Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafarkin Kuka

TAMBAYA (35)

Assalamu Alaikum malan inawuni Anwuni lfy. Maln. Dan Allah miye fassarar mafarkin kuka inayawanyin mafarkin kuka Ina kuka sosai😭😭

AMSA

Waalaikumus salam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

Alhamdulillah

Kuka a mafarki na nufin damuwa, gajiya da hadari. Idan kuma ka yi mafarkin kana kuka saboda tsoron Allah hakan na nufin farin ciki da walwala za su zo wa mutum

SHARHI:

Fassarar mafarkinki na nuna cewar kin kasance cikin halin bakin ciki da damuwa wanda dayan biyune

Immadai kina fuskantar kalubale a rayuwar aurenki wanda silar hakan kike kuka ba iya a zahiri ba harma a cikin mafarki ko kuma dai tsananin tsoron Allah da kike da shi ne ya sa idan kika tuno azabarSa kike kuka a zahiri (a farke) wanda silar hakan ya sa harma a mafarki kike kuka

Fatana shi ne kina mafarkin kuka ne silar jin tsoron Allah da kike a fili da boye domin kuwa ya cancanci aji tsoronSa a matsayinSa na al-Khaliqu mahaliccin makaluqai

Dalili kuwa shi ne: ina son ki kasance cikin mutane 7 wadanda Annabi SAW ya ce Allah SWT zai lullubesu a inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwar al-Arshi, wanda mutumin da shi kadai ya tuna Allah har hawaye suka zubo masa, shi ma yana cikin mutane 7 dincan

(Bukhari da Muslim)

Idan kuma yazaman kina kuka ne silar damuwa wadda saboda tsananinta har a mafarki ma kinayin kuka to a shawarce bai kamata ki dinga kuka ba saidai kamata ya yi ki maye gurbin kukan da yawaita fadin:

"Hasbunallahu wani'imal wakil" da kuma "Lahaula wala quwwata illa billah"

Ki yawaita ambaton Allah a kowanne yanayi kika tsinci kanki a ciki. Ki tuno da hadisin sahabin da ya zo wajen Annabi SAW ya ce Ya rasulullah ayyukan addini sunyimin nauyi (Sallah, Azumi, Zakkah, Aikin Hajji) Sai Annabi SAW ya ce ka jika harshenka da yawan ambaton Allah

Sannan ki daina yawan fushi, kada ki nuna fushinki sai akan wani abu wanda ya danganci sabon Allah. Kada ki manta da hadisin bawan Allah dinnan da ya zo wajen Annabi SAW ya ce: Ya rasulullah ba ni shawara. Sai Annabi SAW ya ce kada ka yi fushi (har sau 3)

(Sahihul Bukhari 6116)

Muna roqon Allah SWT ya yaye mana damuwarmu ta duniya da kuma damuwar lahira

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato, (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments