Ticker

6/recent/ticker-posts

Duniyar Tatsuniya

Duniya tatsuniya ce,

An yi sarki jarumi ne,

Yana da ɗiya budurwa,

Duk 'yan matan garinsu,

Babu mai kyawu kamarta.


Wai tai shuhurar samari,

Jarumai wasu tajirai ne,

Wasu ko ilimi gare su,

Wani ɗan sarki ta aura,

Ƙasaitacce na nuni.


Suna shagalin sarauta,

Guguwar tsufa ta hau su,

Ta danne dukkaninsu,

Wawaye duniyar nan,

Ta ke ruɗa da mulki.


Koda iko koda ilmi,

Su biye wa zuciyarsu,

Yan birni na zuga su,

Har sai sun hallaka su,

Su janye jiki su bar su.


Duniya tatsuniya ce,

A Kano wai an yi Sallau,

Musa mai taka Naira,

An yi Kundila a da can,

Tajirai ne su dukkansu.


Sai dai kuma kan su ƙifta,

Ido su rufe su buɗe,

Sun shuɗe sai wasunsu,

Barau ƙwallo na shege,

Ya shuɗe babu shi yau.


Ribar ita duniyar nan,

Ka bi Allah Shi da Manzo,

Ka rabauta a lahirarka,

Amma ita duniyar nan,

Hilata, wa ne kilaki?


Guguwa ce mai gushewa,

Ga dukkan masu motsi,

Mai kudi talaka da malam,

Wawa gaula da sauna,

Dila zaki da ɓauna.


Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments