hakan ba ta yi musu ba ta fice tare da jan kofar ahankali ta fita cikinsanda. Ita kuwa Madina tana ganin fitar Mamy ta karaso tsakiyar dakin, gab da shi ta karaso tana karewa kyakyawar fuskarsa mai haske da sheki kallo, sajen fuskarsa yanda suka kwanta lub lub take bi da kallo, bata san sanda ta furta " Ma sha Allah", Kasar zuciyarta. Kallon yanda yake barci bil hakki take tana kwabe baki, cikin karfin hali da ƙoƙari irin nata, ta zauna kan gadon nasa ahankali, hannayenta masu kaushi ta sanya ahankali tana shafa fuskarsa, shi kuwa Ridwan acikin barcin ya dan kara motsawa hakan ya sa ta yi hanzarin cire hannunta, durkushewa ta yi da kanta tana ƙoƙarin sumbatarsa a baki, kamar yana sane sai ya kifa a gadon. Ahanzarce ta dago tana kallon ikon Allah cike da fargaba, mutum sai ka ce mai ido hudu, ganin yanda yake a kife hannayensa duk ya sake su bakin gado, cike da ƙoƙari da rashin tsoro ta kamo hannunsa daya tana shafawa ahankali, wani bakon yanayi ta ji yana fisgarta ji take tsigar jikinta na ta shi, nan take ta ji yarrrrrrrrr a ilahirin jikinta, abin da zata iya rantsewa duk auren da ta yi a baya bata taɓa jin hakan ba, jikinta na tsuma kamar mazari ya sa ta yi hanzarin sakin hannunsa wanda ya janyo hannun buguwa da bakin gadon. Daga cikin barcin ya ji zafin buguwa, hakan ya sa ya yamutsa fuskarsa, tare da fara yunkurin juyowa, Madina na ganin réaction dinsa son tashi.

 Ahanzarce cikin azzama ta labe bayan labule cikin tsananin tsoro da fargaba.

Shi kuwa zaune ya yi bakin gado yana kallon hannun nasa da ya buge din, cikin jin inda ya bigen na masa zafi, ya rike dai dai inda ke masa ciwo yana matsawa ahankali tare da ciza labbansa, tsaki yake ta jerowa ta yanda akayi ya kwanta ba Alwala da adu'oi, tashi ya yi yana mika tare da kai dubansa kofar dakinsa cikin idanunsa mai ɗauke da tarin barci, ɗauke ganinsa daga nan ya yi ya dawo dashi kan labulen dakinsa da yake gani dishi dishi tare da tsurawa wajen idanu sosai ba kiftawa, rike da kungunsa ya ke bin wurin da kallo sosai, kana ya kai dubansa a kan kasan labulen. Har ya fara yunkurin tashi domin zuwa wurin, Madina na ganin ya tashi kamar ze nufo inda take ban da innalilahi babu abin da take maimaitawa wani uban zufa ne ya karyo mata lokaci daya.

Ganin ya canza akalarsa zuwa banɗaki, ya sa ta fara sauke nauyayyen ajiyar zuciya. Tana jin sanyi na ratsata ganin ya shige banɗaki.

 ganin ya shiga, kwararan ajiyar zuciya ta ringa sauke wa akai akai, kana cikinsauri da hankali ta bude kofar ta fita tana haki, koda ta karaso wajen Mamy zuru zuru da idanu take bin Mamy da kallo cikin boye tsoronta hade da zama kan kujera ta ce " wallahi Saratu Danki Ridwan Aljanunsa suna da karfi sosai, amma a karshe dai sunce sai kin taimaka min wajen gudanar da aikina ". Ta karasa zancen baki na rawa.

Mamy da zallan mamaki take kallonta, cikin hanzari ta ce " wani Irin taimako zan baki, fadi kawai kinsa baze gagara ba".

" Inason mu sanyawa Ridwan maganin da ze sanya ya fita hayyacinsa na tsawon awa biyu ko uku, amma acikin abincinsa". Ta karasa zancen cikin bukatuwa.

Mamy cike da faduwar gaba ta ce " ai Ridwan kwata kwata tunda ya yi wayau baya cin abincin Gidan nan, kuma ko da yana ci taya zan amince a sumar min da yaro har tsawon wannan lokutan, kinsan bazan yarda ba gaskiya, Malamin naki besan aiki ba ". Cewar mamy cikin takaici.

Madina kuwa ranta ya soma baci, cikin fushi ta dau jakarta da ke kan Centre table tana fadin " ai ke ce kika ce bakya son ya yi aure yanzu kuma ɗan ana neman hanyar da baze taba sha'awar yi ba kinzo kina fadamin maganganu, wannan ba komai kike min ba illah gorin haihuwa, ai na dauka Ridwan ni ma dana ne za mu iya cika burinki ashe kallon muguwa kike min, bayan ke ce kika bukaci hakan ". Ta kai karshen zancen tare da kama hanyar fita daga kayataccen falon, ahanzarce Mamy ta bita cikin damuwa ta fara bata hakuri, tare da tabbatar mata Ridwan baya cin abincin Gidan, da wannan bayanan ne 🔥ta sauko tare da cin alwashin kullum zata ringa zuwa sanya masa magani na kwana bakwai daga nan shi ke nan babu shi babu Aure sai dai a lahira. Mamy taji dadin hakan daga gare ta inda suka dawo falon tare da ci gaba da tattaunawa.

Cotonou

 

Ranar Alhamis

Yasmin tsaf ta gama harhada kayayyakinsu domin zama acikin shirin ko ta kwana, Fauziyya da Safiyya da Firdaus ko wannen su ya zabga uban tagumi, cikin karfin hali Fauziyya ta fesar da numfashi cike da bakin ciki ta ce" ai yaran Alkali sune suke kawo sammaci daga kotu ya akayi Dsp ne ya kawo bayan ba huruminsa ba ne?". ta yi tambaya cikin tsananin bacin rai.

" Ai abu in akace babu Allah aciki ko meye ai zaka gani, sun wakilci yaron Alkalin ne dan su zo su ganewa idanunsu ya muke ciki ". Cewar Safiyya tana hura.

" Ni fa tunda abun ya kai ga haka wallahi banki inci Uban Alhaji Isah ba, haba ! ga abun magana ace ba za muyi ba, kuma wallahi ko da bashi ne sai mun harhada mun dauki lauya mu ma ". Cewar Firdaus cikin fada.

 Fauziyya ta amshi zancen da fadin " ai dole mu dau lauya, in ba haka ba cutar zata yi yawa kusan shekara goma be tare da Mamy shi be sake ta kuma yana kiran mu shegu ze fada mana ta inda aka same mu ". ta yi magana cikin fusata.

 

 Duk hirar da suke Mamy da Kakarsu Mariya suna jin su babu wanda ya tanka musu domin, su kansu kukan zuci suke daga zaunen.

Yasmin da yanzu taga zata iya tofa bakinta cikin maganar cikin muryan kuka ta ce " wallahi ankara kawo mana wani takardan sammaci daga yaron Alkali cewar sa ranar monday za'a fara zaman kotu ". Ta kai karshen zancen a raunace.

Gabakidaya zazzare idanu suka yi har da kaka Mariya, cikin kuka kaka Mariya ta ce " Ni na dauki cikin Isah har tsawon wata tara da kwana tara, na shayar dashi, na ci kashin sa da fitsarinsa, in har ina hakkin akansa ya zama dole na masa baki ". Juya kwayar idanunta ta yi zuwa sama alamun za ta yi mummunar furuci akansa. ta ci gaba da fadin " Isah kamar yanda kasani kuka kasa iyalinka da yayayenka kuka ya Allah ya. . . . . . . ". Cikinsauri Mamy tasa tafin hannunta ta rufe mata baki, cikin kuka take girgiza kai baki na rawa ta ce" kar ki tsine masa wallahi ze kara lalacewa, wallahi inason Isah, kuma nasan kinfini sonsa, sai de ni da ke mun tsani halayayyensa, Isah mutum ne da nasani mai tausayi da jinkai, nayi imani inhar Isah na ne wallahi ko da yaran nan nazo Gidan nan ze rike min su, amma shedan ya masa kidan ganga baya ji baya gani". ta karshen cikin kuka.

Kaka Mariya kuka take harda shidewa, murya na rawa ta ce " A'isha ki barshi ya kara lalacewa kuma ni Mariya na ce Isah sai kagani". Ta kai karshen zancen a raunace tana jin komi zata iya masa.

dan kullum da bakin ciki suke kwana suke tashi.

Shigowar me Gadi da waya ne da sallama a bakinsa ya sa sunyi shiru, tare da basa amsa cikin kasa da murya, tashi Yasmin ta yi dan amsar waya daga hannunsa, dan ta san be wuce Umar ne ke kira, tana karba cikin hanzari ta bawa Mamy wayar tare da gayamata me kiran nata.

Murya a raunace Mamy ta fashe da kuka ya yin da ta kai wayar saitin kunnenta domin bawa Umar labarin halin da ake ciki domin yanzu tafi buƙatar ganin ya dawo gida.

Cen Ɓangaren Basma.

Zaune take bakin gadonta Alhaji Isah na gefen ta yana harhada wasu takardun aikinsa, cikin fara da sakin fuska ya ce " Basma ga wannan takardan na baki mallakar gidana da ke unguwar Gbegamey dan nasan yanda kike son gidan nan ". Ya yi furuci cike da begenta.

Cike da tsananin jin dadi ta ce " tu es sûr? ma'ana ka tabbatar, ya bata amsa da " oui ma chérie". Ma'ana kwarai kuwa masoyiyata. cikin jin dadi ta kai masa kiss a goshi, sannan cikin iya bariki ta ce " kai de dan Albarka ne wallahi ga shi Allah na fiddaka tsakiyan makiya, kuma ranar monday hummm A'isha zata gane illah cin amanar miji". Ta kai karshen zancen cikin yatsine fuska.

Kallonta yake kamar me nazarinta, sannan ya yi dan jim kamar yana son fadin wani abu ko tuno da wani abu da yake ta mancewa tsawon rayuwarsa, hakanan ya ji be ji dadin furucinta ba, a fili kuma ya ce " Hummm kedai Allah ya kaimu kowa ma ya huta. Dan ni da A'isha kotu ce zata raba.

Cikin yauki ta kara narkewa jikinsa har takardunsa suka fadi kasa reras, idanunta masu wutar fitina ta sauke cikin nasa suna kallon juna, murya cike da shagwaba ta ce " wai yaushe zaka saki A'isha ne, na ga babu Aure tsakanin nagari da mugu da". ta yi furucin tana cunno baki gaba.

Bakin nata yake bi da kallo, nan da nan yaji kalmar sakin ta soke shi har kasar zuciyarsa, ta maza ya yi tare da fadin " Basma bana son firan A'ishah pls maganar saki a barta sai nan gaba, zan mata har saki uku". Ya karashe zancen yana juya yin kalamanta.

Ita kuwa ranta babu dadi amma kuma ta dau alwashin nan gaba shi ne ze zo mata da maganar ya saki A'isha ta karashe tunaninta tana yar dariya.

Gwarinfa

Kashe gari Ranar Juma'a.

Da sanyi safiya Amatullah ta fito daga dakinta, tana sanye cikinsabuwar dinkinta doguwar riga atamfa da ya zauna mata daram ajikinta har shap dinta da hip dinta duk suka bayyana, sosai dinkin ya mata kyau wanda ya kara mai da babban yarinya, Hasina ta dinka mata bisa ga umarnin karfin Iko. Cikin gidan har teloli gare su da kasuwa masu siyar da kayan miya, su atamfa leshi, harda gareji akwai cikin gidan, sauran kuwa ba'a cewa komi.

Yau ne karo na farko da Amatullah ta sanya kafafunta a farfajiyar Gidan, cikin zallan mamaki take kallon yanda gidan yake ci kamar kasuwa, kuma sam babu hayaniya kowa harkan gabansa yake, sautin zazzakar murya a nan karatun Alkur'ani mai girma, ta ji daga dayan bangare na Gidan, hakan ya sanya ta fara bin inda take jiyo karatun ahankali tana tafiya bakinta na dan motsawa kamar duk abin da yake karantowa ita ma tana maimaita shi abakinta. Sai da ta iso gab da madaidacin massalaci me kyaun haduwa da tsaruwa cikin zallan mamaki ta ce " massalaci acikin gida? ganin babu me bata amsa ya sa ta yin shiru, barin wannan tunanin ta yi ta fara ci gaba da tafiya, har ta iso inda karantun ke tashi, jin muryan dalibai yan amshi na tashi, kusantowarta wurin yana dai-dai da tsananta bugawar zuciyarta, ahankali ta matso kofar massalacin tare da da lekawa domin ganin abin da ake. Zararan idanunn ta ware a kan fari kyakkyawan dattijo da ya tankwashe kafafunsa yana sanye cikin farar jallabiya fuskarsa ɗauke da gilashi, cikin kaduwa da al'ajab take masa kallon kamar ta taɓa ganin fuskar sa, muryan dalibai ne daga ciki ya katse mata tunani tana jin daga ciki wata daliba tana fadin " Malam ya hukuncin wanda ya labe yana gulma bayan ba'a san da zamansa a wurin ba, ina nufin yana son yaji kwaf". ta yi tambaya yanda kasan sako ta aikawa Amatullah.

Amatullah zazzare idanu ta yi tana nazarin wannan tambayar anya be da hadi da ita kuwa?, wata zuciyar ta raya mata ai karatunsu suke ba su san da zamanki ba, fesar da numfashi ta yi tare da yunkurin komawa cikin gidan, muryan Malam ne ya dakatar da ita, jin yana fadin " gulma ba shi da kyau da yawan gulmace gulmace ake koyon munafunci, sannan akwai gulma mai fa'ida irin mutum ya zo wuce wa yaga ana karatu sai ya tsaya dan ya saurara domin ya amfana, na shi akwai lada kam a wajen Ubangiji ' wallahu Ahlam". Ya bada amsa yana mai cigaba da karatunsa.

Sanyayar ajiyar zuciya Amatullah ta sauke jin amsar da ya bayar.

Tana ganin ana ƙoƙarin tashi ne ya sa ta fara yunkurin barin wurin har ta karya kwana zata fice, taji sautin muryan Malam daga sama yana fadin " dakata ". Ya yi furucin yana mai kusanto inda take cikin kasaita da kamalarsa, innalilahi wa'inna ilairajun ". Ya shiga maimaita da bakinsa, kana cikin rawar murya ya ce. . . . . . .

Makauniyar Shari'a taku ce

Comment and share

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 Na

 IKILIMA ADAM

 (Kyauta daga Allah)

09069080725 whsap

SHAFI NA SHA BIYAR

Kana cikin rawar murya ya ce dakata Baiwar Allah ". Furucinsa ya yi dai-dai da tsayuwarta. Karasowa gab da ita ya yi yana ƙoƙarin ganin ta juyo dan babu abin da yake bukata sama da yaga fuskarta.

Ita kuwa daga tsayen take ji wani irin faduwar gaba mai karfi, a hankali ta juyo domin ganin wanda ya tsayar da ita, kwalalo idanu ta yi ganin Malam ne wanda ta gani yana koyar da karatu, cikin rudewa take kallon kyakkyawan dattijon fari sol wanda yake nuni da a kuruciyarsa ya yi tashen kyau, bangare daya na zuciyarta tana hasaso mata kamanninsa kamar ta taɓa ganinsa ko a hoto ko kuma a mafarkinta.

Malam ganin ta tsura masa idanu ta shiga duniyar tunani ne ya sa shi katsee mata hanzari ta hanyar fadin.

" Yan mata ya sunanki? Kuma tun yaushe kike Gidan nan, me ya sa kika labe kina jin karatu bayan kinada damar shigowa daga ciki ". Ya kai karshen zancen yana jin zuciyarsa na tsinkewa abun da yake son tabbatarwa ya gani da idanunsa, hawaye ne suka samun daman cika a idanunsa, cikin hanzari ya sa tissu ya dan goge hawayen ba tare da ya bari Amatullah ta fahimci halin da yake ciki ba.

Rau rau da idanu take kallon sa rasa amsar da zata basa ya sa ta fadin " a yi hakuri Malam daga yanzu zan fara zuwa karatu dan banyi nisa sosai ba ". Ta karshe zancen cikin cool voice dinta.

 Shi kuwa sosai ya shagala da kallonta cikin boye abin da ke kasar zuciyarsa ya ce " baki fadamin sunanki ba".

" Suna na Amatullah amma ainahin sunana Faridat, yan kauye na kirana da yar wahala". Ta karashe zancen cikin tsantsar kuruciya.

" Innalilahi wa'inna ilairajun ". Malam ya shiga maimaitawa ba kakkautawa hakan ya sa Amatullah, dan tsoracewa har ta fara tunanin ko duka ze mata ne, ahanzarce tabar wurin ta shige sashin su, ta bar shi a nan tsaye.

Shi kuwa yana ganin ta fice ya lallaba ya samu wuri daga nan gefe dakali ya zauna babu abin da kwanyar kansa ke juyawa sai kalaman Amatullah.

Amatullah tana karasawa daga cikin falon, cikin rudewa taga Ƙarfin Iko zaune a kan kujerar falo ya daura kafafunsa daya kan daya yana kallon tashar Tauraruwa in da ake sanarwa da neman agaji a kan wani yaron kauyen wanda rai yake hannun Allah, sakamakon bugawar da yan daba suka masa. Amatullah cikinsanda sanda ta karaso falon murya na ta rintsina gabansa.

Ina wuni! Abba ". ta yi furucin idanunta na kan TV da yake kallo ba tare da ta jira amsar sa ta tashi tsaye cikin kidima take kallon Salim a cikin TV shida iyayensa yanda suke kuka suna neman taimako Naira miliyan Biyar domin fitar da salim kasar waje. Cikin gigicewa da fitar hayyaci ta ce " innalilahi wa'inna ilairajun Salim dinannnn". Yanda ta yi furucinne ya sa karfin iko dawo da kallonsa akanta cikin zallan kaduwa da kalamanta.

Duka hanayyenta ta daura akai ya yin da take kallon Salim a cikin TV yanda ya rame ya kare baka ganin komai nasa sai kasusuwa ma'ana ya koma kamar skeleto. Cigaba da jero salati take tana kuka kasa kasa idanunta cike da hawaye masu dumi. Ƙoƙarin barin falon take izuwa dakinta, taji daga cikin TV ana fadin dan Allah ataimaka ma wannan yaron dan rayuwarsa tana cikin hatsari, ga Mai buƙatar taimaka masa ya zo Asibitin Aminu Kano". Tana jin karshen zancen ta fara sauri sauri wajen yin sashinta. Azafafe taji ƙarfin iko ya rike hannunta wanda ya yi sanadiyar juyowarta ba shiri, yanda ya rike hannun nata take kallo da kuma yanda ya tsareta da idanunsa masu kwarjini. Dago kai ta yi tana kallonsa, cikinsassaita nutsuwa ta ce " ka sake min hannuna wlh rikon da kamin akwai zafi". Ta magana cikinsanyin murya. .

Kyawawa fuskarta yake karewa kallo na tsanaki, kana cikin damuwa kasar zuciyar, saman fuskar ba yabo ba fallasa ya ce " waye salim? meye alakar ku kuma me ya sa kike masa kuka, me ya sa za ki ambaci Salim dinki a gabana, Amatullah kinsan me kike fadi kuwa ayanzu fa kin kama hanyar zama budurwa kuma wanda ze aure ki kike yabon wani agabansa". Ya karashe zancen yana hura kofar hancinsa.

Ita kuwa hannayen da ya sa ki take kallon yanda ya yi ja, bata kara yarda sun hada idanu ba kanta a kasa ta ce " Salim yace inna girma ze zauna damu ya gina min gida ni da papy". Tana kai karshen wannan zancen Ƙarfin Iko rintse idanunsa ya yi da karfi domin sosai yaji tsananin kishinsa ya motsa.

Taci gaba da fadin " shi ne wanda ya taimaka muna Lokacin da aka nemi aka kashemu, dole nayi kuka domin ina tabbacin wannan halin da yake ciki saboda mu ne, kuma bakina ni da papy baze iya fadin Alkhairan da Salim ya mana, dole nayi kuka yana cikin wani hali ban da ikon taimaka masa ". Ta karashe zancen tana mai jin tsayuwar ta isheta.

" Zan bada millon goma a masa magani, ki saurareni zuwa gobe, amma a daren yau zan kawo kudin su kwana adakin ki ". Ya yi furucin yana mai jin tsananin kishinta, amma kuma yana son taimakawa Salim kodan ya faranta mata rai.

Amatullah bata tsorata jin ze bada kudin ba dan ta san yana kudin da ba suda iyaka yanda ta samu labari gun Hasina, murmushi mai sanyi ta yi wanda yakara bayyana zallan kyawunta, cikin jin dadi ta fara masa godiya shi kam hakan da ya ganta ba karamin sanyasa cikin nishadi ya yi ba.

Bayan magrib

Amatullah zaune a tsakiyar dakinta muraja'a take yi na karatun da Papy yake koyar da ita na surori.

 Shigowar Hasina hannunta ɗauke da jaka ne ya sa ta kai dubanta akanta tana sanye cikin doguwar riga mai tsantsi baki tare da bakin hula akanta, cikin jin dadi ta kai ayar karatun ta tare da mata sannu da zuwa cikin fara'a. Hasina ta ce.

" Amatullah yar gatan Haruna karatu ake?".

"Eh karatu nake, kuma nakai aya". Cewar Amatullah.

" Ma sha Allah, Allah ya bada lada ".

" Ameen Nagode sosai". Fuska ɗauke da yalwatccen murmushi.

Numfashi Hasina ta fesar tana karewa Amatullah kallo na musamman kana cikin muryanta ta dabi'a ce ta ce " muga kitson da Nana ta miki, sannan ga sako Haruna yace in kawo miki zakuyi Magana". Ta karashe zancen tana mai kallon kitson kan Amatullah data bude mata cikin hanzari ta furta.

"Ma sha Allah".

" Nagode kwarai ". Ta kai karshen zancen tana mai amsar jakar daga hannun ta.

Sun shagala suna hira tsakaninsu wanda har ya sa Amatullah darawa dan sosai Hasina ke ɗebe mata kewar Papy.

. . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .

Umar Faruk bakin sa na rawa yaje gun mai gidansa tare da fada masa buƙatarsa na son tafiya garinsu, Alhajin ya tausaya masa matuka hakan ya sa ya ba shi kudin mota tare da fadin " in komai ya daidaita dan Allah ya dawo ze kama masa aiki a kamfaninsa. Sosai Umar yaji dadin hakan ya kuma masa godiya tare da zama a cikin shirin gobe asabar ze bar garin. .

 

Ridwan sosai yake shiri bayan Sallah isha'i yanda kasan ze je wurin shakatawa, wandon treequater ya sanya tare da brown din rigarsa cotton, mai daukar idanu, anutse tattare da kamalarsa ya gama shirinsa tsaf, gaban mirror yaje yana taje kansa kana cikin hanzarinsa ya fesa turaruka masu kamshi ajikinsa ta cikin madubi yake kallon kansa shi kansa ya san ya yi kyau, jin wayarsa na rîng ne ya sa shi hanzarta sanya flat din takalminsa hade da fita domin ya san be wuce Mansur ne. . .

Cikinsassarfa yake taka matakalan step din, wanda ya jawo hankalin dukan kannensa da suke falon kallon sa, yana saukowa ya yi dai-dai da fitowar Mamy ita da Madina da idanu suke binsa ganin yana gaisawa da kannensa, kana ya tsaya su na dan taba hira da kaninsa Faisal tare da fada masa ya shirya gobe tare da za su fara fita aiki. Kannensa mata kuwa bayan gaisuwa be kara ce dasu komai ba. Ƙoƙarin ficewa yake daga falon ya ji murya Madina tana fadin " Haba Ridwan baka ganmu ba ne". Cak ya tsaya ba tare da ya waigo ba, cikin kasa da murya ya ce sannunku da fitowa iyayena ". Tare da fara yunkurin fita falon.

Murya Madina yaji again tana fadin " na ga kamar sauri kake dan Allah ka saukeni gida, motata ta lalace". ta yi magana cikin jiran amsa.

Cak ya tsaya yana nazarin kalamanta kana cikin muryansa ta dabi'a ya ce " zan baki kudin Napep zan baiwa me Gadi ya baki, dan ba hanyarmu daya ba". Yana kai karshen zancen ya fice daga falon.

Da idanu suke bin keyarsa da kallo daga su har kannensa, Faisal ne ya yi murmushi domin ba karamin burgesa takun Ridwan yake ba.

Madina rike da baki suke kallon juna da Mamy, kana cikin hanzarinta ta ce " Mamy bari nabi sahunsa nasan ma ze saukeni". ta yi furucin tare da fita ba tare da ta jira amsa ba.

Su Anisa me za suyi in ba dariya ba, ita kuwa Mamy ta fara tsorata da Lamarin Madina a kan Ridwan kasa magana ta yi hakan ya sa ta samu wuri ta zauna cikin ya'yanta.

Madina tana karasowa ya yi daidai da kunna wutar motarsa ze fice daga Gidan, hannun da take masa ne ya bashi damar danna madanni sauke gilashin motar, kana ya dawo da kallonsa a kan ta jin tana fadin " Dan Allah Ridwan ka sauke ni diyar antina ce ba lafiya kafin na samu napep da aiki ". Ta karashe zancen cikin magiya ".

Kallonta yake tuno da ai ita ma kamar Uwarsa take hakan ya sa ya ce " to shiga kofar baya ".

" Haba dana kai ba drever ba gwamma in zauna gaban zefi ". Ba ta jira cewarsa ta shige ta gaban motar, tare da cika kujerar da manyan mazaunata.

.

Ya kai mintuna biyu be tada motar ba lissafi da nazarin matar yake, barin wannan tunanin ya yi tare da tada motarsa, daman ya san Gidanta a lugwai yake hakan ya sa be tambaye ta kai tsaye ya fita da hancin motar daga cikin gidan.

Sun sha tafiya da ya kai akalla minti ashirin, wayarsa ta hau ruri yana dubawa yaga Mansur ne daga wayar ya yi yana mai cigaba da tukinsa cikin kasa da murya ya ce" Mansur ina hanya zan ajiye Mamata Madina Gida ne, ka jirani ina nan zuwa ka ce wa Mama pls aidole inzo cin abinci". Ya karashe zancen tare da katse wayar.

Madina sosai ranta ya ba ce jin ya ce mata Mama, cikin boye damuwar ta kakalo murmushin dole tare da fadin " wai kai yaushe zaka yi Aure ne Ridwan?". ta yi magana domin ta san amsarsa be wuce baya son jin zancen aure kamar yanda ya saba.

Cikin tsantsan mamaki da rudewar tunani a bazata ta ji ya furta.

" Ai na kusa Aure kwanan nan, baki ga na fara gyaran dayan sashin cikin gidanmu ba to a nan zata zauna Amarya". Ya yi furucinsa cikin tabbatarwa.

Zazzare idanu Madina ta yi ƙoƙarin yin magana take, taji yana fadin " mun fa iso". Ya yi furucin yana mai nuna mata da jiransa ake.

Jiki a sanyaye ta sauka tare da rufo kofar, muryanta na rawa ta ce " Rid Nagode Allah ya maka Albarka ".

Be bata amsa da Ameen ba sai dai yabita da kalmar sai anjima. Daga haka yafice daga unguwar.

Ita kuwa cikin hanzarinta ta karasa gida tana mai jin takaicin tambayar da ta masa tana kuma rantsewa da buwayar Ubangiji sai ta Auri Ridwan ko ana ha maza Ha Mata.

Rid mintina sha biyar ya dauka kafin ya isa Unguwar su Mansur, me Gadi na ganin motarsa ahanzarce ya wangale masa babban gate din Gidan.

Cusa hancin motar ya yi yana mai daga mai Gadi hannu, tare da zarcewa farfajiyar Gidan.

Parking space ya ajiye motar, fitarsa daga motar ya yi dai-dai da karasowar Mansur shi ma irin shigar Ridwan din ya yi komi irin daya, murmushi kwance a fuskokinsu suka kama hannayen juna, bakin Mansur na rawa ya ce " kai Abokina har gida kaje kai kawar Mamarka ka barni da jiranka gashi ina jin yunwa".

" Wallahi matar ce ta cika naci ".

" To ai ita ma Mamarka ce dole ta yi iko dakai ".

 " Hummm ni karshe ma saida tasa na fadi abin da bashi ne ba".

 " Ahaf ka ce kayi kwaba tunda kasan karya ba dabi'arka ba ce Lallai ka tabbatar kayi abin da ka fada mata ". Ya karashe zancen suna mai karasowa falon kusan a tare.

Suna isa falon ya yi tozali da Mansura da ke sanye cikin doguwar riga atamfa ba karamin kyau ta yi da shigarba.

Cikinsakin fuska da walwala take fadin " oyoyo yaya Ridwan har ka iso". Furucinta ya yi dai-dai da fitowar Mama cikin riga da zani atamfa Mai kalan ruwan kasa.

Ita ma da murmushi take fadin.

" Lale marhaba da Dana ". Murmushi ya sakar musu dukansu yana mai cigaba da tafiya izuwa kayataccen falon, cike da ban girma ya gaishe da Mama kana cikin dan sakin fuska yake amsa gaisuwar Mansura.

 Bayan taba yar hira da Mama ne yake fada mata Aure zeyi cikinsatin nan kuma sha'awar yin Aure ya zo masa ne a daren. ".

Mansura da ke ƙoƙarin shan lemun acikin kofin glass ba tare da ta ankare ba ta saki glass din ya fadi saman tayis jika kake. . . . . . . . . . . . . .

Makauniyar Shari'a taku ce

Share and comment pls

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 

Sai a lahira

09069080725

SHAFI NA SHA SHIDA

Ta saki glass ɗin saman tayis kas kas ya tarwatse a kasa, "subuhannallah" ta furta cikin zazzare idanu tana kallon yanda kofin ya tarwatse, cikin kidima ta dago kai tare da kai dubanta a kan Ridwan shi da Mansur har da Mama, kowannensu kallon Al'ajab yake mata.

" Hummm am sorry wallahi ban kula ba ne bansan yanda akayi ya subce daga hannuna ba " ta yi magana murya kasa kasa kamar me shirin yin kuka.

Ridwan kar kada kai ya yi cike da kulawa tare da fadin " ba dai ki ji ciwo ba ko? " girgiza kai ta yi alamun a'a cikin kasala rashin kuzari da tsananin faduwar gaba, kama hanya gun dauko tsintsiya da mopper tayi. Da idanu yake bin ta da kallo, ganin yanda take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, mai da kallonsa a kan su Mansur ya yi tare da zama kan dîner table din, cike da jin dadi yake kallon tulin abincin da Mansur ya cika masa a plate, sosai ransa ya biya ganin tuwon shinkafa miyar taushe da naman rago, kamshi abinci sosai ya daki hancinsa cikin yanayinsa na walwala yake kallon Mansur da shi ma din shi yake kallo cike da burgewa da dan guntun murmushinsa ya ce " wannan abincin na mu uku ne ko? ".

 " Ina ce kaga nawa nima a gaba". cewar Mansur yana dariya.

 

 " Haba Mansur kasan duk sona da abinci bazan iya cinye shi ba, bata abinci kuma ba shi da kyau".

 

 " in ka rage akwai wacce zata ci sauran".

 

 Danpp jim ya yi alamun tunani kafin ya dau cokali pme yatsu ya fara kai lallausan tuwo a bakinsa, dadin abincin pyasa ko kara kallon Mansur beyi ba ya fara ci cike da nutsuwa.

pp

P Mansura bayan gama mopper dan gefe ta samu ta labe tana kallon yanda yake cin abinci, jajayen labbansa ba karamin rikitata suke ba. Mama data fito cikin corrido da mamaki take kallon Mansura na leke, guntun murmushi ta yi kana ta karaso tare da tsayawa bayanta ita ma tare da kai dubanta an yi a kan abunda take kallo, ga mamakin ta Ridwan ta gani, murya a sanyaye tare da yin kasa da murya ta ce " haba Mansura yanzu in ya ganki kina masa wannan kallon ai sai ya daina zuwa cin abinci gidan nan pls banason hakan ". ta yi magana cikin bacin rai.

 A furgice Mansura ta waigo tana sauke ajiyar zuciya, cike da jin kunya ta ce " Hummm ai ba shi nake kallo ba ". Ta karasa zancen tare da fita tsakar gidan, domin jiran fitowarsa.

 Da idanu Mama ta rakata tana girgiza kai.

 Bayan kammala cin abinci, sun sha lemuka ba laifi kana Ridwan ya fara shirin yiwa su Mama sallama tare da fada mata ta shirya cikin watan nan zata je Umra. Mama ba karamin farin ciki ta yi ba, gefe daya kuma sai ta bata rai kamar ba abun Alkhairi ya mata ba, cikin bayyanar damuwar fuskarta ta ce " Rid Nagode kwarai da dawainiyaya da kake dani Allah ya saka maka da Alkhairi, sai de Ridwan bazan ji dadi ba ace Mahaifiyarka wacce ta haifeka ko Umra bata taɓa zuwa ba, ni kam nayi hajji ya kai hudu, Umra ba iyaka, pls ka tai. . . . . . . . . . . ".

 " Dakata ". Shi ne farkon abin da ya furta kana cike da jin zafi tuno masa da Mamy ya ce.

 " Mamy Mahaifiya ce, kunsan an ce Hajji kiran Allah ne, ina ga Allah ne be kirata ba " ya kai karshen zance tare da ficewa domin baya son ta kara yin wata magana da zesa ta ga rauninsa.

 Daga Mansur Har Mama da idanu suka raka shi, kana Mansur cikin kasa da murya ya ce " Mama pls dan Allah ki kyale Rid tunda baya so a masa maganar Mamy, yana da ilimi addini dana zamani, kuma an ce ruwa baya tsami banza ke dai mu dage da saka shi cikin addu'a ze fi ". Ya karasa zancen tare da bin sahun Ridwan din.

 Mama kam shiru ta yi tana kallon fitar Mansur.

 Ko da ya isa compound din gidan Hango Ridwan ya yi shi da Mansura tsaye jingine a jikin motarsa da dukan alamu magana suke a yanda ya hango Ridwan na magana ya tabbatar magana yake mai cike da damuwa, jan burki ya yi tare da samun wuri daga gefe ya zauna yana jiran Mansura ta bar wurin.

 Mansura cikin murya kuka ta ce " Ridwan zan fada maka sirrin zuciyata wallahi ina sonka tun ranar dana yi wayau nasan kaina dan Allah ka kaunaceni kar ka ce mun nayi hakuri ".

 Ridwan in ransa ya yi dubu ya baci daman wannan kalmar zata fada masa tun dazu take ta jan zancen da tsawo.

 Kallo daya ya mata cikin kasa da murya ya ce " ni kam koda kika ji nace zanyi aure Yar Daji zan aura banason wayayyiyar mace, kuma Nagode da kulawa". Yana kai aya, ya fara neman Mansur da idanu, hangosa ya yi yana tahowa, ita kuwa Mansura aguje ta bar wajen tana rusa kuka mai cin rai, domin kuwa ta tabbatar samun Rid ba abu me sauki ba ne.

 Mansur na karasowa babu bata lokaci shi ma ya shiga tashi motar domin masa rakiya rabin hanya.

Benin République

Yau takama ranar Litinin inda a yau ne Alkali ze fara sauraron kararraki da ya shafi Isah Sharifai da Uwargidansa A'isha Muhammad.

Tun safe kowa ya shirya daga Fauziyya, Firdaus Safiyya, hatta Yasmin duk sun shirya tsaf, Kaka Mariya tana sanye cikin kodaddiyar atamfarta, kowannen su fuska babu walwala, cike da damuwa Mamy ta ce " wai ko ya labarin Umar ne anya kuwa ya taso kuwa haba ai ya kamata ace ya karaso? " ta yi furucin cin damuwa.

Fauziyya cikin kwantar mata da hankali ta ce " yanzu haka be samu damar tasowa ba ne, kawai a kyaleshi Allah sheda ne baya garine shiyasa be samu zaman kotu ba. Kokan ta gama rufe baki wayarta ce ta fara ruri inda wakar Hamisu breker ke tashi waka mai taken  ku dakata makiyan mu bayanzu, mai son ganin bayan mu ba yanzu ba ahanzarce ta daga ganin number Nigeria ce ta san be wuce Umar, cike da zalla mamaki da Al'ajab taji dan sanda na fadin " Umar yana heatquater na yan sanda bisa babban case da aka dade ana nemansa shekara da shekaru dan haka duk sanda kuka shirya kuna iya tahowa Abujan". Dan sanda na gama magana ya katse wayar.

 Dagacen kallon Umar Yake yanda yake kuka mai cin rai, murya na rawa ya ce " yace wallahi ko tsuntsun ban taba kashewa ba bare mutum dan Allah ku fahimceni iyayena suna bukatata a dai dai wannan lokacin " ya kai karshen zancen yana kuka mai tada hankali.

Yan sanda ko ajikinsu kowannensu babu wanda yakara bi ta kansa.

Dagacen bangaren su Fauziyya Innalilahi wa'inna ilairajun suke ta maimaitawa cikin tashin hankali Fauziyya ta ba su labari, nan dakin ya dau salati, cikin tsananin tashin hankali Mamy ta ce " Fauziyya dan Allah kubani poison in sha na mutu, kila in samu sauki a cikin zuciyata ". Ta karashe zancen tana kuka.

Dukan su kuka suke, Yasmin cikin kukan da ya ci karfinta ta ce " Mamy wai mu kaɗai ne muke rayuwa cikin kunci ne?" ta yi furucin murya a raunace, babu wanda ya bata amsa a cikin su kowannensu da idanu suka bita ganin lokacin na gab da karantowa ya sa suka tashi domin tafiya kotun, Mamy da taimakon Fauziya take tafiya domin saida ta tallafeta ajikinta tana kuka kasa kasa.

Ɓangaren Alhaji Isah shi da Basma da ya'yanta sun shirya tsaf cikin fararen shadda gezner kowannen su sosai dinki ya masu kyau da cikar haiba, cike da jin dadi da walwala suka fito harabar gidan, kokan su karaso har su Yasmin sun fice.

Basma da mijinta mota daya suka shiga, ya'yan nasu kuwa a dayan mota suka shiga inda babbar diyar Basma Nasra ta tuka motar.

Court.

Tun daga sauke su Yasmin a kan mashin din da ya kawo su suke karewa hadadden court din kallo, cike da fargaba da tashin hankali, Mamy ke kallon yanda lauyoyi ke kai kawo a wajen wanda yake nuni da ahanzarce suke domin lokaci na gab da cika.

Soma rarraba idanu suke dukansu suna neman inda za su ga lauyar su, Yasmin cikin damuwa ta ce " Mamy kinganta cen tana magana da wani lauya" ta yi magana tana mai nuna Lauyar da yatsarta. Gabadakiya cike da hanzari suka yi wajen lauyan ganin tana shirin shigewa filin hall din.

 Suna isa wajen ta, cikin damuwa suka zagayeta tare da soma tambayarta inda za su zauna.

 Lauya Hadiza Ibrahin da ke sanye cikin kayan aikinta, kallonsu take Cikin yanayinta da ke nuni da rashin walwala ta ce " ku kwantar da hankalinku shi Shari'a da kuke gani sabanin hankali ce, ni Hadiza Ibrahin zanyi iya ƙoƙarina ganin na kwato maku yancinku". Duk wannan bayanan da harshen French take yinsa.

 Ko ba komai Mamy da ya'yanta sun dan ji sassauci damuwar su dayan bangaren kuwa hankalinsu ya tafi a kan Umar da ke cen a tsare. Suna ƙoƙarin shiga hall tare da barister ya yi dai-dai da isowar Basma da mijinta da ya'yanta harma da yan uwanta. Da idanu suke binsu da kallo tare da yin gaba suka wuce su.

Kaka Mariya cike da damuwa take mamakin halin Isah, cikin takaici take fadin " ku shiga daga ciki ko".

Bayan kowa ya shiga an zazzauna, Alhaji Isah a sace yake kallon A'isha da ita da Mariya, da yaga suna ƙoƙarin dago Kai sai ya yi wuff ya ɗauke idanunsa.

Isowar Alkali ya sa gabakidaya kowa tashi kamar yanda aka saba, Alkali na zama kowa ya zauna. .

 Cike da kamala mai gabatarwa ya mike tsaye file cike a hannunsa da dukan alamun akwai kararraki bayan nasu. Cike da kamalarsa yake fadin " Barka da zuwa ya mai girma mai Shari'a. Karar farko da za mu fara shi ne a kan Alhaji Isah sharifai da mai dakinsa A'isha Muhammad, wacce yake zargin ta haifa masa ya'yan da ba nasa ba, kuma tana zaune masa acikin gida da daurin gindin Mahaifiyarsa". Yana kai karshen zancen ya kai file da ya danganci karar gaban Alkali.

Alkali Auwal Hassan dage gilashin idanunsa ya yi yana mai kallon file din da ke gabansa, kana ya dauka a hannunsa hakan ya sa mai gabatarwa samun wuri ya zauna.

 Alkali cikin daga murya ya ce.

 " Lauyan mai kara ya gabatar da kansa". Yana kai ayar zancen ya yi shiru yana kallon Barister da ya tashi daga zaune.

Suna na Barister Sani Muhammad, nine lauyan da ke kara, tare dani akwai. . . . . ".

 Tashi Lauyan ta yi da kanta tana mai gyara wuyar rigarta, cike da girmamawa ta ce " Sunana Shamsiyya Adam, nice mataimakiyar Barister Sani". Tana gama fadin haka ta zauna.

Alkali sake gyaran murya ya yi tare da fadin Lauyan me kare wanda ake kara Bismillah.

Barister Hadiza Ibrahim cike da kamala ta tashi cikin ban girma ta gabatar da kanta tare da abokin aikinta Mahfouz.

Kotun daukan shiru ya yi na wasu dakiku, Alkali sake bawa Lauyan me kara dama ya yi domin shigar da korafi.

Cike da kwarin gwiwa Lauyan me kara ya mike bakinsa na rawa yace " ya mai girma mai Shari'a Alhaji Isah yana neman a raba shi da wa'yannan ya'yan da ba ta hanyar. . . . . . . . . . . . . . .

Makauniyar Shari'a

Comment and share please.

***

Littafin nan, na kuɗi ne. Da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. Hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Kibiya dari biyar kacal domin samun shiga group na musamman.

Domin Karin bayani a tuntuɓe ni ta wannan lambar 09069080725 ko + 22953726162.

Siyen nagari mai da kuɗi gida.

Post a Comment

0 Comments