Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Girma Tsohon Shugaban Kasar Tarayyar Nijeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari GCFR Turakin Sakkwato

Mai Girma Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari GCFR Turakin Sakkwat

"Sarkin Hwawan Bakura ƙara mai girma, 
Tun da Siyasab Bakura ba ƙarama ce ba"

Inji Makaɗa Amadu Mai Launi Bakura a faifan sa na Marigayi Mai Girma Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari GCFR Turakin Sakkwato mai amshi 'Shugaban Ƙasa mai ban tsoro, Na Garba Shehu Alhaji Shagari. Wannan shi ne Marigayi Mai Girma Sarkin Fawan Bakura, Alhaji Muhammadu. Babban Uban gidan Makaɗa Amadu Mai Launi Bakura wanda shi ne ya tanadar mashi Kayan Kiɗa na Taushi da ya yi amfani dasu a sabgar sa ta Kiɗa da Waƙa har ya zuwa wafatin sa, domin kafin lokacin ya na amfani da tafi/ana tafa masa hannuwa ne ya na bayar da Waƙa kamar yadda Garba Gashua ya soma kafin shi ma ya samu Kalangai/Kalanguna. Wannan lamari ya faru da Amadu Mai Launi ne a cikin 1978/79, lokacin kankamar Siyasar Jamhuriya ta biyu (zamanin NPN).

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments