Ticker

6/recent/ticker-posts

Makauniyar Shari'a [Kashi na 3]

Ya Allah ina godiya da bisa dukan ni'imominka a gareni. Yanda na fara Lafiya ka ba ni ikon gamawa Lafiya. Alkhairan da ke cikinsa ka ba ni ladansa, sharrin da ke ciki ka yafe min.

Allah ka dauka Alkalamin marubuta a duk in da suke

Gaisuwa ta musamman gareku na hannu dama ta.

  • Besty (Sarat Alkasum)
  • Maman Amatullah
  • Ummu shkura
  • Fadila Sani Bakori
  • Maman Sharifa
  • Mamashu
  • ABBA Yakubu
  • Dan Salma
  • Da Autan Jarumai.

Waɗanda ban samu damar kiran sunansu ba, duk ina mika sakon gaisuwata a gare ku.

Yayyena abun Alfaharina

  • Hadiza
  • Hussaina
  • Hassana
  • Maryam

Gaisuwa ta mussaman gareki

Anty Zulai, mutan Kano, surukar Auta na.

Jarumai Writers Association, marubuta masu aiki da Jarumta wajen Fadakar da Al'umma

MAKAUNIYAR SHARI'A

MAKAUNIYAR SHARI'A

IKILIMA ADAM (Kyauta daga Allah)

09069080725 ko +22953726162 (Whatsapp kaɗai ban da kira)

Marubuciyar da ta nishaɗantar da ku a littattafanta kamar haka:

  1. Kai ka ja wa kanka
  2. Kanwata
  3. RAI DAYA (Jan Za ki)
  4. RUDANI (mai tafiya daukan rai)

Da sauran su.

Yanzu ga ni ɗauke da sabon littafina mai suna MAKAUNIYAR SHARI'A

*******

SHAFI NA TAKWAS

Bayan rigarsa suke kallo, inda yaga an rubuta MASTER da babban baki, nan da nan hantar cikinsa ya kada wani irin gumi mai dumi ya ringa sassarfo masa dukan ilahirin jikinsa, ji kake gab!! gab!! da karfi.

 Ahankali mutumin da ya ba su baya ya waigo yana busan sigari da tashin hayaki, cikin isa da kasaita ya ke taku irin na yan daba hannunsa daya sanye cikin Aljihun rigarsa. Cikin razana Amatullah ke kallon fuskarsa a rikice da tsoro, ta fara ja da baya baya, bakinta na rawa ta ce, " kaine?".

Be bata amsa ba illah cigaba da takunsa ya yi yana nufo inda suke yaransa suna cigaba da bashi hanya har ya karaso daf dasu, cikin tsananin bacin rai da ya bayyana a fuskarsa ya ce, " Ina zaku tafi da sanyin asubahin nan? baku san tun lokacin da nasan kuna zaune a nan wurin na fara gadin ku ba? saboda bana son abin da ze taba min Yarinyar nan, akanta zan iya yin komai. " Ya kai karshen zancen yana kallon Papy da ya dukar da kansa idanunsa a kasa. Kara zuko sigarin ya yi tare da turnuke su da hayaki, silan haka ya sa Amatullah kwarewa har numfashin ta na tsarkewa, nan da nan ta fara tari tana yi tana bubbuga kafafunta sosai hayakin ya shiga hudar hancinta ya hau kanta tare da haddasa mata ciwon kai lokaci daya. Papy lura da yanayin da Amatullah take ciki hakan ya sa ya ajiye kayan hannunsa, hanzarta karban kayan da ke hannunta ya yi tare da ajiye su akasa. Kana janyo ta tare da kai mata wawan runguma da ke nuna tausayi da jin kai na Mahaifi, hannayensa ya sa yana mai dan bubbuga bayanta. Duk abin da suke Karfin Iko na kallon su shi da mabiya bayansa da suke sanye cikin face mask.

 "Zan canza muku wajen zama in kama muku haya acikin gari". Cewar Karfin Iko yana cigaba da tashin hayakin sa.

 " Babu inda za mu bi ka, ka barmu inda ka ganmu, bana bukatar taimakon ka ". Cewar Amatullah cikin kuka mai gunji, ba tare da ta dago kanta daga jikin Papy ba. Karfin Iko cak kalamanta suka cika zuciyarshi da zunzurutun mamaki dan ba zato ba tsammani ya ji amon muryanta cikin kuka wanda ya kara sanya dukan gabobin jikinsa yin sanyi kamar kankara, kana yana mai kara kallon yanda take kara shigewa jikin Papynta da ke rungume da ita yanda kasan sace ta za'a ko raba su. Sanyayyar iska mai kadawa da yanayin sanyin asubahi ya buso su hade da ni'imattacen shaka. Nan da nan Amatullah ta kara matse Papy ajikinta dan sam bata son sanyi.

 Karfin Iko jefar da Sigarin hannunsa ya yi, ya take da kafafunsa kana, ya juyo da fuskarsa, yana mai kara kallon su karo na barkatai, cikin babban muryansa ya ce, " Haba Yarinya kul kada na kara jin kina fadin in fita daga tsabgarku, hakan babban zunubi ne, maganar bakyason na canza muku muhalli, to ku zabi in da kuke son zama zan biya kudin haya ". Yana kai karshen zancen ya fara ƙoƙarin daukar kayan nasu. Papy da sai yanzu yaji ze iya magantuwa ya ce, " na amince ka samar muna wajen zama amma don Allah kar ka kama muna daki da kudin haram. " Ya kai karshen zancen yana mai kallon Karfin Iko cikin idanu.

Gabakidaya wajen sosai har yaran nasa suke juya kalaman Papy, hatta Amatullah ita ma kam kalamansa ta daura a ma'auni tana tankade da rairaya amma sam ta kasa gane inda Papy ya dosa. Karfin Iko murmushi ya yi na gefen baki, kana cikin muryansa na dabi'a ya ce, " na muku Alkawarin da kudin gadona zan kama muku haya, dan ma garin mu ba Abuja ba ne da Gida zan baku ku zauna har iya adadin lokacin da kuka bukaci komawa muhallinku ko in ce Garin ku. " Papy sosai ya ji ya gamsu da Karfin Iko, kallo daya ya masa ya tabbatar da gaskiya yake fadi har kasan ransa. Kafin su bar wajen saida ya ba su dubu ashirin kudin cefane, kana ya ba su kwana uku su zauna ciki shiri za su canza muhalli.

 

Papy komawa suka yi bukkansu suna juya kudaden da ke hannunsu, lissafin rayuwa yake hakan ya sa cikin karfin hali ya ce, " Amatullah ". dago kai ta yi tana kallonsa da idanunta masu tarin barci, kana ta lumshe su tana mai sauraren me ze fadi. " Ina son ki sani duk duniya ban da kamarki, kuma ba zan so ganinki cikin damuwa ba, ina son ki sani rayuwa aduk yanda ka tsinci kanka hakuri ka ke yi, dan haka ina mai rokon ki Please ko babu ni kar ki jefa kanki cikin halaka ".

Kamar an tsinkaye da Allura, afirgice ta bude idanunta, tare da dan murza su tana son tabbatar da abin da take ji daga bakin Papy.

 Nan da nan ta nemi barcin da take ji ta rasa, tattaro kuzarinta ta yi tare da zama tana face dinsa dakyau, damshin hawayene suka cika kwarmin idanunta, cikin rawar murya da tsoro da fargaba ta ce, " Papy bangane me kake nufi ba? Kar ka ce zaka guje ni dan Allah bansan kowa ba sai kai ban taso da uwa ba, ban taso da uba ba, Papy in ka guje min waze jibinci lamurana?. " Ta kai karshen zancen tana sheshekar kuka.

 Dubanta yake cikinsanyin murya da tausayawa da jin kai ya ce, " Amatullah nasha gayamiki akwai mutuwa kin san mutuwa bata sallama Amatullah banason ki sawa kanki damuwa aduk lokacin da mutuwa ta yi awon gaba dani pls my Friday ". ya karashe zancen domin kwantar mata da hankali. Duk da hakan sam bata ji sassauci ba, bakinta na rawa da tsoro ta ce, " mu ba mu da dangi ne? ina mahaifiyata Papy? ba mu da yan uwane, mu kaɗai muke rayuwa ne, kuma kana ta yawan ambato mun zancen mutuwa shin ya kake son na kasance in babu kai?. " Ta jera masa tambayoyi cikin muryan kuka.

Cak wutar lantarki jikinsa ya ɗauke, nan da nan ya ji zufa ya keto masa, cikin kasa da murya ya ce, " Amatullah zan miki takarda full na address din Gidanmu in har kin samu zuwa kawai kice kina son ganin dan Gidan kawai, kuna tozali da shi kawai ki mika mishi papper, amma sai bayan raina ko wani abu ya gifta za kiyi hakan, a nan in sha Allah za ki san tarihinki hatta Mahaifiyarki, batun mutuwa Amatullah ko muna so ko ba mu so tabbas sai ta raba mu ". Ya karashe zancen yana maganar zuci inda yake fadin " Amatullah mun kusa rabuwa daman nasan wannan ranar zata zo, Allah ya sa kije gida lafiya, Amatullah banson barinki adaidai wannan lokacin ba amma tun da na fahimci kin fara hankali babu sauran zama ni da ke Diyata ". ya kai karshen zancen yana mai kuka mai cin rai, shi da ita babu mai rarrashin wani domin kukan ya ci karfinsu.

Benin Cotonou

Alhaji Isah Sharifai, cikin tsadaddan shaddarsa ya fito compund din Gidansa, hannunsa rike da bakar jaka, ba karamin haduwa ya yi ba cikin shigar hash color, hular kansa ya tsaya gyarawa yana mai kallon, Meenat da ke kusanto inda yake murmushi a kyakkyawan fuskarsa. Ahanzarce ta karaso tana mai rike hannunsa mara ɗauke da jakar, Yarinya ce wacce bazata wuce shekaru sha bakwai ba, sanye cikin red habaya mai adon stone hannun riga da tsakiyar riga, ta yi rollin din kanta da dankwalin rigarta, doguwa ce fara sol dan tana mugun kamannin da mahaifiyarta Hajiya Basma. Nan da nan ta karya murya cikin cool voice dinta ta ce, " Daddy ni fa yau so nake naje bikin kawata kuma kudin da ka ba ni, naira million biyar satin da ya wuce sun kare, pls ka karamun biyar din dan zanyi bajinta a wajen taron". Ta karshe zancen cikin shagwaba. Alhaji fuskarsa ɗauke da Annuri ya ce, " Haba daughter in kina son kudi, kawai ki ce na tura miki, kin ga Zahra'u tana Dubai tana karatu, zanso kema kije. . . . . . ". sauran kalamansa makalewa su kayi sakamakon ganin, Yasmin cikin shigar makaranta ta fito daga sashinsu, sanye cikin tsohuwar uniforme mai kalan bleu da fari da jakarta da ta rungume, kafarta sanye take da da safa cikin takalmin makaranta mai igiya, Yarinya ce me kimanin shekaru 16 aduniya farace sol zubin larabawa, duk da dushewan fata da ta yi hakan be hana nunawa ita din fara ce sosai ba. Ɗauke ganinsa a kanta ya yi yana kallon yanda Meenat ke binta da kallon mamakin ganinta, shi kuwa kauda kansa ya yi ya fara ƙoƙarin shigewa daya daga cikin jerun motocinsa, da mamakinsa sai gani ya yi Yasmin ta bi kusa dashi har sun kalli juna ta ɗauke idanu bata gaishe shi, bakaramin shock ya shiga ba duk da ya san duk tsawon shekaru ko baze amsa ba zata gaishe shi, cikin hanzari ya kara kai dubansa akanta, hango ta ya yi cike da girmamawa take gaishe da Tanimu me Gadi. Meenat da ke kallonsa tabe baki ta yi cikin siririyar muryanta ta ce, Daddy pls ina jiran kudin, ka tabbatar ka tura su kafun kafita ". ta kai karshen zancen tare da barinsa ta yi cikin gida cikin hanzarinta domin kaiwa mominta labari da dumi duminsa, shi kuwa sai da ya share minti biyar ya tunanin sabon halin Yasmin, barin tunanin ya yi tare da yin transfert din kudin a account din Meenat. Ahanzarce ya tada motarsa. Tanimu mai Gadi cikin hanzarinsa ya bude masa gate, Alhaji na ƙoƙarin fita daga Gidan ya fara jero masa gaisuwa har kasa, amsa masa ya yi yana mai ƙoƙarin danna hancin motar wajen Gidan, yana fita da hancin motarsa daga gidan ya hango Yasmin bakin titi alamun napep take nema, tsaida tukin motarsa ya yi yana kallon yanda take daga hannu wajen tsayar da mashin, tana yi tana kallon agogon hannunta da dukan alamun hankalinta a tashe yake ganin za ta yi latti, wata bakar mota ta faka gabanta kallon daya ta yi wa motar ta fara yunkurin barin wajen, wanda ke cikin motar kyakkyawan matashi ne ajin farko, kallon daya zaka masa kasan dan hutune, domin agogon da ke hannunsa na diamon ne, kara binta da motar ya yi yana mai fadin " Baiwar Allah dan, dan Allah bari na sauke ki makaranta da dukan alamu kin rasa abun hawa ". Ya kai karshen zancen yana mai ƙoƙarin bude murfin motarsa, ita kuwa kin tanka masa tayi, tare da samun mashin a daidai lokacin, ba ta jira sunyi ciniki ba ta fada masa makarantarsu, hawa mashin din ta yi inda suka bar wajen, shi kuwa matashin murmushi ya yi jin sunan makarantar da zataje, daga haka yaja motarsa ya yi gaba.

 Alhaji Isah Sharifai shi ma tada motarsa ya yi tare da fara bin sahun Yasmin, har ta iso makarantarsu, tana ƙoƙarin shiga ya yi daidai da isowarsa makaranta, kallon skul din yake da kyau ganin ansa Raudat school nan dai ya shiga bin dalibai masu shige da fice a makarantar. Wani dalibi ya gani, samun kansa ya yi da tsayar dashi ta hanyar kira, tambaya ya fara masa domin son sanin ajin da Yasmin Isah Sharifai take Cikin zazzare idanu dalibin ya ce, " Tabb wai Yasmin Sharifai, ai yanzu ta ce adaina kiranta da Isah sharifai ".

Zazzare idanu Alhaji ya yi bakinsa na rawa ya ce, "

Wani suna take son a dinga kiranta da shi? ". Ya jefo masa tambaya.

" Yasmin Umar, shi ne sunan da tace mu ringa kiranta da shi kuma mu kanmu ban da malaman mu, har mun fara manta asalin Isah Sharifai din ". Ya kai karshen zancen yana mai bin hanya domin yin uzurinsa. Shi kuwa Alhaji Isah kamar an datsa shi a wajen ya dade yana juya kalaman yaron, cikin rashin kuzari ya tada motarsa tare da barin wurin.

Meenat tana isa sashinsu labari taba hajiya Basma a kan Yasmin ta fito farfajiyar Gidan bayan ta san suna nan ita da Daddy. Hajiya Basma cikin tsoron kada shirinta ya lalace ta ce " Meenat kyaleta dan uwarta zata gane shayi ruwa ne sai nayi sanadin da za su bar gidan nan daga ita har shegun ya'yanta, da kuma Mariya da ke zaune a gidan mu, dan kawai ta haife shi sai ta tare mana a Gida ta ci zamaninta, ta zo kuma tace zataci da surukai haba wannan zancen karya ne wallahi ". Tana kai karshen zancen ta fara ƙoƙarin lalubo wayarta, dayan hannunta na kan Diyar Asma'u da ke kwance saman cinyarta yar kimanin shekaru goma a duniya. Waya take yi da kawarta, nan da ta shiga bata labarin abin da ke faruwa, daga cen bangaren sosai ta nuna jijjiga da batun nata inda har ta nuna mata ya kamata, a yi sabon shirin domin gudun bacin rana.

 Duk hirar da suke Meenat da Asma'u sai murmushi suke, cikin yaukin murya Asma'u ke fadin " ni wlh na tsani ganin su Yasmin cikin Gidan ubanmu, Daddy yace ba ya'yanshi ba ne to a kan me za su zauna mana Gida". ta kai karshen zancen tana kara matsewa jikin Mamarta. Hajiya Basma murmushi da ita kaɗai ta baiwa kanta sani take yi.

 ABUJA CITY

Bayan kwana uku

 Safiyar Litinin da misalin karfe goma

Ridwan yan jaridu makil a kofar Gidansa, yana daga cikin dakinsa sai tashin hayaniyarsu yake ji, duk da asaman bene yake, ahankali ya fara yunkurin sauka daga kan lallausan gadon barcinsa, idanunsa ba su gama wartsakewa, sanye yake cikin tsadaddan kayan barcinsa mai kalan ruwan toka, ahankali ya kai dubansa a kan agogon da ke makale a bangon dakinsa inda yaga karfe goma da kwata, jin tashin hayaniyar na karuwa ya sa shi tattaro kuzarinsa tare da yin wajen window din dakinsa. Lallausan hannunsa ya sa domin janye window glass din Dakinsa, tare da zura kansa domin ganin me ke faruwa, cikin zallan mamaki da rudewar tunani yaga. . . . . . . . . . . . . . . . .

Makauniyar Shari'a taku ce

Comment and sharhi pls

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 

NA

IKILIMA ADAM

 (kyauta daga Allah)

Littafin nan, na kuɗi ne da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Dari biyar kacal

3115484026 Ikilima Adam firts bank

Tura shaidar biya a kan wannan lambar (09069080725) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.

Siyen Nagari mai da kuɗi Gida

Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma. 📚📚

SHAFI NA GOMA

 Yana kara kusanto inda take, tsoro da tashin hankali suka kara tafasar da zuciyarta, damshin hawayen da ke faranti a idanunta, dashi take kallonsa, murya a raunace ta ce, " dan Allah kar ka cutar dani, ban da kowa sai Allah sai Papyna". Ta karashe zancen cikin sheshekar kuka da jan majina. Kallon ta yake kallon tausayi wanda ze iya fadin a kundin Rayuwarsa, tun barinsa Gida be ga abunda ya bashi tausayi kamar ita ba, yasha kashe rai, ya caka wuka a cikin mutum, ya yi garkuwa da mutane, kuma ya yi informa na yan bindiga duka babu inda baya taka rawar gani, sai kukan Amatullah ne ze karya masa zuciya. Kafe ta da idanu ya yi yana kallon yanda take matse jikinta, cikinsanyi murya ya ce " gayamin sunanki? Papyn dinki ya tafi yabarki na har abada a kan idanuna ya hau mota a tasha kuma na ganshi ya ganni da bakinsa ya ce min, in mai da ki kar kashin ikona dan haka ki share hawayen ki, zan zame miki gata kuma zan kula da lamuranki in sha Allah ". ya karashe zancen yana mai kallon yanda ta zazzare idanu jin wai Papy ya bar garin.

Amatullah sabon babin tashin hankaline ya bayyana karara tattare da ita, kuzarinta natsuwarta walwalanta duk sun tafi lokaci daya, maganganun Papy take tariya, hakan ya sa ta saki kuka mai sauti, tare da rusa uban kuka mai gunji tana fadin " ya Allah !! Ya Allah !! ya Allah !!. "

 Karfin Iko ganin kamar kukan ba bari zatayi ba sai ta gaji dan kanta hakan ya sa murya a khausashe ya ce " tashi muje ko kuma in ɗauke ki da kaina, zabi ya rage naki ". Ya yi magana iyakar gaskiyar sa, yana mai kallon yanda ta fita hayyacinta lokaci daya.

 Sosai da tasha jinin jikinta tana mai dago kai tana kallonsa da jajayen idanunta, so take ta yi magana ta kasa, ganin yanda ya haɗa rai yana mai tsurawa kyakkyawar fuskarta idanu babu kiftawar idanu.

 

 Gani ya yi kamar bata da niyar motsawa hakan ya sa shi janyota da hannayensa tare da janta tana kuka yana janta, tana ihu mai kururuwa sai fadi take " Jama'a ku taimaka min ze saceni ". disashewar muryanta ya sa ba'a jinta, har bakin titi suka isa daidai bakar mota kirar Mercedes-Benz, kafin ya karasa tuni aka bude masa murfin motar baya, turata ya yi cikin zafin nama, kana ya sa hannayensa ya rufe gam, ta dayan bangaren ya shiga ya zauna yana mai kallonta tana kuka mai cin rai ta saka kanta a tsakiyar kafafunta, numfashi ya fesar kana ya kalli keyar drever tare da bashi izinin tafiya.

 Babu bata lokaci me zaman drever ya ja motar yana tuki yana kallon Amatullah ta gilashin motar yanda ta cika su da sheshekar kuka, na kusa dashi ya kalla ya tabe baki, shi ma na kusa dashin girgiza kai yake yana jinjina al'amarin. Karfin Iko ransa ya dan soma baci a kan yanda take ta kuka babu sassauci ganin kamar hakan ze sanya sa damuwa ita kuwa ze sanya mata ciwo yasa, cikin kakkausar murya ya ce " wallahi ki min shiru ko na sa bindiga na harbe kanki kowa ma ya huta hatta Papy naki baze kara sanyaki a idanu ba ". Ya karshe zancen cikin dan bacin rai.

 Nan da nan tasha jinin jikinta tare da hadiye ragowar kukanta, soma goge hawayenta ta yi tana mai matse bakinta dan sosai ta tsorata dajin in ya harbeta bazata kara ganin Papy ba, bayan tun tasowarta Papy ya nuna mata illah harbi da wuka duk wanda aka cakawa mutum mutuwa zeyi. Bakin ta na rawa ta dago kanta daga durkushen cikin rawar murya da ban hakuri ta ce " kayi hakuri bazan sake ba dan Allah kar ka ce zaka harbeni ina son ganin Papyna ". Ta karshe zancen cikin tsananin tsoron sa da ya shige ta lokaci daya, dama cen tana tsoron sa be kai na yau ba ne. Drever dana kusa dashi dariya su kayi dukansu jin yanda take magana cikin rawar murya.

 Karfin Iko be bata amsa ba saidai cigaba da bin ta da kallo yake yana fadi a kasar zuciyarsa Amatullah ke tawa ce har abada baki da miji kamar ni baki da mafi cancanta sai ni, zan zama mijin ki uban ya'yanki ". Ya karshe zancen zucin yana mai kar kata idanunsa a kan titi, kallon tituna yake amma sam hankalinsa amma ta gefen idanu yake kallon ta.

 

 Unguwar gwarinfa na cikin Abuja kai tsaye suka nufa, inda suka karya kwana izuwa layin Gidan nasa, babban Gida na Alfarma wanda ya cika da kayan Alatu da kayan more rayuwa, tun daga babban get din kake hango manya bishiyoyin furanni da aka shuka, haka ma wajen gidan kananan furanni ne zagaye da wajen gwanin burgewa da ban sha'awa. Horn ya shiga yi, babu bata lokaci mai gadi ya wangale musu babban gate din gidan, Amatullah wawware idanunta take ganin sabon gida ginin zamani wanda komai na more rayuwa yana ciki, parking space drever ya paka motar, kana cikinsauri sauri aka budewa karfin Iko murfin mota ya fito, yana fita da kan shi ya zagaye domin budewa Amatullah kan ya karasa ahanzarce yaran nasa ya sa hannu ze bude, hannu ya daga masa alamun wannan aikinsa ne, cikin hanzarinsa ya sa murdaddun hannayensa ya bude murfin motar, tare da bin ta da kallo na tsanake, ita kuwa ban da innalilahi wa inna ilairajun da Papy ya koyar da ita in har tana cikin tashin hankali babu abunda take maimaitawa a kasan zuciyarta, kana bakinta na dan motsawa kadan kadan kamar me shirin yin magana, lura da kallon da yake bin ta mai nuna alamun ya gaji da jira ya sa ta sauke fararen kafafunta a kasa, zararan idanunta take bin farfajiyar gidan da kallo ganin ma'aikata masu kai kawo da manya manyan samudawa da ke safa da marwa acikin Gidan, kasa cire idanunta akansu tayi, batare da ta ankare ba taji hannunta cikin nashi yana janta izuwa hanyar da ze sadashi da babban falon Gidan. Kallon bayansa take yana gaba tana binsa, har suka iso gaban haddiyar kofa mai kamar lu'u lu'u ya ci ado kamar na zinare, sakin hannunta ya yi ya danna wasu numbobi da duk alamu code din kofar ne, tana ganin ya shiga ta bi bayansa ga mamakinta sai ganin wani kofar glass ta yi again, shi kam kofar da kansa ya bude kansa, wanda hakan ya sa ta so callara ihu dan tsoro, duk a zatonta ko tsafi ne, gaba da ya yi ne ya sa besan halin da take ciki ba, ganin kamar kofar ze rufe bata iso ba ne ya sa shi ɗan juyowa fuskarsa ba yabo ba fallasa, da mamaki yaga ta rintse idanunta, siririn tsaki yaja kana ya fisgota tare da jan ta zuwa kayataccen falon da aka narka dukiya, naira ta yi kuka a wannan tsararren falon, gabakiya falon kalan hash color ne hatta carpet din falon, sanyi Ac da ke kadawa ya sa ta fara mammatse jikinta tana bin sa har ya zaunar da ita kan kujerar falo mai taushi da dadin zama, ya salam ta furta ya yin da ta ji mazaunanta sun sha taushi mai sa nutsuwa da gangar jiki, wawware idanunta take tana mai kai dubanta a kan television da ke ajiye kan kyakkyawar mazauninsa, sassanyan ajiyar zuciya ta sauke tana kallonsa yana ƙoƙarin barin falon, tare da hawa kan matakalan step da idanu ta rakashi cikin dan tsoro tsoro, papper da ke hannunta ta hanzarta ɗaukewa ganin ya fadi kasa, maganar zuci take dan yau shi ne karo na farko da taga bene kan idanunta duk da papy yasha zana mata a takarda, mai da hankalinta ta yi gun kalle kalle ta har idanunta suka kai kan hadadden fankar da ke kadawa a sama, kana ta kai dubanta a kan kwayayan kwan fitilu masu launin furanni, tana sauke idanunta ta mai da kallonta gun diner table wanda yasha jeren kwanukan abinci da babban wamers da cokula, jok din ba karamin burgeta ya yi ba ganin yanda yake kamar buta, dan tsaruwa da kyau ƙoƙarin tashi take domin tabawa taji takun tafiya hakan ya sa ta kara rike takarda hannunta da karfi, sunkuyar da kanta kasa ta yi tana mai jin buguwar zuciyarta yana tsananta. Jin an karaso kusa da ita ne ya sa ta dago kai sama, cikin kidima take kallon katuwar mata me kiba sosai, da murmushi matar take kallonta kana tana kallon Karfin Iko dashi din ma Amatullah yake kallo, fesar da numfashi ya yi tare da saka duka hannayensa cikin aljihun wandonsa, cikin muryansa ta dabi'a ya ce" yan mata nan za ki zauna tare da kulawar Anty Hasina dan haka, ki saki jikinki da ita agidan nan kaf bakida kamarta bayan ni, sannan duk abin da kike so ki sanar mata in sha Allah za'a miki. " Yakarashe zancen yana mai kallon Hasina da idanu, ita ma kallonsa take tana murmushi kana tana kallon Amatullah da tattare wuri daya.

" Yan mata ya sunanki kuma shekarunki nawa, wace makaranta kike, meye level dinki a karatun boko da islamiyya". Cewar Hasina Ta jero mata tambayoyi ba kakkautawa kamar jiran wannan ranar take.

Amatullah dago idanunta sama ta yi tana kallon Matar daga sama har kasa kana cikin rawar murya ta ce " Sunana Faridat, amma papy yana kirana da Amatullah ko My Friday, kuma mutan kauye suna kirana da Yar wahala, shekaruna goma da biyar ". Ta karashe zancen cikin gaskiyarta da tsantsar kuruciya.

Daga Karfin Iko har Hasina sai da suka dara kusan tare, da murmushi kwance samar fuskarsu, Karfin Iko kallon Amatullah yake kamar ba ita ta yi magana yanzu ba.

 " Waou Nice name, zan de kiraki da Amatullah suna yamin dadi, goma da biyar  ba suke nan shekarun ki goma sha biyar?". Ahanzarce Amatullah ta gyada mata kai kamar kadangaruwa.

Cigaba da magana ta yi fuska a sake ta ce " Ma sha Allah saidai baki gayamin level dinki a. . . . . ".

 Saurin katse ta Karfin Iko ya yi ta hanyar daga mata hannu, tare da zama kan kujera da ke kusa da Amatullah. Jikake tsitt a falon ban da bugawan zuciyoyinsu. Mama Hasina gefe daya ta samu ta dan raba a kan lafiayyan Carpet din tsakiyar falon.

" Amatullah wannan da kike gani yar uwata ce, kamar yanda na dauko ki haka itama na dauko ta daga gidanmu har muka saba nida ita, dan haka ki saka ranki a inuwa kema za ki saba kamar ita kuma za ki ji dadin rayuwa, ki manta komi na baya ki fuskanci Alkibla, sannan ina da dokoki na Gidan nan, ba'a fita daga gidan nan, ko me mutum yake so ya yi magana da zaran kin dan kara wayau zansa a daura mana Aure ni da ke dan kin min ba karya ". Ya karashe zancen yana mai kar kata bakinsa, duk da maganganun da yake idanunsa na kan Television da ke kashe.

 Anty Hasina da Amatullah kusan atare suka kalli junansu, murmushi Hasina ta sakarwa Amatullah, hakan ya sa Amatullah dukar da kanta tana juya kalaman wai Karfin Iko ne yake fadin ze Aure to ta ya ya, lissafi ne ne ya darzan mata a zuciya lokaci daya, kallon Hasina take da idanu ganin ta tafi wajen Karfin iko ta zauna har tana ƙoƙarin rage masa kayan jikinsa, kauda kanta gefe ta yi tunani fal aranta Papy ya tafi yabarta sabon babin kuka ne yake son fara zuwa mata, kukan da take shirin ne ta katse ganin anty Hasina ta kama hannunta tare da mikar da ita, idanunta da suka kawo ruwa take kallon Hasina da shi domin so take ta ji ina zata kaita, tana mai kallon yanda Hasina ke sakar mata murmushi.

" Haruna yace aka kai ki masaukin ki, cen zan kai ki dan haka muje, ki saki ranki nan gidan akwai ma'aikata maza da mata akwai malamai masu koyar da yara, sannan akwai sashin marayu duk wanda kike son hira dashi acikin su kofa abude take ". Ta kai karshen zancen ne tana jan hannun Amatullah izuwa masaukinta.

Amatullah sosai take juya kalaman wai sashin marayu in har bata manta ba Papy yace mata wanda beda Uwa da Uba ko kuma ya rasa daya daga cikinsu shi ne maraya. Nan da nan jikinta ya yi mugun kankara, barin wani tunanin ta yi ta fara sheshekar kukan rashin Papy,  ba suke nan yana nufin ya tafi ya barta  ba suke nan har abada, tunani take me ya sa Papy ya dauki danyen aiki akanta, wata zuciyar ta ce " yo ai saboda Karfin Iko ya san inda kuke ne ya sa ya gudu, nan da nan taji babu abin da take ji da haushi sama da karfin Ikon. Ajiye tunaninta gefe ta yi sakamakon jin karar bude kofar da Hasina tayi, hakan ya sa tabi sahunta gun shiga babban daki me fadi, gado ne aciki sai wadrobe, babu wasu takarce adakin, da idanu take bin dakin da kallo, ganin yanda iskan fanka ke tashi ba sauki daga sama, fankan take bi da kallo hade da dan lumshe zararan eyelashe din idanunta. Ita dai kallon Hasina take ta nuna mata tsarin dakin har toilet da ban daki duk ta kaita, fuskarta ɗauke da murmushin rahma.

 

Wasa farin girki

Umar Faruk satinsa daya acikin Abuja, ya rasa inda ze sanya kansa domin tun acikin mota aka sace wayarsa da kayansa, bashi da komi daga shi sai suturar jikinsa, kuka yake zaune a bakin masalanci tashar daya sauka, ya fara tuno da kalaman Kanwarsa abun soyuwarsa Yasmin a kan bata son yaje Abujan, tuno da halin da Mamy zata shiga ya sa hankalinsa kara tashi. Kuka yake rerawa tsakaninsa da Allah domin wanda ya zo domin shi babu yanda zeyi ya same sa, kuma ya san shi ma mutumin zeyita nemansa, ganin babu mafita ne ya sa shi tashi tare da zuwa wajen drebobi masu lodin fasinja Cotonou, Muryansa na rawa ya ce " Drever dan Allah wani bezo cigiya a wannan tashar ba? ". Ya idasa zancen murya na rawa.

Drever da idanu yake kare masa kallon tsafta kana a hanzarce yace wlh kuwa yau kwana biyu  ba suke nan wani yana zuwa cigiya kuma da dukan alamu ya gaji da kai kawo da yake. Wata irin mummunar faduwar gaba ne ya ziyarci zuciyar Umar, cikin rawar murya da tashin hankali ya ce. . . . . . . .

Makauniyar Shari'a taku ce.

Comments and share pls

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 

NA

IKILIMA ADAM

 (kyauta daga Allah)

Littafin nan, na kuɗi ne da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Dari biyar kacal

3115484026 Ikilima Adam firts bank

Tura shaidar biya a kan wannan lambar (09069080725) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.

Siyen Nagari mai da kuɗi Gida

Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma. 📚📚

SHAFI NA SHA DAYA

Cikin rawar murya da tashin hankalin da ya bayyana karara afuskarsa ya ce " dan girman Allah be bar muku number wayarsa ba? ". Ya karashe zancen murya a raunace, sabon babin tashin hankali ne ya bayyana karara a fuskarsa, yanzu  ba suke nan inhar be kara waiwayo tashar ba shike nan wahala ta same shi, ji yake kamar ya kurma ihu dan tsantsar bacin ciki, tunaninsa katsewa ya yi jin Drever na fadin.

" Gaskiya ba mu amshi lambarsa ba amma shi kam ya amshi namu, yace zeyi ta tuntuɓar mu ko za'a dace ". Drever na kai karshen zancen ya barsa agurin tare da shiga motarsa domin zuwa shan mai.

Faruk ya danji sanyi aransa domin hakan ya tabbatar masa ze iya kira a kowani lokaci, tashin hankalinsa befi tunanin abin da ze ringa ci kafin yaga Megidansa ba, yana hangar me shayi a ketaran titi dabara ta fado masa a kan ya sa ya yanke shawarar yaje ko Allah zesa adace ya ɗauke sa aiki koda aikatau ne.

 

Sun sha tafiya mai dan nisa a headquarters na yan Sanda kafin suka samu zama kan kujeru na afarman saukan baki, Commissioner da ke zaune a kujerar da ke kallon nasu, fuskarsa babu yabo ba fallasa yake kallon kowannensu musamman Ridwan da ya dukar da kai tun shigowarsa dakin, sosai yake ji tsananin tashin hankali wacce ba'a sanya mata rana, sanye yake cikin farar shadda wacce yasha aiki farin zare gun kwararan tela, farar hularsa nake bi da kallo yanda ya zauna masa daram akansa ba karamin kyau gilashin da ke sanya a idanunsa suka kara masa ba. Dakin zagaye suke da ma'aikatan yan sanda kowannensu goye da hannayensa ta gaba. Commissioner Bashir Muhammad ne ya yi gyaran murya hakan ya sa kowa dago kai suna fuskantarsa, fesar da numfashi ya yi idanunsa na kan Ridwan da shidin ma shi yake kallo.

" Haba Ridwan Mai Nasara taya zaka ajiye aiki yau kusan shekara daya  ba suke nan, anyi anyi dakai kaki komawa a kan aikinka, ai zamanka amatsayin shugaban KEDCO na Nigeria ba shi ne yake nunan cewar bazaka iya hada ayyukanka ba, tun da ka tafi ba'a samu mai ƙoƙarin ka ba har ila yau, Ridwan ka tuna fa abaya ba ka dau aiki dan ka ajiye ba ina da yakinin ba tsoro ne ya sa ka ajiye aiki ba, akwai kwakwaran dalilai, haba Ridwan talakawa suna bukatarka wa'yanda aka tauye musu hakkinsu suna bukatarka, Ridwan naso ace kaine a kan kujerata, amma kuma zamanka a wannan kujerar baze baka damar yin aikin da ka saba ba, haba !! haba !! haba !! kayi tunani mana, dan zatin Ubangiji ka dawo aikinka ya Ridwan ya karashe zancen murya kasa kasa alamun takaici.

 Ridwan jikinsa har tsuma yake kamar mazari, kasa jure zaman da yake ciki a kan kujerar ne ya sa ya mike ahanzarce tare da bin gefe sauran jama'a ze raba su ya fice cikin hanzarinsa, har ya kai hannunsa kan handle din kofar ze bude yaji kakkausar muryan Commissioner Bashir yana fadin " Ridwan yanzu kana nufin ban isa dakai ba?". Ya karshe zancen yana kallon keyarsa cike da takaicin taurin kan nasa.

Cak yatsaya be cire hannunsa a kan handle kofar ba, be waigo ba, ban da tsananin buguwar zuciya ba abin da yake tsananta a tattare dashi, kamar baze waigo ba yanda yake tsaye kikam, Commissioner da sauran ma'aikata da idanu suke kallonsa kowannensu. Ba zato ba tsammani suka ga ya waigo, jajayen idanunsa da suka kada jajir suke bi da kallo, daga inda yake tsayen ya kara gyara tsayuwarsa, cikin rawar murya me nuni da zallan bakin ciki ya ce " Afuwan mai girma Commissioner Bashir, ban bijire ba kuma na yaba da nagartan aikina da kuka yaba, kuma ina mai muku fatan samun wanda yafini ko da a nan kusa nasan za'a samu fiye dani kar ku damu, na ajiye aiki bazan. . . . . ". Sauran kalaman da ke shirin furtawa ne suka samu damar makalewa jin wani dattijon dan Sanda ya rike hannunsa, idanunsa sun kada jajir kamar gauta yana girgiza masa kai alamun kada ya karasa furucinsa ya san in har rantsuwa ta shigo ciki tabbas Ridwan yabar abunnan har abada babu waiwaye.

" Dan Allah Dana kayi hakuri, ko dan tsufana, kar ka cire hannu acikin aikinka, kar ka ce zaka raba hanya damu ya kai yaron kirki ". Ya karshe zancen yana ƙoƙarin durkushewa kasa dan magiya .

Ganin haka ahanzarce Ridwan ya durkushe wajen tarosa hakan ya sa idanunsu tsarkewa cikin na juna shida dattijon, be san sanda ya kaiwa Dattijon wawan runguma ba, domin dattijon yana daga cikin wanda yake jin dadin aiki dashi a headquarters.

" Baba zan dawo aiki nan da wata daya in sha Allah". Ya karashe tare da dagowa dukansu daga durkushen, kallonsa ya mai da a kan hall din yan dakin yanda aka zuba musu idanu ana kallonsu, Commissioner murmushi kwance a kan fuskarsa yake fadin " Alhmdulillah ". A Kasar Zuciyarsa. A fili kuma kasa magana ya yi dan farin ciki.

Ridwan be tsaya jira abin da za su fadi ba ya hanzarta barin office din jiki babu kwari.

Dattijon kuwa dawowa tsakiyar dakin ya yi yana kayataccen murmushi, bakinsa na rawa ya ce " Yallabai in sha Allah tunda Dsp Ridwan Mai nasara ya dawo aikinsa zancen ya kare kawai lokaci za mu jira, ahaka da suka ci gaba da tattauna tsare tsarensu.

Shi kuwa Ridwan a farfajiyar ma'aikatan yana gaisawa da yan sanda da ke kai kawo, murmushi kwance kan fuskarsa yake gaisawa da wani abokin aikinsa da ya zo wajensa suna tattauna yaushe rabo, juyawar da zeyi idanunsa ya sauka a kan yan mata yan tallah masu ɗauke da robobin abinci, irinsu shinkafa da wake da miya da salad, nan da nan ransa ya ɓaci, suna hada idanu da Ridwan nan da nan hantar cikinsu ya kada sunsan ya hanasu kawo tallan abinci da kananun shekarunsu, ƙoƙarin yi musu magana yake yaji muryan Mansur yana fadin " kaga shiga Mota muje zan duba Mama batada lafiya sosai fa ". Ya karashe zancen cikin tsanani damuwa.

Ridwan hankalinsa ya ɗauke a kan yan mata masu tallah, be tsaya bata lokaci ba ya shige motar inda suka ba motar wuta a 360 domin gani suke sam basa sauri ayanda akace Mama tana jin jiki.

Kasar Benin Cotonou

Alhaji Isah Sharifai zaune a farfajiyar Gidansa shi da Hajiya Basma wacce take sanye cikin kananun kaya riga da wando ba karamin kama jikinta ya yi ba, shikuwa daga shi sai gajeren wandonsa da rigar shan iska mara hannu, babyn wasan yara ne a hannunsu yana jefa mata tana mai da mashi, fuskokinsu ɗauke da murmushi mai sautin, cikin shagwaba fuska ta duniyanci ta ce " Alhaji ni de ko sai ka goyani". Yanda ta yi furucin sosai ya basa dariya har kuncinsa ya lotsa.

Cikin yar tsokana yake fadin " kema kin bi wakar nan da ake ya yi ko? ai ba matsala ba ne dan masoyi ya goya abar kaunarsa kuma. . . . . ". Kasa karasa ragowar kalamansa ya yi ganin Yasmin ta fito kamar wata yar mabarata, ahanzarce dan sauri sauri take tafiya, sam bata gane inda take sanya kafafunta, tana karasowa kusan Alhaji da Matarsa, kallo daya ta musu ta ɗauke kanta, ganin su ma ita din suke kallo da mamaki fuskokinsu sannan babu fara'a a fuskokinsu. Da idanu Alhaji ke bin ta da kallo ganin kodaddiyar doguwar rigar da ke jikin ta, kara rufe baki ya yi ganin ta isa gun Baba Mai Gadi, muryanta na rawa ta ce " Baba Dan zatin Ubangiji ka taimaka ka ba mu aron dubu daya, wallahi yau kwana hudu ba mu samu labarin yaya Umar ba, kuma Wallahi Mamy olsa dinta ya tashi kwana biyu ba mu ci ba, dan zatin Ubangiji kamar yanda Allah ya taimakeka ka taimaka mana wlh inna samu zan mai da maka kudin ka, ko kuma in antina ta zo za'a baka, wlh kakata ma yanzu haka tana cen kwance, kar ka ce min babu komi a hannunka dan Allah !! ". ta karshen zancen cikin kuka mai gunji.

Bala mai Gadi cikin rudewa ya ce " Subuhannallah muje daga ciki ina da dubu biyar zan baku har sai kun samu ". Ya kai karshen zancen yana mai shiga dakinsa domin dauko kudin, da kuma robar faro faron kununsa a hannunsa.

Yana fitowa mika mata kudin ya yi kana ta yi gaba cikin hanzarinta shima ya take mata baya.

 

 Duk abin da ke faruwa a kan idanun Alhaji Isah shida Basma, siririn tsaki yaja, tare da kai dubansa a kan Basma cikin nuna kulawa ya ce " daman dan A'isha baya garin nan?". Ya yi mata tambaya cikin rawar murya.

 Basma na dan nan ta bata fuska kamar wacce akayi wa albishir da ranar mutuwarta cikin jin haushinsa ta ce " wai kai Alhaji kai har yanzu baka san sharrin Yasmin ba, duk pretendin take, domin a tausaya mata take kuma wallahi karya take, ni dazun ma na ga Umar din, amma kaji yar rainon matsiyaciyata tana fadin baya garin, wai kai Alhaji ina ruwanka da lamarinsu ne, kasan dai yaranta ne ka daina sanya mata idanu da yayanta, ban da abunka ma, kabarsu acikin Gidan ka kar yau mutuwa ta riskeka suce suna da Gadon ka, gaskiya ka dau mataki ". Ta idasa zancen cikin ruwan bala'i. Alhaji sosai maganganunta sukayi tasiri a ilahirin jikinsa, kamar ankada shi da ganga zumbur ya mike, ya kama hanyar da ze sadashi da sashinsu Yasmin cikin zafin nama, ita kuwa Basma ganin ya fice sai da ta ranka guda kana tabi sahunsa tana tafiya tana karairaya har ta iso inda yake. Bankada kofar da karfi ya yi ya shigo dakin.

A kidime Yasmin da Baba mai Gadi suke kallon yanda yake huci kamar zakanya.

 Mamy da ke shan faroron kunun da me Gadi ya kawo mata da shanyayyun idanunta take kallonsa dan zata iya rantsewa rabonta data sanya shi a idanunta anfi shekaru uku.

Shi kuwa kallon su yake yana hura hanci kana ya kalli gefensa ganin Basma tana kusa dashi, ita ma kallon banza take binsu dashi tana kwabe baki .

 Cikin zazzafan kalamai ya ce " Aishatu na baki daga nan zuwa gobe ku tattara ina ku, ku bar min gidana, sannan ina fatan in zaku tafi ku hada da Mamata ku tafi da ita dan kun shayar da ita guban halinku, wanda ni Isah bazan iya zama da ita ba, sannan. . . ". Ba tare da ya karasa ba, Yasmin ta dakatar dashi ta hanyar fadin .

" wallahi tallahi, na rantsewa wanda numfashina yake hannunsa idan. . . . . . . . .

Makauniyar Shari'a taku ce

Comment and sharhi pls

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 

NA

IKILIMA ADAM

 (kyauta daga Allah)

Littafin nan, na kuɗi ne da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Dari biyar kacal

3115484026 Ikilima Adam firts bank

Tura shaidar biya a kan wannan lambar (09069080725) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.

Siyen Nagari mai da kuɗi Gida

Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma. 📚📚

SHAFI NA SHA BIYU

Wallahi tallahi, na rantsewa wanda numfashina ke hannunsa idan kaga mun fita sai da kwakwaran hujja da ze tabbatar mana mu shegu ne kamar yanda kake ambata ko wani time ". Cewar Yasmin cikin tsananin bacin rai, dan hankalinta ya gushe bare har ta gane girman wanda ke gabanta.

Mamy kuwa rintse idanunta ta yi domin taji takaicin tanka masa da Yasmin tayi, cikin raunin murya me nuna da sam babu kuzari tattare da ita, tace " Haba Yasmin Mahaifinki kike jifa da wannan munanan kalaman ". Ta idasa zancen tana kallon Baba Mai Gadi da ke ƙoƙarin fita daga Dakin yana yaba ƙoƙarin Yasmin acikin ransa dan ta burgesa.

 " Ahirr dinki ko da wasa kada ki kuskura ki kara alakantani da ya'yanki nace ya'yan nan ba nawa ba ne kinki ki gane, tsinannun yayanki za ki ringa dangantani dasu dayan tunda ya san ni ba mahaifinsa ba ne ya gudu yabar Gida, shi kuma la'anannen danki Umar tsabar ana son in mutu aci dukiyata shiyasa yaki barmin gidana, ta Allah ba taku ba". Cewar Alhaji Isah cikin kakkausar murya.

 

 Mamy idanunta cike da hawaye tana kallon yanda Basma ta daura hannunta daya a kan kafadarsa tana taunan Cingam ji kake karar karas. Bata ankare ba hawaye Masu zafi suka fara bin kuncinta.

Ahanzarce ta shanye kukanta jin ya cigaba da fadin" tunda ba zaku barmin gidana ba ku saurari sammaci daga kotu nasan a nan ne za'a mun iya daku, sannan ke Yasmin har kinada bakin da za ki dubi tsabar idanuna kice bazaku fita ba, to wallahi kotu ce zata rabamu nida ku, dan asirinku be kamani ba wallahi kamar yanda kuka shanye Mamata haka kuka shanye me Gadi, shi ma hada shi zanyi da ku yabi ku dan babu amfanin zama da wanda ya rabe ku ". Ya kai karshen zancen yana mai jifar Yasmin da Mamy mugun kallo kamar yaga kashi. Ita kuwa Basma sosai taji dadi hakan ya sa ta kara cakumosa tana ƙoƙarin rungume shi ta baya, shi kuwa kaucewa yake ba tare da ya kara bin ta kansu ba ya fice daga sashin nasu a zafafe shida Basma.

 Yana fita suka fashe da marayan kuka dukansu, cikin rawar murya da tsananin tsoro Yasmin ke kallon Mamy da jikakkun idanunta, murya na rawa ta ce " me Alhaji Isah yake nufi yana nufin mu ba ya'yan sunnah ba ne, in har hakane waye Uban namu? Mamy kalmar nan yafi kona min rai in muna da wani uban ki nuna mana, ya fi mu zauna gidan uban w. . . . . . . ". Ragowar kalamanta makalewa su kayi sakamakon jin wawan mari à kuncinta.

Arazane take kallon Mamy hannunta rike da kuncinta, domin ba karamin radadi ke shigarta ba, hawaye kamar saukan ruwa haka ta yi ta silalo su.

" Yasmin wai har ki dubi tsabar idanuna ki ce in nemo muku Mahaifin ku me kuke tunani, wallahi bakuda Mahaifi sama da Isah, kawai cin fuska da rashin tsoron Allah ke damunsa, tunda yace ze kaimu kara kotu, Yasmin ban da mafita illah kawai aje kotun, Yasmin ban da Iyaye ni Marainiya ce, na taso hannun Matar babana bansan kowa ba, ita kanta ta rasu yanzu, damar gidan haya muke zaune, Yasmin bawai dadi ne ko haduwar gidan nan ya sa muke zaune cikinsa ba, muna zaune ne dan bamuda yanda za muyi kuma bamuda kudin kama hayah, Yasmin kinsan Uwa be cancanci tana zubar da hawaye gaban yarta ba, amma yau Yasmin dole ce ta sa nayi, babban tashin hankalina Babu labarin Umar nasan duk inda yaji wannan labarin wlh ze wanko kafa ya dawo Gida, ina rokon Allah a duk inda yake Allah ka kare min shi ya sa lafiya lau yake, radadin yamin yawa Yasmin, rana zafi inuwa kuna ". Ta karashe zancen tare da kaiwa Yasmin wawan runguma, kuka suke dukansu babu mai rarrashin wani.

Kaicona

Alhaji Isah yana zuwa bangarensa, zaro babban wayarsa kiran iPhone 15 prox max, keybor din wayar ya shiga tare da dannawa dan sanda waya, ganin ba'a daga ba ya fara safa da marwa cikin zafin rai da takaicin kalaman Yasmin da ke yawo saman kwakwalwar kansa. Jin an daga wayar ne ya sa shi zama kan hannun kujerar mai zaman mutum daya, fesar da zazzafan numfashi ya yi yana mai magana cikin kakkausar murya tare da fadin " Dsp Faisal Haruna dan Allah ka zo gidana akwai case din da nakeson atura kotu ". Ya kai karshen zancen yana mai kasa falalan kunnuwansa gun sauraren amsa daga cen bangaren.

Dsp Faisal cikin girmamawa ya ce " Alhaji angama, ka kira lauyarka mu hadu dashi a gidan tare". Daga haka sukayi gaba da waya inda sukayi sallama. .

 

 Gefensa ya kalla ya hango Basma tana masa kyakkyawan murmushi mai nuni da tsantsar farin ciki, shi ma murmushin ya mai da mata, cikin muryansa mai nuni da takaici ya ce " Basma badan ke ba da wallahi kullum sai inyi ta kallo yaran nan amatsayin nawa bayan shegu ne, kai wallahi A'isha ta cuce ni tsakanina da ita sai kotu". Ya kai karshen zancen murya kasa kasa.

 Murmushi take sauke masa tsabar farin cikin, cikin azzama ta karasa gabansa tare da jero masa kiss a goshin sa, cike da jin dadi ta nuna godiya a garesa a kan yanda ze cire guba a cikin gidansa.

Abuja Gwarinfa

Hasina zaune a tsakiyar dakin Amatullah, cikin idanu take kallon yanda take kuka ba kakkautawa ganin kukan zeyi yawa tunda aka kawota shi ne abin da ta sanya agaba da anbata abinci saidai tasa kuka tana kiran Papy.

 Hasina zama bakin gadon ta yi tana kallonta cikin idanu, kana cikinsanyin murya ta ce, Haba Amatullah so kike ki kashe kanki, kinsan dai Papy baze so ya ganki cikin Matsala ba bare har yaji bkayason cin abinci, ki taimaka kici koda kadan ne. " ta kai karshen zancen tana jinjina lamarin yarinyar.

Amatullah kamar bata jin ta haka ta yi banza da ita. Cikin zuciyar da bata san tana dashi ba sai yau, cikin da fadafada ta ce" ni kawai a mai dani inda aka daukoni inje inga Papyn kuma wallahi baku kaini ba saina jaza muku bala'i. Ta karashe zancen cikin tsiwa.

 Hasina da murmushi kwance a fuskarta take kallonta yanda Amatullah ke juya karamin bakinta, hakan ba karamin burgeta ya yi ba, numfashi ta fesar fuskarta ba yabo ba fallasa cikin tsare gida ta ce " Amatullah nasan ko ban ban haifeki ba nayi kanwa da ke, ke karamar yarinya ce ina tausaya miki matuka, amma Haruna ba kanwar lasa ba ne duk yanda kike ganinsa ya zarce tunaninki, ki ajiye kuka agefe ki rungumi kaddara, dan ni nan da kike gani a bola aka tsinceni tun ina yar shekara biyu zuwa uku, Maman Haruna Allah yajikanta ita ce ta raineni tare da mahaifinsa, bayan ba ransu shi ne Haruna ya dawo dani kar kashin kulawarsa duk da haka ni Hasina bazan bari ya aure ki ba kamar yanda ya furta, dan babu wacce ya dace ya aura sama dani, wa ze aureni in yaji cewar ni shegiya ce ko kuma akace ban da asali, dole Haruna dai ze aureni domin shi kaɗai ne ya san zafina kuma yake gudun a wulakantani, Amatullah ki godewa Allah, ke har yanzu ne kike kukan Papy, mu da ba mu ga papy da mamy ba me za mu ce?". Ta kai karshen zancen hawaye na bin kuncinta.

 Sosai Amatullah ta gigice ganin yanda Hasina ke kuka ta tabbatar har kasar zuciyarta ne, cikin hanzari ta matso kusa da ita, tana mai share mata kwalla da hannunta, sannan ta ja dogon numfashi, idanunta masu damshi hawaye ne take kallon Hasina dashi, murya a raunace ta ce " Papy na ya gayamin kada in bari babba ya yi kuka akaina ba tare da ya cutar dani ba, dan Allah ki yafe min ". Ta kai karshen zancen tana mai harhada dukan hannayenta wajen rokon afuwa.

 Hasina da murmushi ta warware ma ta hannayen ta tana mai kallon ta cikin idanu.

Amatullah ta ciga da fadin " daga yau in sha Allah na rage damuwar da nasa wa kaina, zan ringa cin abinci, amma bazan taba daina tunanin Papy ba, zanyita addu'a Allah ya nuna min shi ". Ta karashe zancen cikin cool voice dinta.

 Mama Hasina murmushi ta sakar mata tare da kama hannunta ta mikar da ita domin su je ta bata abinci abinci ta ci, domin na dakin har ya yi sanyi. Ba musu ta bi bayanta tana mai rarraba idanu a kan hadadden Gidan da sam bata gajiya da kallo.

Dayan bangaren

Ridwan da Mansur da kanwar Mansur mai suna Mansura sai kai kawo suke bakin dakin da aka rubuta emergency da duk alamun mamar su Mansur tana ciki.

Mansura kallon Ridwan take yanda sukayi cirko cirko gaban kofar shida Mansur ta san jira suke docto ya fito. Kara zubawa Ridwan idanu ta yi ganin yanda suke magana shida amininsa aminci yarda kaunar juna, Amana duk ta hango tattare da abokan juna. Kasan zuciyarta tana tunanin yanda zatayi Ridwan ya fahimci tana sonsa dan ita da gaske wallahi sonsa take, shiyasa take son ta yi amfani da amincin da ke tsakaninsu wajen shawo kan Ridwan din.

Fitowar docto ne ya sa ta bar tunaninta ganin sun Ridwan sun tsare shi da tambaya.

Ridwan ya ce " docto ya jikin mama baka ce mana komi ba". Ya kai karshen zancen yana kallon yanda docto ke sauke ajiyar zuciya.

" Mun yi ƙoƙari gaskiya wajen dai-dai numfashinta yanzu haka oxygène ne ahancinta in sha Allah, muna sa ran daga nan zuwa gobe zata iya farkawa dan haka ku biyoni office domin jin cikakken bayani ". Ya karashe zancen dai-dai lokacin da sauran likiticin mataimakansa suka fito daga dakin emergency, su kam ko tsayawa ba suyi ba suka yi gaba gabadayansu har docto da yabi sahun su.

Ridwan da Mansur kallon juna su kayi suna juya, watau har sai zuwa gobe ne zata farka, ganin tunaninsu babu mafita ne ya sa suka hanzarta kama hanyar zuwa office din docto.

Mansura kuwa mayataccen idanunta ta zuba bayan Ridwan kallo yanda yake tafiya cikin kasaita da haibarsa.

Bayan kwana biyu

Umar Farouk aiki ya samu wajen me shayi inda shi ne yake masa wanke wanke kai shayi da indomi, kullum me shayi ke sallamarsa kudin aikinsa duk da befi na abinci ba yake ba shi, hakanan yaji sam hankalinsa ba akwnace yake ba, zuciyarsa na tsananta bugawa da ƙarfi zumbur ya mike ya samu me shayi da ke hira da customer murya na rawa yace " dan Allah megida ka aramin wayarka zan sanya kati in kira gida inji lafiyarsu, wani wawan kallo mai shayi ya jefe shi dashi cikin jin haushinsa ya ce " Allah yakyauta in baka wayata, dudu yaushe ka fara aiki da har zaka sanya kati kayi kira". Ya karashe zancen cikin fada.

 Daya daga cikinsu da ke zaune yana cin indomi da kwai ne ya ce " Haba me shayi babu kyau wulakanta dan Adam wlh wannan yaron daga ganin yanayinsa kasan yana cikin damuwa, in bazaka taimaka masa ba pls basai ka hada masa da bakaken ma maganganu ba".

Nan fa cece kuce ya barke tsakaninsu in da akarshe mutumin ya yi zuciya yabar abincin jin me shayi na fada masa to shi ya bashi wayarsa mana, yana tashi ya kama hannun Umar cikin zuciya da barci rai ya ce" yaro ka yarda dani ka kuma yarda da Allah muje zan taimaka maka, kabar aikin wahala ba abin da yake baka sai nacin abinci ". Ya karashe zancen yana jan hannun Umar.

Umar cikinsanyi jiki da rawar murya ya ce " Alhaji kayi hakuri ni na hakura da wayar ma, ƙoƙarin zuwa gaban me shayi, da yake sake baki, domin bashi hakuri, tuni Alhaji ya hana cikin fada ya ce " kai bazaka bashi hakuri ba kyale dan iska, wanda be iya magana ba, in zaka shigo mu tafi zan sama maka aikin da za'a ringa biyanka domin alamu ya nuna kai me iyali ne duk da kanada kananun shekaru. Umar kuwa nan da nan Mamy ta fado masa a rai dan haka be tsaya wata wata ba ya shiga motar.

Me shayi na ganin sun fice sosai hankalinsa ya tashi domin be bata samun yaro me biyayya irin Umar ba. Nan fa mutane sukayi ta masa Allah wadai da mugun halinsa shiyasa kullun ya kasa zama da masu aiki.

Me shayi na ƙoƙarin tattare kwanukan shayinsa yaji sallama da bakon murya, ahanzarce ya daga kansa yana kallon mutumin da ke sanye cikin farar jallabiya fuskarsa babu walwala ya ce " bawan Allah daga tasha na fito ina cigiyar wani yaro me suna Umar aka cemin a wajen ka yake aiki? Dan Allah Ina yake inason ganinsa ni uban gidansa ne. " Ya karshe zancen cikin kosawa da amsa.

Zazzare idanu me shayi ya yi ganin babban mutum ne mai kamala da haiba agabansa, cikin rudewa ya ce " wallahi yanzu nan wani ya tafi dashi sakamakon mun dan samu sabani ni dashi". Nan fa ya koro masa dukan abin da ya faru tsakaninsu.

Mutumin sosai ransa ya baci, cikinsanyin jiki ya koma motar ya zauna tare da dafe kansa cikin damuwa.

Bayan kwanna uku

Benin Cotonou

Yasmin cikin takaici ta ce " Mamy me ya sa da yaya Umar ya kira baki gayamasa halin da muke ciki ba ". Ta kai karshen zancen tana cin tuwo miyan kuka wanda suka kada shi lami babu magi bare gishiri a ciki.

Ƙarar kwankwasa kofa ne ya sa Mamy yin shiru ba tare da taba Yasmin amsa ba. Ahanzarce yasmin ta bude kofar cikin tsananin rudewa ta ga jami'an yan sanda su uku, bakinta na rawa ta ce " bayin Allan lafiya kuwa. ". .

Suka ba ta amsa da " mun kawo muku sammaci ne daga. . . . . . . . .

************* 

Littafin nan, na kuɗi ne. Da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. Hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Kibiya dari biyar kacal domin samun shiga group na musamman.

Domin Karin bayani a tuntuɓe ni ta wannan lambar 09069080725 ko + 22953726162.

Siyen nagari mai da kuɗi gida.


Post a Comment

0 Comments